MAHWISH PAGE 13

62 5 0
                                    

Tsalle ya yi a saman gadon shi, ya hau murna, tare da yin
Kissing d'in wayar shi, lokaci d'aya kuma ya nutsu, ya zauna,

"Sa'eed ka shirya, zan zo maka da abun mamaki gidan ka, za ka ga qarfin soyayya, wuyarta na jaddada mata soyayya ta a gare ta, na kuma nuna mata a aikace, kashin ka ya bushe,"

Ya so ya kira ta, amma ya qi, dan kuwa zuwan bazata yake so ya mata, ya san ranakun da Sa'eed d'in ya fi yin tafiya ai, dan haka zai je ba tare da ya sanar da ita ba, sai dai kawai ta gan shi.

Tun daga wannan lokacin ya fara shirye shiryen zuwa gidan Mahwish, komai sabo yake siya, dan ya burge ta, ya kuma sai mata tsarabar kayan kwalam da maqulashe, dan ya san ta akwai son ciye ciye.

Kwana biyu kenan da ganin message d'in na Mahwish, Salim ya yi shiri da yamma tsaff, kamar mai zuwa gasar zaben kyawawa, hannun shi riqe da wata 'yar jaka mai kyau da ban sha'awa, ya haye machine d'in shi, sai gidan Sa'eed.

Ya na zuwa ya leqa, mai gadi ya gan shi ya na leqe ya taso ya na tambayar shi lafiya?

"Eh na zo ne wajen qanwa ta, ina so na yi mata bazata, shi ya sa ban kira ta ba, ina fatan su na nan ko?"

"Wace ce qanwar ka? Ko dake da gani ma babu tambaya Amarya ce ko? Dan ga kamanni nan,...eh ita ta na nan, amma shi Alhaji da Hajiya Mama da Hajiya Tasneem ba sa nan, sun je ta'aziyya, ita d'aya ce a gidan"

'perfect' shi ne abinda Salim ya fad'i a ran shi, a zahiri kuma ya ce,

"To bari in shiga mu gaisa, ba jima wa zan ba nima,"

"To Bismillah."

A cikin gidan bayan flowers ya yi parking machine din shi, dan kuwa ba kowa ne ma zai kula da shi ba, in ba an nuna ma mutum ba, ya na gama parking ya tambayi mai gadi ina ne sashen ta, ya ga sashe uku, nuna masa ya yi ya koma bakin aikin shi, shi kuwa ya gyaggyara ya isa bakin qofar gidan.

Kwankwasawa ya yi a hankali, ya jira, shiru shiru bata buɗe ba, dan ta na ciki, ta na tunanin ko Sa'eed ne, ita ta gaji da fad'a, dan kafin su fita sai da aka yi ita da Tasneem, akan tafiyar ba a sanar da ita za a je ba, kawai ganin su ta yi sun shirya, kawai ya ce ta je za su ta'aziyya, ya kwana a wajen ta, amma bai sanar da ita ba, shi ne ta ce ba zata ba, Tasneem ta nemi fad'a mata ba sukari ta wanke ta tas,bai matsa mata ba, suka wuce da Hajiya Mama, ya yi qaryar kan ta na ciwo bata jin dad'i, duk da cewar Tasneem ta so qaryata wa, amma ba hali, tunda a gaban shi ne.

Sai da ya sake bugawa ta tashi a hasale ta bude qofar,ta na ganin shi, wani irin farin ciki ya baibaye ta, a guje ta nufe shi, ta fad'a jikin shi ta na murna, tare da fad'in,

"Yah salimmm"

Mai gadi na can na hango su, ya na washe baki, ba tare da sanin matsayin Salim a wajen Mahwish ba, ya ji sun burge shi, da alama akwai shaquwa a tsakanin yaya da qanwar ta shi, ciki suka shiga, sai murna take, Salim kuwa ba abinda yake sai kallon jikin ta da ya murje ya yi kyau, irin na amaren da ke hutawa a gidan miji.

Daki ta nufa ta yafo mayafi akan qananan kayan da ke jikin ta, dan kuwa sun bayyana surar jikin ta, kitchen ta je ta d'ebo masa abinci da abubuwan sha, bakin ta ya qi rufuwa.

Shi ma Salim din kan shi cike yake da farin cikin ganin ta,

"Yah Salim wannan shi ake cewa zuwan bazata, kuma na ji dad'in shi matuqa, ya gida? Ya su Goggo? Ya ka ke?"

"Kaiii Mahwish, irin wannan farin ciki haka, lallai zargin da nake na kin dena so na ya tafi,na gama tabbatar wa ba wanda ki ke so bayan ni"

Murmushi ta yi, ta rufe fuskar ta, ta na jin dad'in kalaman shi, wayar ta ce ta fara qara daga ciki, tashi ta yi ta ce masa,

MAHWISHWhere stories live. Discover now