MAHWISH PAGE 38

25 3 0
                                    


Kafin ta bude Xulaihah tai saurin karb'a, ta bude, ta na gani ta miqa wa Hajiya, salati ta sanya, sannan ta yi wa Allah godiya ta ce,

"Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, ya Allah mun sani dukkan abinda ya samu mumini daga gare ka yake, jarabawa ce, ya Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawa, ka sa ya zame mana kaffarar zunuban mu, Alhamdu lilLAAH, Allah ka sa hakan shi ne ya fi alkhairi"

"Hajiya Mai me ne ne a takardar?"

Miqa mata Hajiya ta yi, ta wuce d'akin ta, Mahwish na gama karanta wa ta sa dariya, kallon mamaki da tsoro Xulaihah ta bi ta da shi, kar dai ta haukace ne saboda damuwa !

"Hajiya ! Hajiya zo ki ga Yah Mahwish!"

Da gudu Hajiya ta leqo , ta ga Mahwish na dariya har da hawaye, salati ta sanya, ta duqa gaban ta, ta fara karanto addu'ar da ta zo bakin ta,cikin dariya Mahwish ta ce,

"Hajiya lafiya ta qalou, wato shashancin Zaituna ne ya ke ban mamaki, muguwar jaka ce, da ba ta abu da tunani, wai ni za ta yaudara, wannan rubutun shigen nashi ne tabbas, wani aka sa ya kwaikwayi rubutun shi, amma ba shi ya rubuta ba, haba, shekara a qalla uku mun shiga ta hud'u tare ace ban san rubutun miji na ba?"

Sai a wannan lokacin Xulaihah ta karba ta duba sosai, tabbas itama ta san rubutun Sa'eed wannan ba rubutun shi bane, to wannan wanne irin wawanci ne da wasan yara su zaituna suke, ko ita da take yarinya ba za ta yi haka ba, ballantana su uwayen ta.

"To bari dai Abban ki ya dawo, dole a kira shi, in ya na son ki ya zo ya dauke ki, ya kuma sama maki inda za ki zauna ko da gidan da za a saka ki ne da fari aka fasa, ko ya kai ki wani, ai ba gida d'aya yake da ba, na soma gajiya da halin mutanen nan"

Tattauna wa suka yi ta yi, suna aikin maraice, har mahaifin Mahwish ya dawo, shi ma da ya gani, ya ji haushi, ya ce wannan ai wasan yara ne, ba hankali a lamarin,nan take ya kira Sa'eed, Mahwish na zaune cikin ran ta, ta soma karaya, anya ba shi ya rubuta ba, dan kuwa gaba d'aya wayar shi bata shiga.

Abu kamar wasa har sai da aka kwana uku, ana ukun ne ya kira Mahwish ta qi dauka dan kuwa mahaifin ta ya kira ya qi daga wa sai kuma ya kira ta?

Message ya mata ya na bata hakuri, tare da karbar laifin shi, ya kuma tabbatar mata da tafiyar gaggawa ce ta taso masa zuwa Ciro, Hajiya Mama kawai ya samu ya sanar wa, ya kira wayar ta bata shiga ba, shi ya sa.

Jin cewa baya qasar ne ya sanya ta yi masa message, ta ce ya kira Abban su, ya na son magana da shi.

Ai kuwa ta na nan zaune a tsakar gida inda take shan iska, ta ji mahaifin ta na waya, ya na ba wa Sa'eed umarnin ya zo, a ranar ba sai gobe ba, komai dare ya na nan ya na jiran shi.

Haka kuwa akai, Mahwish na ba wa Ludhfi abinci Sa'eed ya zo, ta na jin shi ta qi fita, direct parlour ya shiga, suka zauna da Abban ta, Abban Mahwish ya ce,

"Sa'eed a gaskiyar magana, ina son 'ya ta, na gaji matuqa da musguna mata da ake, 'yan uwan ka sun kawo wannan takardar ta saki, sun ce in ji ka, shin da gaske ne? Dan kuwa matar ka ta ce qarya ne"

Karba ya yi ya duba, sannan ya yaga ta, ya damqe a hannu, ya ce,

"Abba dan Allah ku yafe min, haka ba za ta sake faruwa ba,kuma game da wannan takarda, ba ni na rubuta ta ba, ban san da ita ba, Mahwish ta yi gaskiya, wannan ba rubutu na bane, an dai kwafi rubutu na, amma ba shi ba ne,"

"To masha Allahu, ka na son matar ka ko za ka saw....."

"Ina son mata ta Abba, dan Allah ka yafe min abubuwan da na aikata a sane na ko bisa kuskure, in shaa Allahu Mahwish ba za ta koma wancan gidan ba, tare da ita zan koma sabon super market dina, akwai gida a bayan wajen, ba nisa da super market din, dan da qafa ma mutum zai je ya dawo bai gaji ba, amma ina neman alfarmar aban nan da wani weekend sai na zo mu tafi"

MAHWISHWhere stories live. Discover now