MAHWISH PAGE 6

44 3 0
                                    


Da jin motar tasu ta tsaya itama ta tsaya da yin wayar ta ta, ta d'aga kai ta gan su gaban wani gida mai shegen kyau, kyabe baki ta yi, dan kuwa har cikin zuciyar ta ta ji tsanar gidan kwarai ta kama ta, duk kyawun gidan sai ya zamar mata kamar wani akurkin kajin qauye.

Mai gadi na bud'e gate ta kyabe baki irin na kukan nan, gani take kamar in ta shiga ta shiga kenan har abada, wasu zafafan hawaye ne suka fara zubar mata, kamar an kunna bakin pampo, Salim sai magana yake ya ji shiru, kashe wayar ya yi, ya na ta kai wa da kawo wa a tsakiyar d'akin shi, gani ya yi yawon ba zai kai shi ba, ya tsaya ya rubuta mata saqo da wayar shi,ya na gamawa  ya tura mata, sannan ya fad'a gadon shi ya na tunano irin kyawu na surar Mahwish, tare da fatan Allah ya sa ta ga saqon shi kafin wani abu ya faru tsakanin ta da wancan Sa'eedun.

Sa'eed kuwa jin kukan ta yake kamar ana soka masa kibiya a zuciya, kwata kwata baya jin dad'in shi, yanzu in su Hajiya Mama suka ji, za su ji dad'i ne ai, su ce ga abinda rashin jin shi ya jawo masa.

Lallashin ta ya miqa hannu zai yi, wani irin mugun kallo ta watsa masa, a hankali ya zare hannun nashi, ta kuwa b'are baki ta saki wani kukan iya shegen mai sauti.

Goggo Zulai ce ta fito daga cikin mutane ta kama ta, suka shiga, jin yanda take kuka ne tun qarfin ta ya sanya su Kaita bangaren ta direct, domin kar ta je wajen kishiya ta musu rashin hankali a can su ji kunya, Abban ta ba karamin qoqari ya yi ba wajen qawata mata bangaren ta da kaya na gani na fad'a, duk wanda ya ga wajen sai ya sake saboda tsaruwar wajen, sai fad'in,

"Masha Allah, tabarkallah gida ya yi, Allah ya sa gidan zama ne, Allah ya kawo kazantar d'aki, amma ba ta qin shara ba, Allah ya sa gidan zama ne"

Da dai ire iren wad'annan adu'o'in, duk wanda ya yi addu'ar kwarai,Mahwish a cikin ran ta sai ta ce ba Amin ba, domin a burin ta nan da wasu 'yan satika ta dagula masa lissafi ya auna ta gidan su, ai dai dole a aura mata masoyin ta ko?

Duk wani abu da ya kamata a gabatar na kawo amarya an gabatar, dangin ango duk sun shigo, sun sanya albarka, Hajiya Mama kuwa ta na ido hudu da Mahwish ta ji kamar za ta maida Mahwish d'in ciki, sai kyawun Mahwish d'in ya dauki hankalin Hajiya mama, Aunty Zaituna kuwa wani irin kishi da qiyayyar Mahwish ne ya d'arsu a zuciyar ta, nan take suka had'a ido ita da Ihsan suka yi wani iri da fuska, bak'in ciki da tsanar da ta d'arsu a ran su game da Mahwish bai boyu ba.

A haka sauran 'yan uwan ango suka gama ganin amarya suka tafi, tunda suka fita Hajiya Mama ke santin kyau irin na Mahwish, Aunty Zaituna ce ta tsaida ta a gefen hanyar komawa sashen Hajiya Mama sannan ta ce,

"Hajiya Mama a gaskiya ki rage wannan zumudin da ki ke, in ba so ki ke ki jefa Tasneem a cikin mawuyacin hali ba, yanzu ma ya aka kare ballantana ta ji ki na yabon amarya, kin ga gidan ku d'aya ko bayan tafiyar mu dan girman Allah kar ki nuna wa Tasneem wani abu game da yarinyar can, in ba so ki ke ki b'atawa 'yar da ki ka d'auka kamar  taki rai ba, na dai san ba za ki so haka ta faru ba"

Sa hannu ta yi ta toshe bakin ta ta na dariya qasa qasa,

"Ai ganin yarinyar na yi kamar jinsin Adamawa can mutanen Yola fulani ba, ko kuma wadda aka tsallaka bahar maliya aka haifa a can, waiii zankad'aziyya kenan, barakallah masha Allahu,ina ma Sa'eed kallon soko sumi sumi ashe ya iya zab'e,"

Dan b'ata fuska Aunty Zaituna ta yi, Sannan ta kama Hannun Hajiya Mama suka shiga ciki.

***********************

Taro ya lafa kowa an maida shi gida, dare ya tsala, daga ango sai amarya a dakin, a kuma kan gado, domin kuwa amarya taqi sam ko sallar ma ta daren farko a gabatar, isha'in ta ta doka dan yau a yanda ta gaji sauran da bata yi ba ma sai dai a yafe mata sai gobe ta rama.

Da kayan da aka kai ta da su ta haye gadon ta kwanta, Sa'eed na hawa ta ji wata iriyar tsanar shi na nunkuwa a zuciyar ta, duk yunwar da take ji, ta na ganin kaza da kayan makulashen da ya kawo amma ta qi ci, gani take in ta ci abinda ya kawo ta masa alfarma, Ita kuwa da ta masa alfarma gwanda ta dena ganin shi har abada.

MAHWISHWhere stories live. Discover now