MAHWISH PAGE 18

50 3 0
                                    


"Za ka zauna ne ko za ka tsaya qare wa fuska ta kallo, har sai ka hango wanzamin da ya ciren 'yar wuya?"

Da sauri Sa'eed ya samu waje ya zauna, su Ihsan kuma suka kalli Hajiya Mama suka kashe mata ido, suka shige ciki.

Kicin kicin ta qara yi, alamar ba wasa,ta ce,

"Sa'eed na kira ka ne ba dan komai ba sai dan in sanar da kai ina so daga yau, abinci na ya dinga zuwa daga kitchen din matar ka Mashawi, dan kuwa bayan tafiyar ku Iya ta koma qauye, ita wannan bata iya kunun shinkafa da Iya ke min ba kullum, Sannan ga aikin gida, abun zai mata yawa, dan haka daga yau girki na ya koma hannun ta, in ka san ba za ta yi abincin ba, ka sanar da ni, ni in dinga shiga ina girka wa kai na,"

Wani irin mamaki ne ya kama Sa'eed, Wannan wace iriyar magana ce ma? A iya sanin shi duk sati biyu yake cefane, ko abinci ya qare ko bai qare ba zai kawo, kama daga kan nama, kifi, kayan miya da kayan shayi,omo, sabulun wanka da wanki, veggies, su indomie taliya, cuscus, da dai duk wani nau'i na abinci, shinkafa ce kawai sai wata, amma komai ko bai qare ba zai siyo ya aje musu, sannan me Tasneem take? A iya sanin shi mace ce da ta iya abinci, ga Ihsan d'in, kuma dama can Mahwish na kawo musu abinci, daga lokaci zuwa lokaci, mene ne na son a kallafa mata ya zama aikin ta?

"Ka yi shiru, toooo ba za ta yi ba kenan, amsar ta fito, ai shike nan, tashi ka je, bari ka ga na je na girka abincin dare na, tunda matar so ba za ta ba uwar miji abinci ba"

"Haba Hajiya Mama, ta ya za a ce mata ta ba za ta baki abinci ba, kawai dai ina mamakin wannan hukuncin naki ne, amma ba komai, bari na je na sanar da ita, daga yaushe ki ke so ta fara?"

"Yau mana, ko haka zan kwana da yunwa?"

"Allah ya kiyaye ki kwana da yunwa, bari na je,"

"Tom da kyau, a fada mata ta min kunun shinkafa, kullum.ni in ban sha shi ba, ji nake kamar ban ci komai ba"

"To Hajiya Mama"

Tashi ya yi, ya tafi sashen Mahwish, ya na fita su Ihsan suka tafi da gudu suka dira a kujerar da Hajiya Mama take zaune, suka sa dariya tare da fad'in,

"Se maamaaaa, da kyau Hajiya Mama ikon Allah, kowa ya ja dake ya kwana kuka, kin yi daidai, aikin ki na kyau"

"Ai yanzu za ta ga kala ta, tunda na ga take taken ta so take ta mallake min yaro, to gwanda na yi maganin abun, in ta rasa lokacin kan ta ta ya za ta samu na mallakar shi?"

"Babu"

Dariya suka sanya suka tafa, Tasneem ta miqe ta ce,

"Bari na tafi Hajiya Mama, na dan dora wani abu,"

"To maza ki je, ke ma ki dinga qoqarta wa dalla, sai ki zauna wani figai figai dake kamar ke aka gani aka koyi figar kaji ko zogale, ki maida hankali ke ma ki mallaki miji kin tsaya jiran a kashe a baki ki mora, maza kama hanya ki je ki"

Dik da maganganun Hajiya Mama sun mata zafi, amma gaskiya ne, dole ne ita ma ta san abun yi, ba zama zata yi ba.

Har ta fara baccin ta ya same ta a d'aki, rasa yanda zai yi ya tashe ta ya yi, motsin shi ne ya tashe ta, cikin mutsittsike ido ta kalle shi,

"Yah Sa'eed me ne ne? Ka na buqatar wani abu ne? Ni fa bacci na ke jiiiii"

Qarasa.maganar ta ta yi cike da shagwaba,kamar za ta yi kuka, ta qi jinin a dinga tsayar mata da bacci.

Zama ya yi a bakin gadon ya kama hannayen ta biyu, ya ce,

"Ammmmm, Baby Na, dan Allah wata alfarma zan roqa a wajen ki, ina fatan za ki yi min, domin hakan zai taimaka min wajen faranta wa mahaifiya ta, amma in kin ga za ki takura dan Allah kar ki boye min, ki sanar da ni,"

MAHWISHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora