Hakuri ya bata, ya nuna mata cewa, Xulaihah ta ce Sa'eed na iya bakin qoqarin shi akan yarinyar, to su yi hakuri, kar a ga rashin kawaicin su, in bata samu lafiya ba, nan da wani dan lokaci kad'an sai su je.
Hajiya ta so matuqa ta je ta ga 'yar ta, amma da yake mace ce mai tsananin biyayya, da kawaici, sai ta nuna babu komai, Allah ya ba wa Mahwish lafiya kawai.
Mahwish kuwa na can jiki ya qi dad'i, gashi mutanen gidan ko a jikin su, biki ma suke shirin tafiya Danbatta, ba tare da sun sanar da Mahwish din ba, duk da dai dama ba iya zuwa za ta yi ba.
Sa'eed ya kashe kudi matuqa a tafiyar da za su yi, saboda siya musu sabbin kaya, sabbin takalma, jakkuna , da mayafai, sai kudin kashewa, har da na liqi, Hajiya Mama sai fad'a take, kamar ta ci babu,
"Yanzu tun shekarar da ta wuce da nake ta masa maganar ya dauki driver da ya ji magana ta, da yanzu ma bi motar haya? Mutum na da arziki amma ba zai ci ba,ko uban wa yake tara wa oho tunda dai ya san ita wannan ba haihuwa za ta yi ba, ita kuma waccan ko b'atan wata ban ji ta yi ba, ni uwar shi in ban huta da kudin shi ba wa zai yi?"
Maganganun Hajiya sun dasa wa Tasneem wani tunani na daban, wanda ita ta bar wa kan ta sani a wanan lokacin.
Sa'eed dai qarshe Baba mai gadi ya ba wa mota ya kai su, sannan ya bada cigiyar a nemo driver, ko dan Hajiya Mama.
Da misalin tara na safe suka bar gidan Baba mai gadi ya tafi kai su.
Su na fita Sa'eed ya yi wa Sulaiman waya, ya sanar da shi zai iya zuwa yanzu ba kowa gidan, ba tare da b'ata lokaci ba, ya ce su bashi awa d'aya, zai zo, kafin ya zo Xulaihah ta haɗawa Mahwish ruwan wanka, Sa'eed ya shiga ya yi mata, ta rasa dalilin da ya sa in ya taba ta take jin wani irin tsabar tsanar shi, da qin shi, tare da wani irin qunci a zuciyar ta.
A haka ya gama.mata wankan ta na kuka, ya shirya ta, Sulaiman na zuwa ya ce,
"Ina so ka min izinin shiga lungu da saqo na cikin gidan nan,domin ina so in duba wani abu, in zargi na ya yi daidai, tabbas akwai abinda aka binne a cikin gidan nan, wanda yake sanya ta wannan ciwon"
"Na baka izini, Bismillah,Amma wa ka ke ganin zai wannan aikin? Lafiya qalou nake rayuwa da matata, mu ba wanda muke qi a ran mu, to wa zai mana wannan aikin?"
"Lallai Sa'eed ba ka san halayyar d'an Adam ba har yanzu ko? Wani ya na nan ba ya so ya ga ka na da qumbar susa, wani numfashin ka ne baya so ya dinga fita, wani kuwa gilmawar ka ce baya son gani, ka tafi duk inda za ka ka rayu, amma banda inda zai dinga ganin ka, kuma duk wannan tsanar da za a maka, ba ka taba cutar da kowa ba, haka halayyar wasu suke hatta da murmushi wanan ba a so ka yi, kai dai a kullum ka nemi tsari da maqiya,"
Su na tafe su na hira, su na zagaye gidan, sai Sulaiman ya yi shiru, a daidai lokacin da suka je qofar bathroom din d'akin Mahwish, a hankali ya taka ya bude qofar, ya na budewa ya hau dube dube, can ya d'aga kai sama, sai ya ga wani waje a ceiling ba guda d'aya, juya wa ya yi ya kalli Sa'eed ya ce,
"Ko za ka iya bani wani abu da zan iya takawa in duba saman nan pls?"
"Kwarai kuwa"
Fita ya yi ya samo side tables guda uku aka jera ya hau, ya leqa, ya saka hannun shi, sai gashi ya zaro layu har guda biyu (laya) layun kala biyu ne, daya an rufe ta da baqar fata, daya kuma an rufe da jar fata.
Ko da aka dakko aka bude sunayen Mahwish ne a kowaccen su, da Sa'eed, da surkulle wanda Sulaiman ne kawai ya gane ma'anar su, tashin hankalin da Sa'eed ya gani a fuskar shi ne ya sa shi kiran shi waje su tattauna, dan baya so su Mahwish su ji me za a ce, duk da sun ga me aka ciro, tayi ta yi ya bata a hannun ta ta gani ya qi.
Su na fita Sulaiman ya ce,
"A gaskiya Sa'eed sai kun kula sosai, dan kuwa ku na da mutanen da ba su son tarayyar ku, da gaske ake so a raba tsananin ku, ina jin tsoron abinda zai faru anan gaba, in har an fara da wannan, farraqu akai maku, Allah ne kawai ya taimake ku, amma tabbas da Mahwish bata zaune a gidan nan yanzu, sannan an mata sihirin da zai sa ta yi ta rashin lafiya, har sai ta bar gidan nan za ta samu sauqi, amma kar ka damu, zan hada maka wani magani na karya sihiri,inshaa Allahu, komai zai yi daidai"
![](https://img.wattpad.com/cover/292798077-288-k314670.jpg)
CZYTASZ
MAHWISH
RomansQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........