Ko da suka isa gidan Hajiya Mama tun daga gate suke jin qamshin turaren wuta, Baba mai gadi sai hangame baki yake, kamar yanda ya hangame gate din gidan, Sa'eed Murmushi kawai ya masa, ya fice daga motar, sashen Mahwish yake ta kallo, dan ba ya so a ga rashin kyautawar shi ma, da can ya yi, tsaye yake bai san ina ma zai nufa ba, ya ga Hajiya Mama da kanta ta kama hannun amarya, ta hada da nashi, sannan ta musu jagora zuwa sashen su, har quryar daki ta kai amarya ta aje, dangin amarya lamarin ya musu dad'i kwarai matuqa, sai yaba uwar mijin suke, ango kuwa toilet ya shige, ya bar amarya zaune bakin gado ta na kuka, saboda ba yarinya bace,za ta kai talatin da d'aya, tabbas ta fahimci an musu qarya, da aka ce shi ya gan ta da kan shi ya ce ya na so, bai mata magana bane saboda ya ga a kan hanya take, to dai ga ango na nuna mata halin da ta tabbata na rashin so ne.
'Yan uwan ta kuwa sai zaga cikin gidan suke su na saka albarka, tare da yi ma' Yar uwar su fatan zama dindindin mutuwa ta raba.
Hajiya Mama ta na ganin sun kammala kallon gidan amarya za su zauna ta ce,
"Ai ba zama za ku yi ba, ku taso mu je ku ci abinci ku sha, sannan anjima akwai qawaye na da za su zo duk sai ku gaggaisa da su, kunga ko bangaren uwar gidan ma baku shiga ba,"
Cikin jin dadin karamcin Hajiya Mama suka bi bayan ta.
Suna shiga sashen Mahwish suka sau baki, masha Allah, ko ina fes waje na kyalli kamar nan ne sashen amaryar, mahaifin amarya ma ya yi qoqarin sa mata kaya sosai, amma gaskiya na Mahwish ya fi kyau da tsada, yan mata suka gani kyawawa guda biyar su na ta musu fara'a, ga ruwan sha da lemuka sun kawo musu, cikin ladabi da girmamawa suke gaishe su, bakin qofar dakin mahwish suka bi da kallo dan ganin wa ke taho wa, saboda qamshi da qarar kayan adon da ta sanya a jikin ta, dauke da Ludhfi ta taho, ya na ta kukan shagwaba a hannun ta, ta na ganin su ta saki murmushi, tare da samun waje ta zauna, gaisawa suka fara yi da matar, yaron na ganin Hajiya Mama ya bi ta da kallon sani,Hajiya Mama kuwa sai wasa take masa ta na kiran shi, ya qi zuwa.
"To jama'a ga uwar gida nan fa sarautar mata, ita ce matar yaro na din, sunan ta Mashawi"
Yanayin yanda Hajiya Mama ke fara'a da raha ya ba wa su Mahwish mamaki, amma basu nuna ba, sai Khaleesat ce ta yi murmushi ta ce,
"Hajiya Mama Mahwish dai ba Mashawi ba ko"
"Ke arrr kun ji da shi, ni wannan suna ba iya fad'ar shi na yi ba, na rasa me ya sa ba a zabar suna kamar su Bilkisu, Aisha, Maryam, a sa wa yara, sai an yi qaqale,"
Dangin amarya dariya suka yi, dan sun dauka duk a rahar ta ne, su kuwa su Mahwish sun san hali dama.
Goggon Amarya ce ta ce,
" Allah sarki ashe ma ba babba bace sosai, ai na yi zaton za ta girmi Sumayya ma, amma da alama Sumayya ta girme ta, to ubangiji ya baku zaman lafiya ya kare ku daga dikkan fitina, sharrin shaidanun aljanu da shaidanun mutane Allah ya maku tsari da shi, Allah ya kawar da masu ziga da munafukai a tsakanin ku, Allah ya hada hankulan ku ya bashi ikon yin adalci a tsakanin ku, Allah ya hore masa abinda zai riqe ku ameen"
Mahwish ta ji dadin addu'ar sosai, sai amin take fadi Hajiya mama jin addu'ar tai kamar da biyu ake yin ta, dan haka tsuke baki ta yi, ta yi gum, a ran ta fadi take,
'Ko amin din ma ba zan ce ba, in ma dan ni kuke yin ta ba karbuwa za tai ba, se Mashawi ta bar gidannan, ai ina da labarin' yar taku dik inda ta je se ta fidda kishiya,'
Bayan nasiha da addu'o'i Hajiya Mama ta ja su sashen ta, anan fa suka tarar da tagomashin kayan azziqi Zaituna da Ihsan da suka riga suka yi gaba, tun da suka dawo, sun lodi kayan flour da akai, irin su cincin dubulan alkaki, da nama, sun kai daki sun boye, dangin amarya sun ga karamci tabbas sun yaba kwarai, sun ci sun sha, sun goge baki da kaji, sannan an qulle musu za su yi guziri.
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........