Hajiya Mama da Zaituna da Ihsan na zaune, su na tattaunawa akan yanda za su tinkari kotu nan da kwana uku, suka ji sallamar Tasneem, ita da sabbin qawayen ta 'yan gayu masu ji da kyau da aji,sannan su suke bata duk wata shawarar da take aiwatar wa a yanzu, cike da fara'a Hajiya Mama ta tarbe su, ita a dole qawayen 'yar ta sun zo.
Su na gama zama, Tasneem ta ce,"Hajiya mama, na zo maku da babban albishir, wanda na tabbata za ku yi farin ciki da hakan,"
Bakin Hajiya Mama a washe ta ce,
"Har ma na ji na fara shiga cikin farin cikin tun kan na san mene ne,"
Jakar ta ta bud'e ta fito da makullai, sannan ta miqa wa Hajiya Mama, ta ce,
"Hajiya Mamana, wannan makullin gida na ne da Yah Sa'eed ya bani kyautar shi, kuma ya zuba min kayan yin gyaran gashi da hannu da qafa a shagon gidan, ma'ana dai ya na so mu koma can, in ya zo gida, a ganin shi yanzu tunda gidan ya cika ba zai samu sakewa da iyalan shi ba"
Wani irin kallo Hajiya Mama da yaran ta suke bin Tasneem da shi, kallo ne da zai iya kashe mutum in da kallon na kisa,mamaki irin na butulcin Tasneem ya baibaye su, duk fad'i tashin da ake kusan duk akan ta ne, da kuma suma samun nasu arzikin shi ne ta zagaye ta kwashi na ta rabon sannan ta zo ta na fada masu maganar da in wuqa za a sa wa Sa'eed a wuya sarai sun san ba zai fada ba.
Tabbas Tasneem ta cika butulu, kallon qawayen ta tayi, suka yi wani irin abu da ido, na 'dama mun fada maki ai ba son ki suke ba', cike da yarda da zugar da suka jima su na mata ta kad'a kai, ta karb'i makullin gidan ta, ta ce wa Hajiya Mama,
"Hajiya Mama yaushe za mu je ki ga gidan? Za mu je yau ne ko sai gobe in an gama saka komai ? Dan kuwa kaya sun iso, gobe za a saka komai, na dauki ma'aikata domin yin hakan"
Hajiya Mama ta wuce duniyar lissafin har million nawa Tasneem kenan ta tatsa wajen dan ta ta yi wannan facakar da kud'in? Ashe yanzu sun raini 'yar kunama ne basu sani ba? Ta girma ta na d'allin su? Lallai rayuwa abar tsoro ce.
"Ba sai na je ba Tasneem, Allah ya sanya albarka, kin nuna min kuskure na a rayuwa, na jan d'an kunama na raina, tabbas watarana ni zai d'alla, na gode wa Allah da ya sa harbin ki bai kashe ni ba, Allah ya baki sa'a Tasneem, na gode da irin sakayyar da ki ka min a rayuwa, ke tawa ce har abada, ina son ki, irin son da ban wa yara na ba, kin dafa tudu biyu ne Tasneem, shi ya sa zan kyale ki, soyayyar da nake wa 'yar uwa ta da soyayyar da ki ka taso ina maki tun ki na qarama,har yanzu ina hango ki kamar 'yar qaramar yarinyar da na raina, ki je ba komai, ba dai wad'annan ki ka zab'a a matsayin masoya ba? Allah ya taimaka"
Hajiya Mama kuka take mai tsananin kuna, tabbas ta na son Tasneem so mai tsananin da ba ta yi wa yaran ta kalar shi ba, Banda haka da ta gane kuren ta a wajen ta, amma a hakan ma bata tsira ba, a juri zuwa rafi.
Zaituna da Ihsan ne suka dinga zagin Tasneem, su na kiran ta da sunaye na masu cin amana kala kala.
Cike da rashin kunya ta gaggaya musu magana, tare da nuna musu ita yanzu ta fi qarfin su, in asiri ne sai dai ta nuna masu yanda ake yi yanzu, dan kuwa har qasashen kusa damu zuwa take yanzu akan sihiri, Zaituna ta sha jinin jikin ta da yarinyar, ta kuma yarda da abubuwan da ta fada, duba da yanda ta fi su wayon ta yagi rabon ta ta kafa kan ta da kan ta.
Su na ji suna gani Tasneem ta miqe ta yi wucewar ta, su na fita Zaituna ta kalli Hajiya Mama da ke ta sharar hawaye ta ce,
"Ba kuka za ki tsaya yi ba, dole ne mu dau mataki akan hakan, kuma na san abinda za mu yi duk mu sanya su cikin kunci, da damuwa."
"Me ki ke nufin za a yi Aunty Z? A gaban ki yarinyar nan ta gama iskanci ta tafi, ita kuma waccan ta shanye shi, sai yanda ta yi da shi, me za a yi musu da zai quntata musu, kuma mu karbe d'an uwan mu daga hannun su?"

KAMU SEDANG MEMBACA
MAHWISH
RomansaQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........