MAHWISH PAGE 20

60 3 0
                                    

Kusan kwana biyu Sa'eed be kira Mahwish ba, ba saqo, ba komai, ba aike, kuma be je ba, tun ta na damuwa, har ta fara jin haushi, kar ku manta dama ba wani zurfi ya yi ba a zuciyar ta, dan haka a hankali sai ta fara tunanin ko dai dama ya na so a raba su, yanzu ya samu hanyar rabuwa da ita cikin sauqi ne?

Xulaihah da Hajiya sun yi iya qoqarin su na ta bashi uziri, amma ta qi, har sai da watarana Abban su ya dawo, bayan ya huta, ya ci abinci,ya yi wanka, Hajiya ta labarta masa duk abinda ke faruwa, ran shi ya b'aci matuqa, amma Hajiya ta kwantar masa da hankali, kuma ta nuna masa cewar ya yi hakuri ya danne fushin shi, dan kar Mahwish ta samu dalilin sake jin haushin Sa'eed, dan basu sani ba, ko Hajiya mama  ce ta hana shi zuwa.

Sawa ya yi a kira masa Mahwish din, bayan sun sake gaisawa, ya tambaye ta meke faruwa, nan da nan kukan da ta ke ta riqe wa a dalilin fushi da take da Sa'eed ya kwace mata, sai da ta yi kuka sosai sannan ta ba wa Abban su labarin komai.

Hakuri ya bata, sannan ya ce ta je zai neme ta.

Su na zaune da yamma ita da Xulaihah suka ji sallamar Ibrahim, da sauri Mahwish ta kalle shi, a da da ta na gida in ta ga yaron haushi ke kama ta, amma a yau sai ta samu kan ta, da shiga yanayi na farin ciki, gaishe su ya yi, sannan cikin yanayi na damuwa ya ce,

"Yah Mahwish, dama na gudo ne dan in sanar da ke cewar tun da ki ka tafi, Yah Sa'eed yake kwance a asibiti, ba lafiya, dan Allah ki je ki gan shi, ko sau d'aya ne"

Ji ta yi kamar bata gane me yake fada ba, sai daga baya, kamar an jefe ta da maganar, ta hau tambayar asibitin da yake,Ibrahim kuwa sanar da ita ya yi, ya ce zai tafi, kar a neme shi a ga baya nan.

Da kyar ya tsaya ya karbi kudin da Hajiya ke bashi, bayan tafiyar shi ne Mahwish ta koma daki ta zauna ta na kuka, saboda tunanin halin da Sa'eed ke ciki.

"Ai ba kuka za ki yi ba, addu'a za ki masa, sannan ki shirya mu tafi, mu ga jikin nashi,"

Da sauri ta kalli Xulaihah, ta ce,

"Amma ba ki da hankali ko? Ta yaya za mu ganin shi a irin wannan yanayin?"

"Ahhh meye a ciki, har yanzu dai ko sun qi, ko sun so ke matar shi ce, dole ki ga mijin ki,"

"Ba inda za ni, sai dai in ke za ki"

"Ni kuma a su wa? Ki na so wannan figaggiyar Ihsan din ta cinye ni da haqoran ta ko?"

Dan murmushi Mahwish ta yi, sannan ta koma ta kwantar da kan ta, ta na tunanin a wanne hali mijin ta yake ciki.

Hajiya da Abba da Xulaihah, sun sha fama kafin Mahwish ta yarda za ta je ta ga Sa'eed,amma ta tabbatar masu da cewa ba jimawa za su yi ba, suka ce sun amince,ta je dai a hakan.

Basu tashi tafiya ba, sai da yamma ta yi liss,Mahwish ta sha wanka, ta sha gayu, jikin ta sai tashin qamshi mai sanyi take, wanda in ba a kusa da ita ka ke ba, ba za ka ji ba, kasancewar ta na matar aure bai kamata ta fesa turare mai qarfi ba in za ta fita ne ya sanya ta saka wanda ba za a ji ta na qamshi sosai ba, kuma zai kawar da warin zufa.

Bakin ta dauke da sweet mai qamshi, lips d'in ta ta sha man lebe, mai kyau, ya yi daidai yanda Sa'eed ke so.

A hanya Abban su ya tsaya ya sai masu lemo da ayaba da Apple, da kankana, sai ruwan roba katan d'aya, da maltina katan d'aya.

Ya na ajiye su ya tafi, su kuma suka shiga ciki, nan fa ido ya raina fata, a wanne ward yake ma tukunna? Waje suka samu suka zauna, su na sake ganin wautar su, gashi Mahwish bata so ta kira Sa'eed d'in, da alama dole su kira shi, su na qoqarin kiran shi, suka ga Ihsan ta fito daga wani waje, za ta fita,da sauri suka nufi wajen, dakuna ne, a jere, dan haka da shiga nan fita can suka gano inda yake.

MAHWISHWo Geschichten leben. Entdecke jetzt