MAHWISH PAGE 31

30 3 0
                                    

Duqawa ya yi cikin wayance wa ya ce,

"Allah Sarki ashe su Hajiya Mama sun kawo gudun mawar tasu, ba su jira na basu nawa su had'a ba, ba komai, bari na je na shigo da su"

Da sauri ya fita, ya na shiga Mota ya zauna, ya jingina kan shi da kujerar motar, tare da lumshe idanun shi da suka cika da kwalla.

Kamar shi ace ya na da super market har biyu a garin kano, manya ba qanana ba, ace matar shi da yaron shi za a kawo wa irin wannan kayan? Sanin hali ya fi sanin kamanni, kamar ya san za su iya masa haka, ya sa aka had'a masa kaya masu rai da lafiya na jariri, da na Maman shi, a cikin akwatuna masu matuqar kyau, da tsada.

Diban biyu ya yi, ya shige da su, sannan ya sake dawowa ya dauki d'aya da wata jaka mai kyau ya kai ciki, Mahwish me za ta yi in banda murna, ya na shiga da na qarshen ta tafi da gudu ta d'ale shi, ta na ta murna,

"Honey na gode sosai, gaskiya akwatin kawai ya sa na wadatu ina ga ba sai na ga kayan ciki ba ma, dan in na gani a yau murnar za ta zautar maka da matar ka"

Dariya ya yi, nan da nan ya nemi quncin da yake ciki ya rasa, to jama'a waye ba zai so mace kamar wanan ba? Mai kawar da damuwa ta sanya farin ciki, da ka kalle ta.

Zuciyar shi fal farin ciki ya ja ta suka zauna a bakin gado,sannan ya ce,

"Dan Allah wannan akwatunan su zama sirrin mu ni da ke kar ki sanar ma da kowa na shigo da su,"

A sannan ne Mahwish ta fara wani tunani, ganin za ta gano shi ne ya sanya shi saurin kawar mata da tunanin ta,

"Kin gane, saboda ban sai wa Tasneem komai ba, sai bayan na ga gudun Mawar da su Hajiya Mama suka kawo ne sannan na ce gwanda ma da basu hada da wannan ba, dan kin ga ba za ta ji dadi ba, amma ita ma zan mata nata na daban,in shaa Allah"

"Gaskiya ya kamata kam, duk da dai ni ma da dalilin da ya sa aka sai min, amma ita kuma ya kamata a bata dan kar na dinga sabunta kaya ita ta na maimaitana da....honey ka ci abinci na nuna maka kayan da na samu, da kud'ad'e dama haka ake yi in an haihu? Abban mu ma ya aikon da kaya masu yawa, da kayan abinci masu yawa, Hajiya kuma ta yo mana  kayan flour, irin su cincin, dibulan, da alkaki, su acama, da wasu abubuwan ma da ban sani ba, su Innah Sa'a ne suka kawo,(Qanwar Hajiyan su)"

"Masha Allah, ki ce d'akin ki ba masaka tsinke,"

"Ai har da store, da naka d'akin sai da na yi ajiya"

"Ikon Allah, ok let me eat first I am famished  Baby"

Ya qarasa cikin nuna tsantsar jin yunwar, da sauri ta miqe, ta haɗa masa abinci, ta kira shi dinning area, ko wanka be tsaya yi ba, ya hau cin abinci.

Bayan ya kammala da kan shi ya kwashe komai, ya gyara wajen, sannan ya bi ta d'aki wajen jaririn su, a zaune ya gan ta, ta na shayar da yaron,tsaya wa ya yi, ya na kallon su, wani irin dad'i na ratsa shi.

"Ya da kallo, za mu ci ka tara fa,"

"In za ku ci tara ta a kowanne second ba zan qi dawwama ina kallon ku a haka ba, baby na, kin San kuwa kyautar da zan maki tun ran da muka dawo daga gida? Ran da na dawo da ke har Ihsan ta shigo? Ko da ke daga baya fasa wa na yi na ce in kin haihu zan baki, zai fi maki amfani, bari na kawo maki yanzun nan, just wait here yanzu zan dawo"

Da sauri ya koma d'akin shi, komai an sauya masa waje, abubuwan shi masu mahimmanci duk ta adana masa, saboda gidan suna, baka yarda da mutum yanzu ko ya kuke da shi kuwa.

Ya na nemo kyautar ya koma wajen ta ya na dariya, ya ce,

"Rufe idon ki, ki karbi kyautar ki"

Ta na dariya, ta ajiye Ludhfi, ta juya wajen Mijin ta, ta na gyara rigar ta, hannu ta sa ta kulle idon ta, shi kuma a hankali ya riqe hannun ta na dama, ya damqa mata wasu makullai, a hankali ta ke bude idon, kamar abun wasa, makullin mota ne ta gani, kallon shi ta yi cikin rashin fahimta, ta ce,

MAHWISHWhere stories live. Discover now