MAHWISH PART 2 PAGE PAGE 16

41 4 1
                                    

"Kallo na ya ci gaba da yi, ya na jiran amsa ta, ni kuma na yi shiru na qi na tanka shi, tunda ya san matsayin Modu a waje na, me ya sa ya ke so ya raba ni da shi?"

'Ke na ke jira, ki zaba ko ni, ko Modu'

'Grema abun nan be kai ace wai ka na furta na zaba ko kai ko Modu ba, amma ina so ka sani in dai ka ce sai na maida Modu to nima zan hada har da kaya na, daga baya an kwashe sauran, Modu tashi mu tafi'

" Ina kama hannun Modu Grema ya miqe tsaye ya sha gaba na, tare da kama hannu na, ya na murmushi da alama murmushin be kai zuci ba, cikin sauri ya ce,"

'To ke wai baki san wasa ba ne? Ta ya ma zan ce ki maida Modu, wasa nake miki, zo nan, Modu jeka dakin can ka yi wasa ka ji'

"Da wannan aka kashe maganar maida Modu, sai dai ya fanshe haushin rashin tafiyar Modu a jiki na, dan kuwa Grema ya azabtar da ni a wannan ranar, ya gurje ni son ran shi, ban hana shi ba, tunda na san dalilin yin hakan, kiran sallar magariba ne ya katse Grema daga ci gaba da abinda yake yi, wanka muka yi, muka yi sallah, ni kuwa na jima a sallah ta dan dai in sama wa kaina lokaci, abinci ya ja ya na ci tare da sanar da ni in yi sauri in idar ya na jira na, kalaman shi sun sa gaba na faduwa, ni yanzu gaba daya tsoro yake bani indai ta wannan bangaren ne, dole na na sallame sallah ta, na ja jiki kamar kazar da kwai ya fashe wa, na zauna zan debi abinci, hannu na ya kama ya ce,"

'Haba Sumayyah ki kalle ni ki ga halin da nake ciki, amma saboda baki tausayin angon ki zaki tsaya wani cin abinci? Dan Allah ki zo mana mu shiga ciki'

'Haba Grema ka bari in ba wa yaron can abinci mana? Tun dazu yake kallon TV, na kuwa tabbata yunwa yake ji, Modu yaro ne mai hankali, ba dan haka ba ai da tuni ya fado mana ya ce ya na jin yunwa ko so ka ke ya shigo ya ga me muke yi?'

'Yi hakuri, dena fushin amaryar yaro, je ki ba wa Modu abinci ki zo, kin ji'

"Murguda baki na yi, na wuce na debi abinci da yawa na tafi dayan dakin, Modu na kwance ya yi bacci, da alama kallo yake kafin baccin ya dauke shi, dan haka na tada shi na fara bashi abinci a baki, nima ina ci, a haka muka qoshi, muka je muka wanke bakin mu, na wanke hannu na, sannan na raka shi ya yi fitsari, ya sha ruwa, na maida shi dakin, na masa addu'a na kwantar da shi a katifa, ina nan zaune ina tunanin komawa dakin, saboda na san abinda xan tarar in na koma, takun Grema na ji ya na dosowa dakin, da sauri na miqe na fita, a hanya mukai karo, tun a hanyar ya fara manne min har muka shiga daki, nan fa ya dasa daga inda ya tsaya, in taqaice maku labari har mukai wata d'aya da aure Grema be dena yi min mugunta ba, a da na zaci duk d'okin amarci ne, se daga baya na fahimci haka yake, Grema ya maida ni kamar wata fata duk ya jeme ni a cikin lokaci qanqani, ko a gidan uwar gidan shi yake baya hana shi biyowa daga kasuwa ya zo waje na, tun ina masa wa'azi ya na saurara har wata rana ya gaji ya taushe ni ya yi abinda zai ya tafi kasuwa abun shi, a haka har aka fara azumin ramadhana,"

" watarana ya biyo gida na dan mu gaisa, muna zaune mu na hira, mu ka ji alamar tsayawar keke napep, ba jima wa mu ka ji ana buga gidan kamar za a balle qofar, kiran suna na kawai ake kamar a tsakiyar tasha, ina qarasa wa soro na gane  mai muryar ashe Grema ya san wace ce shi ya sa ya qi fita, sannan ya ce kar na fita, masifa ce ta zo, ni kuma na ce masa Allah ya mana tsari da masifa, biyo ni ya yi, ya ce na kyale ta ta gama haukan ta ta tafi kar na bude, har zan bude na ji ta na fadin, "

'Ki zo ki bude mcijiya, ki zo ki bude mu daku da ni da ke, na gaji da wannan iskancin naku'

'Akan me zamu daku kamar wasu' yan iska? '

' Kin mallake min miji, kin maida shi mace, in ya koma waje na bai da aiki se bacci, amma nan wajen ki an ce har kwana ku ke ku hantse ku na abu daya'

"Jin haka na san wataqila ko maqota ko kuma shi uban gayyar wani na kai mata gulma, dan haka ni kuwa na kada baki na ce mata"

'Banda abinki ai dole a kwana ana abu daya, taya za a hada zuma da dusa wajen dad'i?'

"Wannan maganar da na fad'a ta matuqar hasala ta, dan haka se ta fara jefo dangur ( dutse) ,nima haushi ya hasalani, na fara mata masifa da yaren su na Kanuri, ita ma ta na mayar min, katanga ta kama za ta hauro, sai aka riqe ta,' yan uwan ta suka je a adaidaita sahu suka kama ta da qarfi aka sa ta ciki, sai ta qi koma wa gidan Grema, tai yaji, a ranar aka tattaro min yaran ta aka kawo min, da me shekara goma, da me shekara shida, dika mata, yaran akwai surutu, iyayi da manyance, amma baya hana su da sun kwanta su min fitsarin kwance, a haka washe gari zan gyara masu dakin in saka turaren wuta da humrah dan ya dauke xarni da warin,dan na san akwai lalura, ta yu ba da son ransu bane suma,a kwana a tashi sai na fara musu shimfida a qasa saboda sun fara rub'ar da katifar, hakan da nake sai ya hasala shi, ya hau min fada, wai akan me zan dinga barin yaran shi a qasa Modu a gado, na masa bayani dalla dalla, amma ya qi gane wa, ai kuwa raina ya baci na hau masifa ni ma, ya na yi ina yi, a haka muka bar dakin kowa rai bace"

"Bayan kwana biyu kuma ya dawo daga kasuwa ya hau kiran yaran shi, ya na kallo, ya na jujjuya su, yana magana da yaren su na kanuri, ko da na fito se na ji ya na fadin

'Kalli yanda ku ka rame, gaskiya ba zai yu ba, yara da gidan su a bari su na ramewa haka,'

"Kallon shi na yi na ce,"

'Me ka ke nufi?"

' Ai dama na san wahala ki ke ba wa yaran nan, diba ki gani duk sun yi baqi sun sauya, rannan ma na ji ana cewa ruwa wannan da marfin buta kk basu tsabar mugunta, a gaskiya Sumayya ba zan yarda da wannan zaluncin ba'

"Kallon shi na yi cikin takaici, wato ni ce ma azzalunar?"

'Dan Allah Grema ka dau yaran nan ka kai su inda ba za a zalunce su ba, kar na kashe maka su, ko ka je ka yo bikon uwar su, ko ka kai su dik inda ka so'

' Eh zan kwashe sun, kai ku dakko kayan ku ku zo nan'

" Ba bata lokaci kuwa suka shirya suka dau kayan su sai gidan Hajiya, ta na ganin su ta yo min waya, ta na tambayar dalilin da ya sa na ce ba zan riqe yara ba"

'Eh Hajiya ki yi hakuri amma ni na  ce ba zan riqe yaran ba, saboda ya ce ina zaluntar su, duk kalar abinda nake musu baya gani, komai a zan cutar masa da yara yake a wajen shi, to Hajiya in ba yarda a tsakanin mu, se ya kai su in da hankalin shi zai kwanta,tunda ya dawo da su nan shikenan, sun ji dadin wasa da kakar su'

'Ah ah Sumayyah ba haka xa ai ba, ki yi hakuri ya yi kuskure ba zai sake ba'

"Ni kuma fafir na qi, dan haka ta sa shi a gaba tai ta masa fada, bayan an kwana biyu uwar su ta hakura da yajin ta koma ta kwashi yaran ta daga wajen mahaifiyar shi,"

"Bayan an kwana biyu Grema ya fito min da wani sabon hali, wanda ya yi matuqar ban mamaki, in baya gida na, ya na gidan abokiyar zama na, cikin dare sai in dinga jin ana tafiya dif dif dif kamar an hauro ana leqe na, ni kuma saboda tsoro se na qi motsa wa, a haka har na dinga daukan Modu ya na taya ni kwana, sannan dan na samu na kula da shi kar abinda nake jin ya na shigowa ya illa ta shi, watarana ina zaune ina wankin kayan shi, ina tunanin yanda xan guga tunda ba wuta, kasancewar tunda ya auren ni ke masa wanki da guga, a da Grema ba qaramin qazami bane amma zuwa na gidan shi ya ke saka kaya wankakku har da guga, zuwa na ne Grema ya fara saka turare, mahaifiyar shi dake mai tsafta ce se ta fara min godiya, ta san ni na ke sa shi yin hakan, dawowa na yi daga duniyar tunani sakamakon ji da na yi Modu ya taba ni, kallon shi na yi, na ji ya na cewa,"

'Umma na, kin san me Baba yake min?'

'Ah ah Modu?'

" Cikin tsoro da fargaba nake jiran jin amsar yaron, bude baki ya yi ya ce, "......

*Na sani kuna hakuri ku qara akan na da, Allah ya sanya mu cikin bayin shi masu yawan hakuri, ba laifi na bane, laifin yadeee ne😂*

MAHWISHDove le storie prendono vita. Scoprilo ora