Zaune ya gan ta a bakin gado ta na gyara saman mirror din ta, mamakin shi ne ya qaru da ta taso ta na tambayar shi ko ya samu ya gama cin abincin?
"Mahwish.."
Dakatar da shi ta yi da sauri cikin shanye baqin cikin da ke taso mata ta ce.
"My love kar ka damu kan ka akan abinda ni ba ni da ikon canja shi, Allah ya bawa maza damar su auri mata sama da biyu, to ban ga dalilin da zai sa in hana ka ba, tabbas maganar ta daki zuciya ta, kuma na ji matsanancin kishi lokaci daya ya lullube ni, amma ba zan taba jayayya da umarnin Allah ba, idan na yi na zama daka cikin fajirai masu take dokokin Allah, ina mana fatan wannan auren ya zame mana alkhairi in ma ana nufin mu da wani sharrin ya juye ya zame mana alkhairi, ka qarasa cin abincin? Dan ni ban qoshi ba"
Gaba daya jikin shi ya yi sanyi, yarinyar ta bashi mamaki, a zaton shi zata masa rashin mutunci duba da abubuwan da suka faru a baya, gashi ita ba mace bace da ta iya boye abinda ke ran ta, komai take ji za ta fada, ya tabbata abinda ta ce shi ne a ran ta, me zai mata ya wanke mata quncin da ke ran ta?
Shiru kawai ya yi ya kwanta, ya na jin wani irin qunci a ran shi, ta ya zai iya rayuwa da wata mace bayan Mahwish? Tasneem ma dan ta zame masa qaddara ne, amma da daga randa ya auri Mahwish zai sake ta.
Haka suka yini ba wani walwala a tare da su, ko da Mahwish sukai waya da Zulaihah da su Hajiya duk sun tambaye ta ko akwai wata damuwa ne? Sai tace musu gajiya ce kawai, amma ba wata damuwa.
Hajiya ta san akwai wata a qasa, amma dai bata matsanta ba, Abban su na fita ta sake kiran Mahwish ta sake tambayar ta damuwar ta, kuka Mahwish ta sanya mai matuqar kuna a zuciya, sannan ta labarta wa Hajiyan ta komai,
"Allah ya miki albarka, ya amsa addu'o'in da ki ka yi, tabbas kin kyauta da baki daga wa mijin ki hankali ba, tunda shi ma ba da son ran shi bane, inshaa Allahu wannan amarya alkhairi za ta zame maki,ke dai ki ci gaba da addu'a mu ma za mu taya ki, sannan ki ta qoqarin danne baqin cikin da ke ran ki, Allah ya muku albarka ya zaunar da ku lafiya a gidajen ku"
"Ameen Hajiyar mu na gode"
Wani kwarin guiwa Mahwish tai ta ji na samun ta a hankali, sannan ta riqe fadin Hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem.
*******************************
Hajiya Mama da tawagar ta sun tasamma shirin qarin auren Sa'eed da gaske ba da wasa ba, qawayen ta na kusa da na nesa duk sun hallara, ana ta shirye shiryen biki, Mahwish kuwa ta na gefe ta zuba musu ido, ganin haka Sa'eed ya shirya yanda zai ya kawo murmushi a fuskar tauraruwar tashi,Sa'eed ya sa an kwashe kayan dakin ta, yana so ya yi mata sababbi, Hajiya Mama ta tada bala'i da masifa akan hakan, ta ce sai dai in ya hada har amarya ya mata sababbi, shi kuma ya ce ba haqqin shi bane haqqin iyayen ta ne tunda haka ake yi a qasar hausa yanzu, dan haka shi ma haka zai yi, wannan karon dole su Hajiya Mama suka hakura suka sakar masa, amma duk sun tattare kayan Mahwish da aka fitar wasu sun riqe wasu sun bayar,hidimar biki kuwa kowa na nashi ne, dan kuwa ba me saka Mahwish a cikin hidimar bangaren Hajiya Mama, a cewar su yanda take baqin ciki mijin ta zai qara aure, za ta iya rusa abun.
Wulaqanci, habaici, harara, zagi kuwa ta sha shi wajen su Hajiya Mama, amma a koda yaushe, wani irin murmushi ta ke musu, wanda suka kasa gane ma'anar shi, hakan kuwa na matuqar qona ran su, ita kadai ta san ya take ji a ran ta, bata nuna musu ba, su kuma ba haka suka so ba, a so samun su, su gan ta a tagayyare, a wulaqance, amma Sa'eed ya tsaya tsayin daka dan ganin ya kyautata mata, kama daga sauya mata kayan gidan ta kafff da ya sa ayi, hatta da cokali sabo ya sanya mata, cikin kwanaki uku aka kammala komai, ma'aikatan na tafiya ya dauki Mahwish ya tafi da ita super market din shi, ya dinga mata siyayya, duk abin nan da ake a fuska ba wani bacin rai amma zuciyar ta ta quntata da abinda ke tunkaro rayuwar su.
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........