MAHWISH PAGE 43

24 2 0
                                    

Shiru shiru Sa'eed bai dawo ba har yamma, Mahwish ta yi jira har ta ji ba dad'i, wankan ta biyu, dan ta na tunanin ko sai la'asar zai dawo, amma shiru, sai can bayan Magrib ya dawo, Mahwish har ta cire ran zai dawo a ranar, ta tattare abincin da ta masa ta saka a freezer, ta na ta kuka, ko da ya dawo ba ta yi wani murnar ganin shi ba, kamar yanda shi ma, bai yi wani d'okin ganin ta ba, duk da abun na bashi mamaki yanda gaba d'ayan su, suka nuna halin ko in kula da junan su, a duk sanda ya yi tafiya, ko ta yini ce, kalar soyayyar da suke nuna wa juna abun burgewa ce ga kowa,amma yau ba wanda ya yi d'okin ganin d'an uwan shi,tabbas ya yi farin cikin ganin ta a ran shi, amma ya kasa bayyana mata hakan, ita ma ta kasa yi masa magana akan jimawar da ya yi.

Bayan kwana biyu, Sa'eed abu sai gaba gaba yake, ba ya neman Mahwish, duk son shi da ayi tarayyar aure, ya dena shisshige mata kamar da, gashi sai ya dinga satar jiki ya na  amsa waya a sirrance, wanda tuni Mahwish ta gano da Mommy ya ke waya.

Watarana su na zaune su na cin abinci, kawai sai ta yi masa waya, ta ji bai dauka ba, sai ta biyo da saqon soyayya , Mahwish duk na kallo, dan kuwa wayar na daf da ita, taqi miqa masa, Sa'eed na so ya dauki wayar kunyar ta ta hana shi, ba tare da ya kammala cin abincin ba, ya dau wayar ya miqe, ya na wani basar wa, ya ce,

"Akwai abinda za a siyo ne?"

Murmushi kawai Mahwish ta yi ta ce,

"Ba komai, ka je kawai, in kun gama wayar  ka gaishe ta"

Kunya ce mai tsanani ta kama Sa'eed, dan kuwa ya tabbata Mahwish ta gama gano shi, kan shi ya ɗan sosa, ya fice da sauri.

Ya na fita Mahwish ta share hawayen da ya zubar mata, yanzu wai ita sa'eed ke juya wa baya akan wata? Gaba d'aya ya sauya, ba wani tarairaya, ba wata soyayya, ba kula wa kamar da, me ya ke faruwa ne?

Sa'eed shi kan shi, ya rasa me ke faruwa da shi,Allah Allah yake weekend ya yi ya koma wajen masoyiyar shi Mommy, shin da gaske masoyiyar shi ce? Ko dai maqiyyiyar shi? Ba zai iya tantancewa ba, shi dai kawai abinda yake ji a yanzu shi ne, dare da rana ya dinga ganin mommy a kusa da shi, ya dinga jin kalaman ta masu dad'i a kunnen shi.

Mahwish kuwa da ta tattauna abinda ke faruwa da ita da Xulaihah, nan take Xulaihah ta bata shawarar ta yi addu'ar ruqya a ruwa ko a abincin da yake ci, ta bashi, inshaa Allah yau da gobe komai zai daidaita.

Haka kuwa aka yi, kafin sati ya zagayo, Sa'eed ya dawo hayyacin shi, ya na kuma dawowa hayyacin shi, zazzaɓi da ciwon kai suka rafke shi, a ranar bai kwana gida ba, sai asibiti, Mahwish ta yi kwanan damuwa matuqa, ganin halin da ita ma take ciki, na rashin isasshiyar lafiya ne, ya sanya abokin shi  zama a wajen shi, ita ta koma gida.

Wata rana ta kai musu abinci asibitin, su na zaune su na hira, sama sama,saboda ya na dan jin jiki, cikin tsananin tausaya masa, ta miqe za ta koma gida, jiri ya debe ta, ta zube a qasa, qarshe dai sai gado aka bata a wajen.

Mahwish ta sha qarin ruwa wajen leda uku, kafin ta samu jikin ta ya yi normal, ba tare da ta kwana ba, aka sallame ta ta koma gida.

Sa'eed ya so a sallame shi ya je ya kula da ita, amma bai ji sauqi ba, ya na ji ya na gani ta tafi ita daya.

Maqotan ta ta shiga suka ara mata yarinyar su qarama, ta zauna da ita.

Da sassafe kuwa sai ga Sa'eed ya koma gidan,saboda ya kasa zama a asibiti, dole suka rabu da shi, ya dawo gida.

Tare suka ci gaba da jinyar junan su, cikin ikon Allah kuwa su ka samu sauqi a tare.

Wataranar laraba tun asuba wayar Sa'eed ke ringing, Hajiya Mama ce ta ke ta kiran shi, ta yi masa missed calls takwas, bai dauka ba, Zaituna ma haka, Mommy ma ta kira ba adadi, ga kuma Tasneem a gefe, ita har da messages ta bari.

MAHWISHWhere stories live. Discover now