MAHWISH PAGE 23

41 5 0
                                    

Jiki ba kwari ya sanar da Mahwish me ya faru, ba tare da ta so komawa ba, amma haka ta bashi kwarin guiwa dan dai kawai kar ya b'ata wa mahaifiyar shi rai, sannan ta tunatar da shi kalmar Hajiya Mama ta qarshe, komai ya wuce a yafi juna, sai ya samu kan shi da samun kwanciyar hankali, wataqila da gaske take, komai ya wuce d'in.

Da yamma suka tattara komai nasu, suka koma, su na shiga cikin gidan Mahwish ta ji wani irin mummunan ciwon kai ya kama ta, da sauri ta dafe kan ta, ta ce,

"Washhh Allah na,"

Sa'eed ne ya juya ya kalle ta ya ce,

"Me ya faru da kan na ki?"

"Ciwo yake min sosai,"

"Sannu Allah ya sawaqe, bari zan sanar da Abubakar a baki magani, Allah ya baki lafiya Baby na"

"Ameen"

Ko da suka shiga gidan ba kowa a harabar gidan, Baba mai gadi sai sunkuyar da kai yake, alamun bai ji dadin abinda ya faru ba kwanaki, amma Sa'eed ko d'aga masa maganar ma be ba.

Sashen su Mahwish ta nufa, shi kuma ya tafi wajen Hajiya Mama.

Ta na shiga bangaren su ta  ji wani irin zazzaɓi ya kama ta, da kyar ta daddafe bango ta qarasa kujera ta kwanta.

Sa'eed kuwa na zuwa wajen Hajiya Mama, suka hau gaisawa daga gaisuwa sai hira, kamar ba abinda ya tab'a faruwa a tsakanin su.

Ya ji dad'in hakan sosai, sannan ya ce musu, Mahwish na nan zuwa a gaisa ta shiga da kayan su ne da suka dawo da su,

"Babu komai, ai mu ya kamata mu je mu bata hakuri, yarinya ce me hakuri, ba dan haka ba, wannan shegen halin nawa wa zai iya da shi? Kai dai Allah kiyaye gaba kawai"

"Ameeen Hajiya Mama, bari in je, Tasneem na nan kuwa? Na ga ban gan ta anan ba, kuma ban ji motsin ta ba"

"Eh ta ɗan je gidan Zaituna, yanzu za ta dawo"

"Ok, Amma bata sanar da ni ba, ni yawan fitar tan nan na damu na, kuma in za ta fita ba za ta sanar da ni ba kawai sai dai in dawo na ga bata nan"

"Tooo ai ni ka san gunki ce aka sassaqa aka aje a gidan zoo dan tarihi, in na bata izinin fita nayi laifi kenan ko? To ka yi hakuri daga yau ba zan sake ba ta izinin fita ba, ni dai zaman lafiya na ke nema, ba tashin hankali ba"

Maganganun ma sun masa yawa bai san wanne zai dauka ba, kawai fita ya yi be ce komai ba, sashen Tasneem din ya shiga, ya gan shi fess ko ina qal, amma mai wajen bata nan, tsaki ya yi, ya samu waje ya kwanta dan ya d'an huta, bacci mai nauyi ya dauke shi.

Mahwish kuwa na can ta na jiran ya shiga ta sanar da shi meke faruwa da ita, shiru shiru bai je ba.

Abu sai gaba gaba yake, jikin ta ya dauki mugun zafi, ga ciwon kai.

Wayar ta ta dauka da kyar ta kira Hajiyan ta, take sanar da ita, cike da tausaya wa Hajiya ta ce Xulaihah za ta zo dan taya ta kwana, tunda Sa'eed ba a wajen ta zai kwana ba.

Godiya ta yi ta kashe wayar.

Da misalin bakwai da rabi, na yamma, ta miqe da kyar ta je ta yi alwala ta yi magariba, a wajen ta kwanta, ta na hawaye, ba Sa'eed ba labarin shi, ya na dawowa daga Masallaci ya wuce sashen Tasneem, wadda ta dawo tun kafin magariba, ta yi musu abinci, suka ci suka sha.

Zaune suke su na kallo, ya tuna da Mahwish, kamar wanda ya zauna akan allura haka ya miqe, ya ce,

"Ya Salam, na manta kwata kwata yarinyar can bata da lafiya, ban kai mata maganin ba,Tasneem ko ki na da maganin ciwon kai?"

Murmushi ta yi, dan kuwa da alama aikin  bokan Aunty Zaituna ya na ci.

"Eh ina da shi, ina zuwa"

Cike da farin ciki, ta shige, ta daukko maganin ciwon kai ta bashi, dan ta san ba wannan ne zai taimake ta ba, jiki na rawa ya tafi.

MAHWISHWhere stories live. Discover now