MAHWISH PAGE 7

47 3 0
                                    

💅🏻  *MAHWISH*  💅🏻


*BY HAERMEEBRAERH*

PAGE 7:

Wani irin baqin ciki ne ya kama Sa'eed, cikin takun da bai fi biyar ba ya isa gaban ta, d'aga kai ta yi suka yi ido hud'u da juna, b'ata fuska ta yi, ta murgud'a baki, sannan ta ce,

"Yah Salim yaushe za ka zo?"

Da qarfi Sa'eed ya sa hannu ya fizge wayar ya wurga ta saman gado, sannan ya kalle ta da idanun shi da suka kad'a su ka yi  jajawur, ya ce.

"Mahwish ! Kar ki bari rai na ya b'aci akan abubuwan da ki ke yi da wannan banzan yaron, kin san mene ne aure kuwa? Kin san wane ne miji? Kin san matsayin abinda ki ke aikatawa a musulunci? Yanzu ke ba abun kunya bane a ce kina wulaqanta mijin auren ki? Ke wace iriyar yarinya ce mai kafiya?  Mahwish ki sani duk randa yaron nan ya tako qafar shi ya zo min gida, sai na damqa shi a hannun hukuma a matsayin ya zo kwartanci,"

Cike da fushi ya juya zai tafi, ta miqe ta na tafi, cikin rashin kunya da tsiwa, ta isa gaban shi, sai da ta zagaye shi ta na masa wani kallon raini sanan ta kama qugu ta tura d'anwalin ta a gaban goshin ta ta ce,

"Ka gama? Na ce ka gama tattabara Sarkin aure, da an magana ka hau cewa wani aure aure, to sannu ayu, kaiii Sa'eed dan Allah in ka haifu cikin uwa da uba ka saken a yanzu, ka gani in ban samu wanda zai auren ba,ina da Yah Salim a aje in ka cika haifaffe ta auren sunnah ka sake ni, kuma Yah Salim zai zo gidan nan dan Allah in ka ga dama ka kai shi barikin sojoji inda za su maida naman shi kamar na rago a mahauta, sannan na san kai d'an zafin zuciya ne, aikin banza kawai,"

Juyawa ta yi za ta tafi, da qarfi ya rufe qofar dakin ya danna key, cikin zafin nama ya fizge ta jikin shi ya matse ta da kyau, wata iriyar zufar wahala ce ta dinga keto wa Mahwish, hankalin ta ya yi bala'in tashi, kyawawan idanun ta masu dogayen gashi take ta qiftawa baki na rawa, ta kasa ce masa A, Sa'eed kuwa ba abinda yake kalla sama da qirjin ta da suka yi sama su na gogar nashi, cikin mintinan da ba su kai biyu ba ya kashe fitilar d'akin ya wurga ta saman gado,wata gigitacciyar qara ta saki, da ta sanya ni toshe kunnuwa na na rintse ido na na yi waje.

Duk abin nan da ake Salim bai kashe wayar ba sai da katin shi ya qare, jin qarar Mahwish da nishin Sa'eed ya gama tabbatar masa da abinda zai wakana, wani irin baqin ciki da tsanar Mahwish da Sa'eed ke huda shi, ya za ta masa haka? Ita ba za ta iya kwatar kan ta bane?

Ni kuwa Ina nan zaune parlour na dinga jiyo zagi kala-kala kamar a sabon gari, ihu da tarin Mahwish ne kawai ke tashi, na kai kimanin awa d'aya a wajen kafin na ji ta dena kuka, shirun ne ya yi yawa har ya sanya ni leqa wa na ga me ke faruwa, ina shiga na ga Sa'eed durqushe gaban Mahwish, ya na watsa mata ruwa, daga shi sai jageren tambo, (gajeren wando🤭)

Da wani gigitaccen ihu ta farfaɗo,sannan ta kalli Sa'eed ta takure waje daya ta buga masa qafar ta a baki, nan da nan kuwa jini ya ɓalle,bai damu da dukan da ta masa ba, idanun shi sun nuna tsananin nadama da tausaya wa a gare ta, duba gadon nasu ya yi inda ta tashi, ya ga yanda ya ɓaci da jini, (ba lallai bane a ga jini a zanin gadon amarya, domin kuwa kowacce mace daban take da 'yar uwar ta, abun kamar dankali ne, kowane da shape da size din shi, ke dai ki tsarkake rayuwar ki, kar ki bi kowa kafin aure, in ki ka kiyaye Allah zai kiyaye ki)

Qarfin da ya sanya mata ne ya yi resulting samun wannan jinin, qasan zuciyar shi kuwa ya na ta istighfar saboda zargin su ita da Salim da ya fara yi, wani b'angaren na ran shi kuwa falll farin ciki, ashe Allah zai dube shi ya bashi nagartacciyar macen da bata taba aikata zina ba? Godiya ya dinga yi wa Allah, sannan ya hau bawa Mahwish hakuri,ba abinda take sai kuka, cikin ran ta kuwa ji take duk duniya ba wanda yake kin wani sama da yanda take qin Sa'eed, da ace in ka kashe mutum ba komai, to tabbas da za ta sa wuqa ta farke qirjin shi ta fito da zuciyar shi ta yi gunduwa gunduwa da ita.

MAHWISHWhere stories live. Discover now