Ya na zaune ya na jiyo duk maganganun su, anan ne ya fahimci Mahwish ba ta da laifi, zuwa suka yi har gida suka same ta, dan su yi mata fyade, dan haka da sauri ya dau keys d'in gidan, ya fita, ya kulle su, sannan ya sauka qasa, bai tsaya a ko ina ba sai a wajen 'yan sandan qasa mai tsarki, (ba wasa kenan) ya musu bayani dalla dalla, kuma sun fahimce shi, dama su na jin haushin yanda mutanen Nigeria suka cika masu qasa, kuma suke aikata manyan laifuka, kala-kala.
Su na isa gidan, suka tarar da sun had'a zufa sharkaf, sai qoqarin b'alle qofar suke, sun kasa, Mahwish kuwa banda kuka ba abinda take yi, baqin cikin da ke zuciyar ta ne ya sanya ciwon ta tashi, wai yanzu ace lalacewar har ta kai mata su bi mace 'yar uwar su, su ce za su mata fyade, wannan wanne irin zamani muke ciki na lalacewa da maida sab'awa Allah ba bakin komai ba, kamar ba za a koma gare shi ba.
Ta na ganin Sa'eed ya bud'e qofar ta ji wani farin ciki ya mamaye mata zuciya, kallon lokaci ya yi, ya kalle ta ya ce,
"Kar ki damu, za mu yi waya, dama mantuwa na yi, na keys d'in gidan mu na can Nigeria bari na d'auka na wuce, ina gab da makara, in Hajiya ta dawo ku je asibiti ki ga likita, dan na san yanzu dole sai jikin ki ya motsa saboda wannan hatsaniyar, Mahwish kar ki manta, ina son ki, no matter what happens, ke tawa ce, sannan ni naki ne, hakan ba zai tab'a sauya wa ba, ba bu wanda ya isa ya shiga tsakanin soyayyar mu, inshaa Allahu, I love You, sai na dawo"
Kalaman shi sun shige ta fiye da yanda duk wani mahaluqi ke zato da tsammani, Sa'eed ya dasa wa zuciyar ta soyayya mai wuyar fassara, mutumin da ya yarda da kai haka ba ka da masoyi sama da shi.
A zaton ta zai yi zargin dan ta ga ya yi tafiya ne, ya sa ta kira su, ko kuma basu sani ba, amma da suka neme ta ta amince musu cikin son ran ta.
A gaskiya samun miji kamar Sa'eed na da wahala, haka Mahwish ta yi ta saqe saqe, har Hajiya ta dawo, nan fa ta hau bata labarin abinda ya faru, har kama su Sumy Fara da aka yi, godiya Hajiya ta dinga yi wa Allah akan tona asirin 'yan iska da ya yi, Sannan ta d'ora da yi wa Mahwish nasiha sosai, akan jin tsoron Allah, Hajiya ta fad'awa Mahwish kalaman da duk mai hankali ya ji sai natsuwa ta shige shi.
"Mahwish wannan zamanin da muke ciki, babban qalubale ne ga dukkan Musulmi, mai imani, wanda ya yi imani za mu mutu in lokacin mu ya yi, ko da ciwo ko ba ciwo, mu na sallah, ko muna karatun Alkur'ani, ko mu na sata, ko maita, ko mad'igo, ko luwad'i, ko mu na sauraren kid'a ko mu na sauraren qur'ani, Allah shi ne kawai wanda ya san a wanne hali mutum zai koma gare shi, kuma da yaushe mutum zai mutu din, Mahwish bawa ba ya tab'a sakankancewa ya ce ai shi Allah ya taimake shi ba ya aikata wasu manyan zunubai, to dole ne bawan nan fa ya dage da addu'a akan Allah kar ya bashi ikon aikata manya da qanana, dole ne mutum ya dinga roqon Allah kariya da shiriya, akan lalacewar da wannan zamani ya yi, kuma dole ne mai rai ya yawaita istighfari, saboda ba ka sani ba ko ka aikata wani laifi bisa ga kuskure, ko kuma cikin sani.
Mahwish ina maki nasiha da jin tsoron Allah, a komai ki ke ki sani ya na kallon ki, ko mene ne shi, ba abinda yake boye wa ganin shi subhanahu wata'ala, Mahwish duk yanda ki ke zaton Allah, za ki same shi a haka, ina nufin, in ki ka kyautata masa zato, ki ka sakankance shi mai rahama ne, to tabbas zai yafe maki laifin ki, gaba daya, ya maki wannan rahamar, Mahwish ki bi mijin ki, domin kuwai biyayya za ki masa da kyautata wa, in ya aminta da ke, sai Allah ya aminta da ke, ya sanya ki a aljannah, amma in mijin ki bai aminta da ke ba, tabbas Allah ma ba zai aminta da ke ba, Allah ya yi muku albarka, Allah ya qara maki lafiya Allah ya kare ki daga sharrin mutum da aljan"
"Ameeen Hajiyar mu, Allah ya qara wa rayuwar ku albarka, mu ci gaba da jin dad'i tare,"
"Ameeen,"
"Hajiya Yah Sa'eed ya ce mu je asibiti na ga likita, amma ki huta, zuwa yamma sai mu je"
"To in ce dai ba jikin bane?"
"Ba na jin komai, sai yawan faduwar gaba, Hajiya me ki ke ganin zai faru idan ya je? Kar su riqe min shi, saboda sun saba riqe shi da ya je wajen su, Hajiya ina yawan damuwa shin a wanne hali Ludhfi yake ciki? Sa'eed zai samu damar kawon shi nan kuwa?"
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........