MAHWISH PAGE 40

45 4 0
                                    


Mahwish duk ta bi ta rame, ta fita hayyacin ta, shi kan shi Sa'eed sai Allah ya jarabce shi da tsananin kewar Ludhfi, dama abinda suke so kenan.

A lalace sai da watanni biyu suka gifta ba Ludhfi ba bayanin shi, Mahwish ta yi kuka, ta yi bori, ta yi roqo duk akan a dawo mata da yaron ta, amma kowa ya toshe kunnen shi, ba mai duba halin da take ciki, mahaifan ta sun bata hakuri, tare da tabbatar mata da cewar Ludhfi na lafiya qalou, ba wata damuwa da ke damun shi, dan haka ta kwantar da hankalin ta.

Abin ka da uwa da d'a Ita dai ta ji su ne kawai, amma ta na buqatar yaron ta, musamman da ta tabbatar da cewa ba ya hannun mutane nagari.

Watarana ta na kwance ita kad'ai,ta na tunanin yaron ta, Sa'eed ya tafi weekend, ta gama saka ran zai dawo mata da yaron ta, duba da irin kuka da tashin hankalin da ta dinga yi, ya tabbatar hankalin ta ba kwance yake ba, sai ta ga yaron ta, ta kuma san duk abinda take so a duniya Sa'eed na yi mata shi kome ne ne, sai dai in ya sab'awa addini ne kawai yake bari, dan haka ta na da yaqinin zai dawo mata da yaron ta, sai dai kuma in be dawo da shi ba fa? Wannan tambayar ita ke ta kai wa da komowa a zuciyar ta, daga qarshe dai ta tabbatar wa kan ta da Sa'eed ba zai barta cikin kunci  ba, zai dawo mata da yaron ta.

Wayar ta ce ta yi qara, ta na dauka sai ta ga No Ihsan, mamaki ne ya kama ta, dan kuwa ko rashin mutuncin za a mata Zaituna ce ke kira, tunanin ta ya tsaya cak a daidai lokacin da ta tuna tunda zaituna ta haihu ta koma gidan ta,yanzu Ihsan ke kula da Ludhfi what if wani abu ne ya same shi?

Cikin sauri hannu na rawa ta dauki wayar, ta na dauka ta fara magana, sai ta ji Ludhfi na kuka, nan da nan ita ma kuwa hawaye suka fara zuba mata.

Ihsan kuwa ta na sane ta kira Mahwish dan kawai ta saurari kukan Ludhfi, zuciyar ta ta quntata, kuka yake mai tab'a zuciya, da alama wani abun aka masa, ko wani abun yake so, ko kuma rikici ne kawai,

'Ina Sa'eed ya je ake wa yaro na haka? Ya tabbatar ya dawo min da yaro na, in ba haka ba, zan je na d'akko abu na da kai na'

Kashe wayar Ihsan ta yi, ta na ta dariya tare da kwaikwayon Muryar Mahwish,

"Ludhfiiii ! Ludhfiii dear what happen? Me akai maka, Ludhfi yi min magana"

Dariya suka sanya ita da Tasneem, message ne ya shiga wayar Tasneem, da sauri ta bude, ta na gama gani, ta saki wani murmushi mai sauti, sannan ta goge shi, kallon Ihsan ta yi ta ce,

"Bari na je sashe na, tunda har yanzu bai dawo daga wajen Aunty Z ba, zan dan watsa ruwa kan ya dawo"

"Ok, a tahon da abun dad'i"

"Ba ki da matsala, ina nan ajiye kuwa da cake da na yi jiya, in zan dawo zan taho maki da shi"

"Shi ya sa nake son ki 'yar qanwa taaa"

"Yauwa ki sanar da Hajiya Mama zan je na dakko Ibrahim, yau zai dawo, inshaa Allahu,"

"Ok tom bari ta fito, Allah sarki Iroro, shi kenan sauran shi shekara yanzu kuma sai jami'a, an zama saurayi "

"Haka muke fata, bari na je na dawo"

"Ok"

Tasneem.na zuwa sashen ta,mayafi da jaka kawai ta dauka, ta kulle sashen ta,wajen motar ta ta nufa, hannun ta ta sanya a jakar ta, ta dauki key din motar, sannan ta bude ta shige, Baba mai gadi na bude mata gate ta cilla motar saman titi, kida ne irin na arnan kudu ke tashi a motar, ta na ji ta na bi, tare da kad'a kai ta na rawa, wani irin nishad'i take ji sosai, fiye da tunanin mai tunani, ita kad'ai ta san me take kulla wa a ran ta.

Wayar ta ta dauka ta yi waya, cikin fara'a.

".....ok to gani nan zuwa, amma ba jima wa zan ba, gani kawai zan na wuce dauko yaro daga makaranta"

MAHWISHOnde histórias criam vida. Descubra agora