MAHWISH.
RUBUTAWA HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️
PAGE 49.
Gidan ba kowa sanda Sa'eed ya qarasa, kamar sun samu masaniya a game da zuwan shi, juyawar nan da zai yi dan koma wa inda ya fito, su ka yi karo da Tasneem da ta shiga kamar sabuwar mahaukaciya.
Zube wa ta yi a gaban shi, cikin matsanancin kuka da tashin hankali, ta na bashi hakuri, Maryam da ke maqale ta waje ta na ci gaba da daukan komai a video.
Cikin fushi Sa'eed ya sa qafa ya shure ta, ya nuna ta da yatsa, sannan ya ce,
"Tasneem na tsane ki, na tsani duk wata hulda ko alaqa da za ta sake hada mu, ki rufa wa kan ki asiri ki bar bi na, na datse duk wata alaqar aure da ke tsakanin mu, dan haka ki bar bi na, wai Shinn ya akai ma ki ka shigo? Ban ce kar a bar ki ki shigo ba? Ba kina da gidan da ki ka cuce ni ki ka gina ba? Me ya kawo ki nan?.... Baba mai gadi! Baba mai gadi!"
A guje mai gadi ya isa, ya durqusa, sannan ya fara bada hakuri, tare da qoqarin kama Tasneem ya fidda ta, Sa'eed dauke kan shi ya yi, tare da sanya hannun shi a aljihu, dan nemo wayar shi, ya na so ya kira Hajiya Mama ya ji ina suka tafi.
Tasneem na ta kuka ta na kiran sunan shi, ta na roqon ya ce mai gadi ya kyale ta, ita ma gidan su ne, amma ko juya wa bai ba.
Mai gadi na gab da fitar Tasneem daga gate din gidan, motar su Hajiya mama na tsaya wa, an debo qawaye har biyu, sai Zaituna da Ihsan, driver'n su Hajiya Mama ta tsayar, ta fita ta na mamakin ganin ana jan Tasneem za a fidda ta a gidan, duk kuwa da cewa ta na fushi da Tasneem din akan abubuwan da take yi na nuna ita wata ce yanzu, Hakan ba yana nufin bata son ta bane, ba kuma za ta bari a wulaqanta ta ba, ko ba komai 'yar'yar uwar ta ce.
"kai me nake gani haka wai qarfin hali ɓarawo da sheqa wa masu gida sallama? Gidan uwar wa za ka kai min ita da ka ke jan ta kamar ka samu buhun rogo, ke zo nan"
A guje Tasneem ta fada jikin Hajiya Mama ta na kuka, ta ce,
"Hajiya shi kenan ni kam na shiga uku na lalace, rayuwa ta ta zo qarshe, mun shiga uku daga ni har ku Hajiya Mama"
"Tasneem zan ci uwar ki 'yar Aba in baki fadan me ya faru ba yanzun nan, zuciya ta gab take da ta buga tsabar rudanin da ki ka sanya ni ciki"
Bude baki Tasneem ta yi za ta yi magana suka hango Sa'eed ya fito daga sashen Hajiya Mama, fuskar nan kamar hadari, a iya rayuwar Hajiya Mama da Zaituna basu taba ganin shi a irin wannan yanayin ba, gaba dayan su sun sha jinin jikin su, ga kuma qawayen Hajiya Mama 'yan ganin kwaf da suka baje baki da hanci dan jin me ke faruwa, duk da cewa ran Sa'eed a bace yake, bai manta wace ce Hajiya mama a wajen shi ba,dan haka ba zai zubar mata da mutunci a gaban mutane ba, da taimakon Allah, da taimakon rashin samun su a gida da bai ba tun zuwan shi, fushin da yake ya ragu, wanda da ace ya same su sanda ya shiga gidan, da ba a san me zai faru ba.
Dan haka ko ci kan ku be ce musu ba, ya bude sashen MAHWISH ya shige, ya na shiga ya zube a wajen, ya na zubar da hawayen baqin ciki, ba tare da ya san sautin kukan shi na fita ba.
Hajiya Mama da kyar ta sallami qawayen ta da suka dawo daga yawon bin bokayen su, dan kuwa sai da ta bude musu ido sannan suka tafi, sun so su ji wace badaqalar ake a gidan.
Ko da ta shiga gidan bata bi ta kan Sa'eed ba,dan kuwa ba qaramin sanyi jikin ta ya yi ba dan ganin idanun shi.
Zaituna kuwa ta jima da fara karyar da zufa, dan haka cikin saurin magana ta fara tambayar Tasneem me ya faru, cikin kuka kuwa Tasneem ta zayyana musu duk abinda ya faru.
Wata iriyar qara cikin Hajiya Mama ya yi, da sauri ta yar da mayafin ta da wayar ta, ta yi toilet a guje, ta jima ta na zazzage duk wani ruwan tsoron da bata taba zaton zai shige ta ba a game da tilon d'an na ta da take azabtar wa, Yaron da take ganin sun gama mallakar shi, amma sakin da ya danqara wa Tasneem ya tabbatar musu da cewa Sa'eed ba zai saurara musu ba Sam Sam.
Gaba dayan su sun qarasa wunin ranar cikin tashin hankali, ta yanda ko ruwa ba wanda ya sanya a bakin shi, jira kawai suke Sa'eed ya bayyana ya musu masifa da bala'i, su ji kalaman shi, koma wanne iri ne dan su san mene ne a ran shi game da su,
Tasneem kuwa ta yi kuka har ta ji ba dadi, ta kwanta lamooo a gado, Maryam da ta gama daukan rahoto ta musu sallama ta wuce gida, da niyyar da ta isa ta tura wa qawayen su su ga ya akai wa Tasneem wulaqanci a wannan rana.
Sa'eed kuwa bawan Allah bai samu damar fita daga sashen MAHWISH ba sai bayan isha'i, dan kuwa a ciki ya yi sallolin shi, sannan ya kwanta, ya na ci gaba da tausar zuciyar shi, da ba wa kan shi hakuri, kar ya je garin bayyana fushin shi ya saba wa Allah, Mahaifiya ko arniya ce Mahaifiya ce, Allah zai kama shi da yi mata ihu aka,abinda ya sani kawai shi ne, dole sai ya nuna masu ya san duk abinda suke aikata wa, a game da shi da matar shi.
Hajiya Mama yau gaba daya sallar ta a hargitse ta yi ta, su Zaituna kuwa dama sai an ga dama ake yin sallah, ana nan zaune ana tsammanin zuwan Sa'eed.
Sa'eed kuwa ya na fita motar shi ya fada, dan zuwa sama wa cikin shi abinda zai ci, yunwa ta dame shi, ba zai iya jure wa ba kuma.
Ba tare da ya sha wahala ba kuwa, ya sami abincin da zai ci, ya siyi take away biyu ya nufi gida, ya na zuwa Mai gadi ya bude Masa qofa, ya miqa wa mai gadi daya ya shige ciki.
Ya na tsaka da bude qofar sashen MAHWISH ya ji an fada jikin shi ana kuka, da qarfi ya wurgar da ita gefe, ya ajiye abubuwan da ke hannun shi, ya ja hannun ta, da qarfi, har ta na jin ciwo, ya kai ta sashen Hajiya Mama, ya wurga ta, ihu Hajiya Mama ta sanya ta miqe a matuqar tsorace,
"Sa'eed kana da hankali kuwa, matar taka ka ke wa riqon bara yi? Ni har ka tsor...."
"Hajiya Mama ki dena yin abu kamar baki san na san duk irin qulle qullen da ku ke aikata wa ba, ina da labarin duk wani mugun abun da ku ka qulla a tsakani na da macen da ke ban farin cikin da ku kuka gaza a matsayin ku na jini na, wanda ku ne dole na a rayuwa, me na yi muku ne? Mene ne laifi na dan ina so in samu rayuwar farin ciki kamar kowa? Me ya sa ba za ku so abinda na ke so ba? MAHWISH ce kawai macen da na san in ina tare da ita ina zama d'an Adam mai daraja, dan kuwa ta na min duk abinda mata za ta yi wa mijin ta, 'yar uwa za ta wa qanin ta ko wan ta, abinda uwa za ta wa dan ta na kulawa, tausaya wa da riritawa, daidai misali MAHWISH na min duk wadannan abubuwan, wanda ku ko daya ba ku yi min, Hajiya Mama ke ki ka haife ni, ki ka raine ni, har na zama abinda na zama a rayuwa, na taba tauye maki wani haqqin ki, ko na gaza wajen biyan buqatun ki ko da bana so ne? (da sauri ta kada kai alamar ah ah, sassauta fushin shi ya yi, ya ci gaba da magana cikin sanyin shi) Aunty Zaituna ki sanar da ni wace biyayya ce bana miki, a matsayin uwa na dauke ki,ba yaya ta ba, ke kuma Ihsan ina maki soyayyar da uba ke wa 'yar shi, me ya sa ku ke azabtar da ni? Tasneem ke kin san ya auren mu ya kasance, amma duk da haka na yi iya qoqari na wajen na ga na kyautata maki,na yi biyayya wa iyaye na, sannan na sada zumuncin da ke tsakanin mu, amma duk da haka ba ki zama mace ta gari ba a gare ni, na jure na hakura na zauna da ke a haka, Mahaifiya ta, da mata ta, da' yan uwa na ne ke son ganin baya na, da iyali na, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ni Sa'eed ban yi sa'ar uwa da 'yan uwa ba, ya Allah ka kawo min agaji, tun kafin na sab'a maka"
Kuka yake sosai wanda ya karya zuqatan su sosai, amma saboda Adama Adama ce, bata tashi shiryuwa ba, sai ta miqe ta tsaya gaban shi, tare da tura masa jikin ta, ta ce,
"Iya fushin naka kenan? Shi ne ka sa na wuni cikin fargaba da tsoro? Ai ni na zaci samu za ka yi a gaba ka babbake da fetur ko ka bude gas ka kyasta mana ashana mu qone, ko kuma ka sa kawunan mu gabas kai ta bi kana yanke wa, ashe iya fushin naka nan ya tsaya, mtswww aikin banza, da ka saki Tasneem mu kuma sai ka tsine mana uban mu, na ce sai ka tsine mana, shashasha wanda mace ta wanke ta bawa ya shanye, ashe ma ilimin naka na banza ne, tunda har za ka iya daga muryar ka akai na"
Jan mugun tsaki ta yi, sannan ta nemi waje ta zauna, ganin Sa'eed ya zube guiwowin shi a qasa ya na zubar da hawaye masu mugun zafi, tare da qoqarin bata hakuri, Zaituna ce ta samu karfin guiwar magana cike da nuna isa
"Hajiya Mama rabu da shi, ai yanzu Sa'eed din da ki ka san kin haifa a baya, ba shi ne a gaban ki ba, dan haka kyale shi kawai"
Tuni Hajiya Mama ta gane yaren Zaituna, amma duk da haka bata kyale shi ba, sai da ta sake ruguza masa duk wani lissafin rayuwar shi da ya fara, sai da ta sake jefa shi a cikin qunci da tsananin tashin hakalin da ya sanya shi zubewa a wajen a sume................
Hummmm ma fiful mu je zuwa yanzu aka fara wasan
KAMU SEDANG MEMBACA
MAHWISH
RomansaQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........
