MAHWISH PAGE 35

35 2 0
                                    

Bude bathroom d'in na su ya yi daidai da qarasa zamewar Mahwish qasa, cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara, ta yi matuqar galabaita, jini ko ta ina ya b'ata qasa,

"Baby me ne ne ke faruwa? Me ya same ki haka? Tashi, tashi mu tafi asibiti,"

Jin muryar shi a rud'e sai ya karya duk wata jarumtar da take yi tun farkawar  ta, kuka mai cin rai ta fashe da shi, da sauri ya durqusa a gaban ta ya rungume ta, daga baya ya yi qoqari ya d'aga ta, kaya ya sanya mata, ya kai ta mota, sannan ya dauki Ludhfi dake bacci ya kai wa su Hajiya Mama,

"Ina za ku je da sassafen nan aka kawo mana rainon yaro, ko bacci bai tashi ba?"

"Hajiya Mama ina zuwa, Mahwish ce ba lafiya, ta na ta zubar da jini"

"Jini ? Daga ina?"

Rasa me zai ce mata ya yi, gashi ya baro 'yar mutane cikin mawuyacin hali, da sauri ya bar wajen, ya koma mota, kafin su isa asibiti ya sanar da Abubakar, cikin rashin sa'a baya nan, ya yi tafiya Abuja, amma ya yi waya asibiti ya sanar da zuwan su.

Likita ta duba Mahwish ta gano cewar ciki ne da ita, ya ke so ya fita.

Ta yi duk wani qoqarin da ya kamata, har aka samu tsayawar shi, likita ta bada shawarar a daure mahaifar Mahwish har cikin ya yi kwari, sanan ta daina aiki, saboda kar ya fice.

Mahwish ta qi yarda da farko, saboda tsoro, amma daga baya ta amince, bayan sun dawo gida ne, Hajiya Mama ta taka da kan ta, ta shiga sashen su Mahwish din, kwance ta gan ta, ta rufe ido tsabar ciwon da kan ta ke mata, ba tare da ta yi sallama ba ta ce,

"To kun dawo kuma ba za a sanar da mu ba, a dawo maki da yaron, sai kawai ku kama ku yi shiru, ku ga ku kun kai yaro wajen raino ko?"

Bud'e idon ta tayi a hankali, saboda yanda kan ta ke ciwo, ta ce,

"Ki yi hakuri Hajiya Mama, bani da lafiya ne"

Sa'eed ne ya fito daga kitchen hannun shi riqe da mug ya hado mata tea mai kauri, ya na ganin Hajiya Mama ya koma ya zauna, ya hau shan tea d'in, saboda gudun magana

"Auuu shayin ma da kan ka za ka haɗa? Da kyau, to me yake damun ta?"

"Hajiya Mama ashe ciki ne da ita, bamu sani ba, har ya kusan zubewa, amma mun je asibiti an yi mata daurin mahaifa, kuma an bata bed rest"

"Tooo ikon Allah, to ki huta mana, yaushe yaushe ki ka haihu? Yaran zamani ba ku da aiki sai tara yara, a cika gida da yara"

Mamakin kalaman ta ne suka sanya Sa'eed bude baki, da sauri ta sake cewa,

"To ba zan lamuci ka dinga aiki da kan ka ba, daga yau za a dinga kawo abinci daga wajen mu, sai ku na ci, tunda an hana ta aiki, sai ki ta kwanciya kamar ruwa, shi wancan dan tayin na riqe shi har sai kin warke"

Ta na gama maganar ta ta wuce, Sa'eed kuwa ya ji dadi da ta ce za su dinga yin girki, ba sai Mahwish ta wahala ba, cike da murna ya ce,

"Kin ji ko? Hajiya Mama ta ce ba sai kin wahala ba, ba sai kin yi girki ba,"

Cikin ranta take ayyana,

'Lallai Yah Sa'eed son mahaifiyar shi ya makanta shi,ta yaya zai yarda da ita so easily? What if suka sa abinda zai ajali na a abincin? Yanzu kuma in sanar da shi cibi ya zama qari'

Shiru ta yi, bata amsa shi ba, dan kuwa bata ma son magana, ita kad'ai ta san me take ji.

Da dare sai ga abinci mai rai da lafiya daga sashen Hajiya Mama, shinkafa da miya, da naman kaji zuqu zuqu, sai zob'o, an yanko kayan lambu a ciki, sannan an had'a salad na musamman, Ihsan ce ta kawo, ta na ta b'ata rai, saboda aikin da ta yi.

MAHWISHWhere stories live. Discover now