*KI NA BUQATAR TSAHON GASHI?LAUSHIN GASHI? KI NA DA AMOSALI AKAN KI DA YAKE HANA GASHIN KI TSAWO? KI NA FAMA DA KARYEWAR GASHI? HANZARTA KI SAI HAMIBRAH HAIR CREAM AND OIL**HAMIBRAH HAIR CREAM ₦1800 NE KACAL, HAMIBRAH HAIR OIL QARAMIN ROBA ₦1000, BABBAR ROBA ₦1800*
*KINA FAMA DA YAMUSHEWAR NONO? KI ZO GA HAMIBRAH BREAST CREAM DAN YA TADA MAKI DA MOTSEWAR DA NONON KI YA YI A 1200 KACAL*
*SHIN KI NA FAMA DA QURAJEN FUSKA KO TABON FUSKA? KO LALACEWAR FATA BAYAN KIN YI BLEACHING? KI NEMI HAMIBRAH SOAP AND BODY SCRUB DOMIN GYARA FATAR KI*
*BODY SOAP 1500*
*BODY SCRUB 1500**ANA SAMUN WADANNAN KAYAYAYYAKI A GARIN KANO ZUWA KOWACCE JAHA IN SHAA ALLAH*
*HANZARTA KI NEMI NAKI AUNTY GUIDEES (GUIDA YARA) KEMA A DAMA DA KE* 💃🏻💃🏻❤️💖
*Dan neman qarin bayani kira ko ku aika saqo a wannan lambar*
*09031416423*
Ranta a matuqar bace ta shiga gidan, ba ta tsaya a ko ina ba sai parlour'n ta, ko zama ba ta yi ba, ta duba fuskar Ihsan ta ga yanda idon ta ya kumbura sabo da kukan da ta sha, ga kuma shatin yatsun Sa'eed nan a kuncin ta, sai ta qara shiga cikin tsananin damuwa, nan take ta ce wa Ibrahim ya je ya kira mata Sa'eed d'in yanzu yanzu ya zo, ta na neman shi, kar Ibrahim ya sake ya koma ba shi, kamar wani wanda zai dakko mata shi a ka.
A hanzarce yaro ya tafi, ya na jin tsoron hanyar amma haka ya isa, dan yau Hajiya Mama ta juye ta koma Adaman ta.
Sanda Ibrahim ya sanar da Sa'eed saqon Hajiya Mama, sai Sa'eed ya ce masa ya ce gashi nan zuwa,
"Ta ce mu koma tare,"
Tsaki ya ja, ya miqe cikin fushi zai fita, Mahwish ta riqe hannun shi, Ibrahim kuwa fita ya yi, ya tsaya a qofar shiga sashen nasu,
"Dan Allah Honey kar ka yi fad'i in fad'a da Hajiya Mama akai na, dan Allah ka sassauta kalaman ka a gare ta, domin duk yanda hankali ya gushe ba za mu taba manta wa da mahaifan mu ba, iyaye na da babban matsayi mai girma, komai za a ce akai na su fad'a, ni d'in me? Daraja ta bata kai ta mahaifiyar ka ba, kar ka b'ata da ita akai na,dan Allah"
Kalmar ta ta farko ta fi tafiya da hankalin shi, wato "Honey" yaushe har ya samu wannan matsayin bai sani ba? Ya na cikin yanayi na b'acin rai, amma sai da ya murmusa, ya sumbaci lips din ta, da idanun ta da suke kallon shi kamar kar su dena.
A hanzarce ya saki hannun ta ya tafi, a qofar shiga wajen su ya tadda Ibrahim suka tafi tare, su na zuwa ya ga tashin hankali da bala'i a fuskar mahaifiyar shi, wanda be tab'a ganin kalar shi ba, zama zai yi ta daka masa tsawa, sannan ta ce,
"Sa'eed akan mace ka cire hannun ka da ka raini qanwar ka da shi, ka ciyar da ita abinci kala kala, ka shayar da ita ruwa, ka wanke mata kashi, yau kuma ka mare ta da shi?"
Wannan lissafin da Hajiya Mama ta yi sai ya sanya Ihsan sake fashe wa da kuka sosai, wanda har ya karyar wa da Sa'eed zuciya, ya ga rashin kyautawar shi akan abinda ya aikata, har a wannan lokacin da ake magana ruwa kawai ya sha be ci abinci ba.
"Hajiya Mama ba laifi..."
"Ban kira ka dan na ji wane ne mai laifi ba, na kira ka ne dan na baka umarni dole ne a yau ba sai gobe ba, Mashawi ta bar gidan nan, in kuma.ba haka ba, da ni, da Ihsan za mu bar maka gidan ka, ko a titi ne za mu kwana,ke Ihsan,shiga ki hada mana kayan mu, domin da dukkan alamu, da yanda fuskar shi ta nuna, gwanda ya zabi matar shi, akan mu,"
Jiki ba kwari Ihsan ta miqe,dan ta na tsoron kar Hajiya Mama ta zaqe ta kwafsa, ina za su?
Da sauri Sa'eed ya zube da guiwowin shi a qasa ya na ba wa Hajiya Mama hakuri.
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........