"Wai me ki ke cewa ne ki na ta magana da sauri kamar wadda ta zauna a kan garwashi?"
"Ce wa na yi Sa'eed ya san me ke faruwa, yanzu Malam ya kira ni yake sanar da Ni"
"Garin ya akai ya sani?"
Shiru ta yi ta latse wayar sakamakon ganin Sa'eed da ta yi fuskar shi jawur, daure fuska ta yi tamau, alamar ba wasa, waje ya samu ya zauna,tare da yin murmushin yaqe, sanan ya ce,
"Hajiya Mama na san dalilin da ya sa ki ka b'ata rai, ki dau wayar Aunty Zaituna na da magana da ke, gashi nan sai sake kira take,ko dake na ji ai ki na magana da ita kafin na shigo, ina godiya da kalar soyayyar da ki ke nuna min a matsayin ki na.mahaifiya ta, duk da ban san ta ina na gaza ba, ban san laifi na ba, a cikin kaso dari na.kyautata wa iyaye da 'yan uwa, na yi maku kaso tamanin,ashe na yi qoqari haka.ne? Mene ne laifi na Hajiya Mama? Dan Allah ki sanar da Ni"
"Kai ba ka isa ka sa ni a gaba da tambayar da ban niyyar amsa wa ba, tun farko na fad'a maka ba na son auren nan, ba na qaunar auren nan, amma ka dage sai ka yi, to ina mai gargad'in ka, tun wuri ka saki yarinyar nan, ta zauna a gidan su, ka sawwaqe mata, ko kuma ta dawo, duk abinda ya same ta, ita ta ja wa kan ta"
Kallon ta ya yi, ya na tsananin mamaki, da ta'ajibin kalaman ta, mahaifiyar shi, da ta haife shi ce ke masa irin wannan kalaman ido da ido ba boye boye.
"Yauwa, magana ta gaba, kar ka ga last time ka kai qara ta, wajen Yaya ban ce maka komai ba,in ka kuskura ka sake had'ani da d'an uwa na, to ka sani sai na yi maka bakin da ba a tab'a yi wa wani d'a ba,ina mai baka shawara da ka sake ta, ka zauna lafiya,ita ma ta huta,ka ji na fad'a maka"
Sa'eed ya rasa ma bakin magana, wato sun yarda kuma sun amince su azzalumai ne,masu shirka da Allah ne dan quntata wa rayuwar auren shi kawai,masu so su raba sunnar ma'aiki ta kowacce hanya su, ko da hakan na nufin sab'awa Allah ne kuwa,
Kamar daga sama ya ji Hajiya Mama na fadin,
"Ga 'yar uwar ka nan, yarinya kamar ta kashe kan ta saboda son ka, amma ka dauko yarinyar da za ta mallake ka, ta raba ka da kowa naka,in ka na tare da ita ba ka ji, ba ka gani,ko ganin ka ba ma yi, sai lokacin zuwa sallah ya yi, ka leqo a gurguje, a gaisa, da ka dawo ka koma gindin yarinya qarama ka tare, ba a sake ganin ka, sai an kira wata sallar,baka dauke ni da mahimmanci ba,dan haka kowa a bayan ta yake, hatta ni mahaifiyar ka,"
Bai san sanda ya katse ta ba cikin cikin fushi, ya ce,
"Hajiya Mama ta yaya zan fifita wata mace akan ki? Ke ce uwa ta, ke ce mace ta farko da nake wa komai a rayuwa ta, kafin 'yan uwa na su biyo baya, mata na ma ba na musu abu sai na muku, Hajiya Mama mene ne laifi na? Me Mahwish ta yi na mallaka ta? Farin cikin da nake samu ne matsalar ku? Sanin kan ki ne Tasneem rainon ki ce, ba ta min komai da ke nuna ni mijin ta ne, hatta da matsayin yaya bata bani ballantana na mijin ta, to ta ya zan daidaita tsakanin ta da matar da ke nuna min so, take kula da ni? Hajiya mama ta yaya zan iya daidaita soyayyar su? Ina sauke duk wani haqqin ta da Allah ya dora akai na, me ya rage da kuke so na yi wanda ban yi ba? Sanin kan ku ne ni ban taba son Tasneem a matsayin matar da zan aura ba, ina mata son 'yan uwantaka ne, ba son aure ba,Amma duk da haka na yi biyayya, me kuke so in yi? Me ku ke so daga waje na?"
Hawaye ne sosai suka balle masa, da sauri ya fita daga sashen Hajiya Mama, wadda ke ta zagin shi, da yi masa gori kala kala, akan haihuwar shi, da rainon shi, da kula da karatun shi, har ya girma ya yi abun duniya.
"Dan Iskan Yaro mara mutunci,wato Tasneem raino ce, shi ya sa ta yi rashin tarbiyya ko? Da kyau, yaro ace wai da girman ka amma mace ta susuta ka, ta maida kai mara mutunci, yaushe na tab'a fada ka mayar min? Duk abinda zan maka ba ka tab'a sa in sa da ni ba, amma akan waccan yarinyar me zubin gwanda dubi yanda ka ke min, ko zan yawo daga ni sai d'an kanfai a garin Kano sai yarinyar nan ta fita a rayuwar ka har abada"

ESTÁS LEYENDO
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........