MAHWISH PAGE 8

41 2 0
                                    


Kwance Hajiya mama ta tadda Tasneem a qasan carpet din parlour'n ta, ta wurgar da komai a qasa ta na ta kuka, irin na tab'ararrun yaran nan, da uwa ba kwab'a,uba ba hantara, isa ta yi ta daddafe qasa ta zauna, sannan ta dora kan Tasneem a cinyar  ta, ta na share mata hawayen ta, ta ce,

"Tasneem anya kuwa kin tab'a b'atan rai a duniya sama da yau? Kalaman ki sam ba su min dad'i ba, kin san mene ne abinda ke saurin raunata zuciya ta, kuma ki na amfani da shi wajen quntata wa zuciya ta, mutuwar Mahaifiyar ki ita ce babban abinda ke d'agan hankali a duk sanda na tuna, da ke da Ibrahim ku kad'ai ne nake gani na ke jin dad'i a rai na, kuma bayan su Zaituna da Yayah ku ne kad'ai dangi na a duniya, Ni ce silar mutuwar mahaifiyar ki, domin kuwa da ban kafe ba za a je asibiti ba a gida za ta haihu, wataqila da tuni mu na tare da ita anan, amma kafiya ta ta jawo rasuwar 'yar uwa ta, masoyiya ta, amanar da iyayen mu suka damqa a hannu na, alhamdu lilLAAHi ta bar min ku, kuma na yi alqawarin kula da ku har qarshen tawa rayuwar, ba zan bari ku yi kukan maraici ba, da zuciyar mahaifin ku bata buga ba sakamakon rasuwar mahaifiyar ku, da sai na ce akwai na gaba da ni a iko da ku, amma kamar yanda bani da kowa sai ku, kuma ba ku da kowa sai ni, dan haka ki dena kuka, ki na fad'in kalaman da za su sanya ni cikin tashin hankali, me akai akai kishiya? Matsala ta da ke rashin hakuri, da ace ki na da hakuri, da mun cimma nasarar abinda muke fata, shi aikin gaggawa baya kyau, kuma baya qarko,"

"Hajiya mama ya fa kwana da ita, baki ga d'akin su ba da na leqa, kafin a kawo ta har wajen boka sai da na koma, aka bani maganin qiyayya, amma sai da ya kwana da ita, a haka ma Sa'eed ya makance akan son ta, ina ga ya kwana da ita?"

"Ta yaro kyau take ba ta qarko, ai ki yi hakuri ki ga abinda zan mata, kin ga wannan fuskar tata kamar gwanda? Se na maida ita bayan abarba, ba dai kyawun ta ke rud'ar shi ba? Ki bani nan da wani lokaci, duk wata soyayya da Sa'eed ke yi wa Mashawai take ko wa sai ya ajiye ta da kan shi, ai a gaban ki boka ya ce sai a hankali za a yi nasara ko? Saboda ita soyayya aba ce mai qarfi raba ta da mutum sai an yi da gaske, ki qara hakuri kin ji?"

'Daga kai Tasneem ta yi, sai ta samu zuciyar ta da yin sanyi da kuma yarda da alqawurran Hajiya Mama, hira suka dinga yi kamar ba abinda ya dame su, daga qarshe Hajiya Mama ta ce ba inda za ta sai an mata Farfesun kaza, Tasneem ta iya girki, amma ta tsani yin shi, a dole dole ta yi wa Hajiya Mama farfesu, ta na yi ta na mita, ita kuma.Hajiya Mama ta na fadin,

"Sai kin dafa yasin, shegiya marowaciyar banza, in banda shegen rowa,ruwan gora kullum na shigo bangaren ki ke bani, ko dan tsinannen lemon nan na roba ba ki san ki ba Uwar ki ba da sunan ta kawo miki ziyara"

"Hajiya Mama daga can zuwa nan d'in ne kin kawon ziyara?"

"To da motar uban ki zan zo ko da ko a sayyarar qafata? Can da nan din ban narka kitse ba kan in iso? Ke ni je ki ki duba kar ki bar ta ta yi luguf dinnan kamar za ki ba wa tsohuwa ko jariri, da haqori na casss Allah bai tauye ni ba, ba shegen da zai min dahuwar tsoffi"

Tasneem na ta dariyar rikicin Innar ta ta, ta je ta juyo mata kazar, ai kuwa haka Hajiya Mama ta zauna ta cinye kaza guda ta turawa, bata rage komai ba, da kyar Tasneem ta had'a mata da lemon kwali, Tasneem na da matsalar rowa ainun, Hajiya Mama na da matsalar kwad'ayi.

Hajiya Mama a nan ta yi magrib, ta yi isha'i, saboda bata so ta tafi, Tasneem ta je wani wajen, su na nan zaune Hajiya Mama na gyangyadi, Tasneem na hamma suka ji horn din motar Sa'eed, kamar wanda aka d'alawa duka haka Hajiya Mama ta farka ta na fad'in,

"To Sa'eed ya dawo, ni kuma kin ga tafiya ta, ki yi hakuri ki jinkirta, kin san komai sai da saka hannun Zaituna, in ta ji labarin an je wani wajen ba ita sai ta maki tijara, ba ruwa na ni kuwa, kin ga tafiya ta, sai da safe"

"Hajiya mama dan Allah ki kwana da ni, Iya na nan fa za ta kular maki da b'angaren ki,tsoro nake ji, da kyar nake bacci a gidan nan ni kad'ai"

"Ai kin ga saboda d'an banzan kishi irin naki akai akai a kawo maki mai aiki wai ke me miji, ki ka qi, yanzu dai gashi auren dai da ba ki so, ya yi shi, kuma ba ki da d'an tayin kwana,kuma da da yake tafiye tafiye ke da uban wa ki ke kwana? Ko yanzu ne tsoron ya shige ki?"

MAHWISHNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ