MAHWISH PAGE 14

55 4 0
                                    


Mahwish duk ta zama wata iriyar mara laka a jikin ta, sannan ko da yaushe mutum ya gan ta, zai ga ta na kuka, a tunanin Hajiya Mama tsabar son da take wa Sa'eed ne ke sanya ta kuka, dan haka kullum haushi Mahwish ke bata, dan ta na nuna kamar ta fi su son Sa'eed da damuwa da halin da yake ciki.

Tun da ya bar d'akin ta bata bi shi bangaren Tasneem ba, Tasneem kuwa na can na mata tanadin rashin mutunci, ita kuma ko sanya wa ma a rai za ta je duba shi wajen Tasneem ba ta yi ba, ta sani komai daren dad'ewa zai dawo wajen ta, to meye na bin shi? Ciwo ne dai ya riga ya same shi, sai a bi shi da addu'a .

A kullum jira take da tsammanin kiran Salim dan ya wanke kan shi akan abinda ya aikata, shiru, in ta kira layin shi ma baya shiga, a duk sanda ta kira layin aka ce mata is not reachable, sai ta yi kuka ta gode wa Allah dan kuwa haka bai tab'a faruwa ba.

Ta rasa dalilin da ya sa duk da ta na jin haushin shi, soyayyar shi na nan maqale a zuciyar ta, dana sanin son shi kuwa ta yi shi har ta gode Allah, gashi Sa'eed ya roqi alfarmar kar ta sanar da kowa, gashi ita bata iya riqe sirri ba, ta saba komai ya dame ta ta sanar da Hajiyan su ko Xulaihah, komai munin shi kuwa, dan abinda ya sanya Xulaihah jin tsoron kasancewar Mahwish da Salim waje d'aya kenan, ta san me suka aikata a gidan su Salim d'in Mahwish ta bata labari cikin jimami a lokacin, yanzu ma bakin ta qaiqayi yake ta yi maganar da Xulaihah.

Wayar ta ta dauka, ta na ta juya wa, ta rasa yanda za ta yi, kuka ta fashe da shi sosai,ta na fadin,

"Ya zan yi ne? Na riga na yi alqawarin ba zan sanar da kowa ba, maganar nan na ta ci na, Yah Salim ka cuce ni, ka cuci soyayya ta,"

Sallamar Sa'eed ce ta sanya ta saurin goge idanun ta, ta ajiye wayar ta fita, kallon ta ya yi daga sama har qasa, ya gan ta a wani hargitse, ta san yau zai dawo wajen ta, amma da alama ko shara ma bata yi ba, yau sati d'aya kenan da zuwan Salim gidan, amma kullum qara lalacewa take, duk ta rame, ta yi duhu.

Cike da kulawa ya isa zuwa gaban ta, ya d'aga fuskar ta, nan take ruwan hawaye ya hau zuba daga idanun ta, a hankali take fitar da kuka mai sauti, saurin rungume ta ya yi, ya na lallashin ta, tare da tambayar ta dalilin kukan ta,cikin kuka ta ce,

"Na yi babban kuskure a rayuwa ta, ban san haka Yah Salim yake ba, ban san haka ya dauki soyayya ta ba, ya maida ita abun wasa, gashi ba zan iya sanar da kowa abinda ya min ba, ba zan taba yafe wa Yah Salim ba, har abada,"

Sa'eed na jin ciwon yanda Mahwish ta yi zurfi a soyayyar Salim, amma bai isa ya hana ta ba,saboda tun ta na qarama take son shi, amma zai iya qoqarin shi dan ya ga ya dasa mata soyayyar shi mai tsafta, tun su na tsaye har ya samu waje ya zauna da ita, ta na ta zuba masa surutu da labaran yanda suka taso, da yanda suke gudanar da rayuwar su da Salim a baya, ya matsu labarin ya qare, amma kamar sake kunna ta ake, shiru ya yi ya na sauraron ta, tare da nuna mata ya na tare da ita kuma ya na sauraren ta.

Daga baya ya ce ta je su yi wanka sai ta qarasa masa labarin a can, ba tare da ta kula ba da me ya ce ta miqe ta bi shi,ta na ci gaba da bashi labarin soyayyar ta da Salim, wani wajen ta yi dariya, wani wajen ta yi kuka, har sai ya lallashe ta ta yi shiru.

Bata tashi kula da wautar bin Sa'eed wanka da ta yi ba, sai da suka shiga bathroom ta ga ya na tube kaya, da sauri ta juya baya, tare da dafe qirjin ta ta ce,

"Mene ne haka kuma?"

Dakatawa ya yi, ya dafa qugu daga shi sai gajeren wando ya ce,

"Wanka za mu yi ko kin manta ne?"

"Wanka kuma? Ni dai ba zan wanka da kai ba"

"Ba ki so ki ci gaba da bani labarin Salim ne? Dan da mun gama wanka na ci abinci bacci zan yi"

"Gobe na qarasa maka labarin, ko kafin bacci ya dauke ka"

Da gudu gudu ta ke son barin wajen, ya yi saurin kama ta, fuskar shi da ta ta, ya haɗa waje daya ya na goga mata sajen shi a kuncin ta, rufe idanun ta tayi, ta na amsar dukkan saqon da yake aika mata da shi, yau ce rana ta farko da ba ta ji haushi, ko tsanar tab'a ta da Sa'eed yake ba, hasali ma ta bud'e zuciyar ta ne dan karbar saqon.

MAHWISHWhere stories live. Discover now