MAHWISH PART 2 PAGE PAGE 8

38 7 2
                                    


Gaba daya kayan ta fitar daga ledar , kafin ta samu ta dakko wa Ihsan ta ta tsarabar, murmushi ta yi sannan ta miqa wa Ihsan din abinda ta siyo mata, d'an b'ata fuska Ihsan ta yi sannan ta kalli Sumayyah da alamun tambaya....

"Shin wannan na waye kuma"

"Naki ne mana, ko akwai wata Ihsan a gidannan bayan ke?"

"Kan uban can kayyasa, amma dai Sumayya ba a tab'a  raina min  wayo sama da yanda ki ka min ba a  duniya,ba kuma wanda ya taba cimin mutunci kamar yanda ki ka yi min yanzu a duniya, amma banga laifin ki ba, laifin Hajiya mama ne da ta dakko mana yar iska irin ki a matsayin matar aure ba tare da ta san ke wacece ba."

Sumayya ce ta sanya kuka a daidai lokacin da Sa'eed ya shiga, sannan ta ajiye chocolates din dake hannun ta, ta yi saurin karbar jug din dake hannun shi, ta na share hawayen da suka fita da kyar.

Tsoro da mamakin sumayya sun had'u sun hana Ihsan cewa komai, kamar daga sama ta ji muryar Sa'eed na fad'in..

"Ihsan wacece yar iskar? matar tawa ki ke kira da yar iska? ni na taba baki labarin mata ta yar iska ce ko a wajen uban wa ki ka taba ji? ashe rashin mutuncin naki har ya kai haka? to daga yau sai yau, kar in sake ganin qafar ki a sashen kowaccen su, ki kama kan ki a ashen Hajiya Mama, ko me ki ke so ki min waya, na haramta maki shiga cikin mata na ki na cin mutuncin su"

Sumayya ce ta dawo hannun ta dauke da jug din da Saeed ya shiga da shi ta ciko shi da zobo, miqa masa tayi sannan ta goge hancin ta da bayan hannun ta irin na mutanen da suka ci kuka dinnan.

"Gaskiya Abban Ludhfi ba za ai haka  ba, ai Ihsan kamar qanwa ce a waje na, tsakanin yaya da qanwa kuwa a ko ina ana samun sab'ani, muma sabani muka samu, dan haka ba za ka raba mu ba"

"Kin kuwa san me Kalmar yar iska ke nufi Sumayya?"

"Na sani, ka yi hakuri, a zato na kawo mata tsarabar brush, toothpaste da chocolates za ta ji dadi, saboda nima abinda na sai wa kaina Kenan, amma sai sabanin haka ya kasance, kaga ba laifin ta bane, laifina ne da  ban san me qanwar  tawa ta ke so ba,a bar maganar haka, kaga Maman Ludhfi na jiran ka"

"Au abinda ya faru ma Kenan, abun arziqi ki ka mayar tsiya Ihsan? ko dake ba yau ku ka saba cin mutuncin mata na ba,bar nan, dokar da na sa maki ta na nan, har sai kin sauya hali"

A sannan ne Ihsan ta samu bakin Magana...

"Ba halin da zan sauya yaya, ni da kaina na haramta wa kaina shigowa sashen nan, kuma gidan ka ma ka sa ido ka gani, nan da wasu watanni ba zaka sake gani na ba, ita kuma Hajiya Mama da ta dakko wannan macijiyar, ina fatan ta sare ta ita kadai, domin kuwa mu idon mu ya bude mun san wacece ita"

Brush din ta zubar a gaban Sumayyah ta daka mata wata harara, tare da sakin tsaki me qarfi ta fice.

Da sauri Sumayya ta kwashi chocolates za ta bi Ihsan da shi, Sa'eed ya kira ta.

"Dawo nan, har yanzu na kula baki san su waye Ihsan ba, amma a hankali za ki san su"

Jimm ta yi, a ran ta ta na ayyana cewar

'Ni kuwa na san su waye Ihsan, Zaituna da Hajiya Mama, kuma in shaa Allahu sai na yi maganin su zan huta'  A zahiri kuwa ta ce..

"Da ka barni na miqa mata tunda har da ita na dakko"

"No need, ku shanye, ke da wancan shazumamun dan naki, bani jug din, na san ta matsu na koma yanzu.
Sai da safe"

"ka bata hakuri na san za ta ga ka jima, a shafan kan yaro na, a ce masa ina son shi"

Sa'eed ne ya kafe ta da ido, sannan ya ce,

"Baban shi fa, wane saqo za a bashi?"

Sunkuyar da kan ta tayi qasa dan kunya, sannan ta ce..

"A ce wa baban shi, ya kula da Maman shi, sannan ina son Maman shi"

Sa'eed d'an kwab'e fuska ya yi irin na yara, sannan y ace..

"Ok na gane ni ne baki so a gidan nan, sai da safe"

Murmushi ta yi, sannan ta rufe qofa bayan ya fita, a hankali ta furta

"Ina son ka Abban Ludhfi da dikkan zuciya ta, ni kai na mamakin faruwar hakan nake,ban san yaushe na fara ba, amma na ta'allaqa hakan da qoqarin ka na kula da ni, da nuna min ka na so na, duk da na san zuciyar ka ka mallaka wa Mahwish, ba zan maka dole ba, ba kuma zan taba furta maka ba, har sai na gamsu kana so na kaima, domin kuwa ka tattara soyayyar ka kaf, ka bawa Mahwish,sorry ba laifin ka na gani ba, ta cancanci ka so ta, amma ina fatan wata rana nima zan samu gurbin soyayya a ran ka, na gode da mutunta ni da ka ke yi, hakan kadai ya wadace ni a yanzu"

Gishiri gishirin da ta ji a bakin ta ne ya bata tabbacin kuka take, ba tare da ta sani ba, hawayen ta ta share, sannan ta koma ta dauke brush din da Ihsan ta watsar a qasa ta fashe da dariya, ba tare da ta shirya wa hakan ba.

"Sokuwa, a zaton ta ita ma na kawo mata kayan kwalama, hum to ba za ki ci ba, sai dai ki wanke bakin ki na rashin kunya da kwadayi"

A can sashen Hajiya Mama kuwa sun yi tambayar duniya Ihsan ta qi cewa komai daga baya ma sai ta tashi ta koma daki, ta bar su a wajen suna tunanin ko saurayin nata ne ya bato mata rai.
Hajiya Mama ce ta gyatsina fuska ta ce,

"Ke rabu da ita wahalalliya, in saurayin nata ne ya bato mata rai su je can su qarata, ba dai an kusan auren ba, sun cinye kan su"

Da haka kowa ya kama hanya dan zuwa kwantawa  ba tare da sun mata fadan jimawa a can wajen zancen ba.

Washegari bayan Saeed ya fita , Sumayya ke ba wa Mahwish labarin abinda ya faru, sukai ta dariya, Mahwish ta ce,

"A gaskiya Sumayya baki kyauta wa qanwar ki ba, haba, kyautar brush kamar wadda kk ji bakin ta na wari."

Dariya suka fashe da ita, sannan suka ci gaba da tsokanar junan su.
*************************"****

Hidimar bikin Ihsan ta taso gadan gadan, daidai misali Sa'eed ya kashe kudi, da taimakon  Sumayya sukai ta siyan kayyakin, dan kuwa ta yi baqe baqe cikin kissar ta da siyasar ta an damqa mata komai a hannu, dan haka Zaituna bata samu damar yin camama ba, Mahwish na fama da laulayi, lafiya bata samu ba, ko ta samu Hajiya Mama har yanzu ba sake mata take ba, dan haka ta na gefe ta na fama da kan ta, Hajiya Mama kuwa na ta jin dadi ta na yaba wa Sumayya akan namijin qoqarin da take.

Tun ana sauran wata daya su Zaituna suke damun ango akan ya nuna musu inda za a saka amarya amma shiru,  Ihsan ta yi duk wani abu da Zaituna ta umarce ta ta yi amma shiru ka ke ji, dan haka ana sauran kwana hudu biki Zaituna ta fita da kan ta harabar gidan ta same shi, sai zuba surutu yake, kallon shi ta yi sama da qasa sannan ta ce,

"Kai bawan Allah, wajen ka na zo, wai za ku nuna mana inda za a saka yarinya ko baza ku nuna mana ba, mu san me ake ciki?"

Da sauri ya durqusa ya hau gaishe da Zaituna, ita kuwa ta dauke kai gefe, tare da kama qugu ta kalle shi, da alamun kai nake sauraro.

" Ammm dama Aunty na fada mata wajen yau in shaa Allahu ba damuwa kuna iya kai kayan kowanne lokaci."

" Ai ko  ba ka fada ba kam kaya za a kai su, na gani na fad'a ma kuwa, tunda ba zai yu mu kaita  ba kayan daki ba ko?"

Ta fada cike da rashin mutunci tai gaba ta na ci gaba da fadin maganganu son ran ta.
Washe gari kuwa ta debi qawayen ta da na Hajiya Mama, suka tafi dan ganin waje, suna isa ………

MAHWISHWhere stories live. Discover now