MAHWISH PAGE 52

57 6 2
                                    

Tun daga bakin gate ta ke jiyo kukan yaro, sai dai ba ta gama tantance muryar waye ba, a hankali qirjin ta ya fara buga wa, saboda tunano abubuwan da suka faru a cikin wannan gidan, hankalin ta ta ji ya na tashi, ta wani bangaren kuma tsananin zumudin ganin Ludhfi ya na neman ya rinjayi damuwar ta.

Ba tare da ta san sun shiga ba, ta ji muryar Sa'eed na fadin,

"welcome back home Baby Na,"

Cikin murmushi da nuna kula wa da kwadayin ganin fara'a a fuskar ta, sai dai Hakan bai samu ba, hasali ma wani busasshen murmushi ta sakar masa.

Da ta san in sun dawo Nigeria nan za a kawo ta, da gidan su ta je, Sa'eed ya ci amanar ta, ya boye mata abu mai matuqar mahimmanci kamar wannan, bari ta ga Yaron ta, dauke shi za ta yi, su bar gidan, ko ya maida su, can daya gidan shi ko ta koma gidan iyayen ta.

Fita ta yi daga motar ta na raba ido, ta na sake kallon gidan, ba laifi ya na nan cikin tsarin shi, fiye da yanda ta bari ma, sai dai shuke shuken gidan sun mace, nan kuwa bata sani ba, Ihsan ce ta fara neman mai bawa flowers ruwa, Hajiya mama ta kama su, aka kore shi.

Ba wanda ya fito tarar su a gidan, duk da bata sa rai ba, amma sai ta ji ba dadi.

Sa'eed ya gama shigar musu da kayan su, ta na nan tsaye ta na jiran ta ji motsin wani a gidan.

Har ta taka za ta shige sashen ta, ta hango Ihsan dauke da Ludhfi a hannu, kallon qafar shi ta yi ta ji gaban ta ya yi wani mummunan faduwa kamar zuciyar ta za ta Fado qasa, me take gani a qafar Yaron ta?

A gurguje ta qara sa inda suke har ta na tuntube , Ihsan na ganin MAHWISH duqe a gaban ta ta na zubar da hawaye, ta na kallon qafar Yaron, sai ta tura baki gaba, ta ce,

"Hajiya, ko kuma in ce Hajijiya ga Yaron ki nan, gwanda da Allah ya sa ki ka dawo, gaba daya na gaji da wahala, da dawainiya da Yaron nan, yaro Sam ace baya jin magana,.... Ke riqe shi ni, ina da wajen zuwa"

Da sauri MAHWISH ta karbi Yaron, nan da nan ya dena kuka ya hau bin ta da kallo, tabbas Maman shi ce, kuma ya gane ta,saboda hoton ta da Sa'eed kan nuna masa in ya zo, amma ina ta je da da baya ganin ta?

Ihsan na qoqarin barin wajen MAHWISH ta bi ta da sauri cikin rawar murya irin ta masu kuka ta ce,

"Me ya sami yaro na? Garin yaya akai ya qone? Ko ba quna nake gani ba anan?"

Ihsan ce ta bi MAHWISH da wani mugun kallo, Sannan ta ce,

"ke ki bani waje in wuce, mara kunya, duk dawainiyar da akai da Yaron baki gani ba, sai d'an ciwon da ya ji,"

Dogon tsaki ta ja, ta bar wajen, MAHWISH kuwa ba b'ata lokaci ta yi sashen ta da Ludhfi ta na kuka, qafa ta sale, da alama an jima da yin qunar dan kuwa ta dakko warkewa,  ba wanda ya sanar da ita.

Sa'eed ma kan shi da ya fito daga dakin su tsaya wa ya yi, ya yi turus, ganin qafar yaro a qone, kamar an tsoma ta a ruwan zafi saboda yanda ta yi shati, su kadai suka san da me suka qona shi, ko ya qone.

Cike da tsananin d'acin da zuciyar ta ke mata ta ce,

"Sa'eed, ka san Allah? Idan garin nan kafff gatan dangin ka ne, sai an daure duk wanda ke da sa hannu a qonewar yaro na, ko zan rasa komai nawa"

Ta na gama fadin haka ta dauki Ludhfi da ke so ya je wajen baban shi, tunda sun saba.

Hannu Sa'eed ya miqa MAHWISH ta banka masa harara ta shige daki, ta na shiga ta aje shi a Saman gado ta fashe da kuka,

"shikenan na dawo, gidan azaba gidan uquba, yanzu wanne mara imani ne ya qona Yaron da be ji ba, bai gani ba,ya Allah ka fitar da ni, ka min zabi da abinda ya fi alkhairi a rayuwa ta"

MAHWISHWhere stories live. Discover now