MAHWISH PAGE 39

28 3 0
                                    


"Me ki ka ce?"

"Na ce ku na nan dai lafiya ko? Kwana biyu shiru, gashi jiya na yi mafarkin Mahwish ta yi b'ari, in ce dai lafiya ku ke?"

"Lafiya qalou muke,"

"Lafiya qalau ka ce? Ba abinda ya faru?"

"To me zai faru Aunty Zaituna? Lafiyar mu qalou, gamu a gida ma"

"Ok to ka gaishe ta, sai an jima"

"Za ta ji"

Mamaki ya kasa barin zuciyar Sa'eed ta sake, me hakan ke nufi? Ba tare da ya samu amsar da yake so ba, ya ji nurse na sanar da shi mummunan labarin b'arin da Mahwish ta yi, ga shi garin wanke ciki sun qara ta, ta na kuka ta na komai sabo da azaba, aka gama wankewa, suka ce za su d'in ke ta qi amincewa saboda azabar da take sha.

Wahala iya wahala Mahwish ta sha a wannan b'ari da tai, da fari su na ganin wajen zai had'e ba wani qari bane mai yawa, tunda ba na haihuwa bane, dan haka suka bar ta, ta huta, daga baya Sa'eed ya maida ta gida.

Sanda labarin b'arin ta ya riski su Hajiyan Mahwis, Hajiyan addu'a ta yi, tare da gode wa Allah akan ni'imar shi a gare su,ta kwantar wa da 'yar ta hankali sosai da shi kan shi Sa'eed d'in, dan kuwa abun ya shige shi sosai, ya sa rai matuqa akan abinda za a haifa.

Dan tun cikin na wata hud'u suka shirya ya dauke ta ya shiga da ita super market din shi, bangaren da ake saida kayan yara, ma'aitakan wajen na ta kallon yanda uban gidan su ke zuba wa matar shi soyayya, kamar wannan ce haihuwar fari (tabbas na tuna wannan ranar😭)

Mahwish ta shiga tsananin damuwa da qunci  saboda ta saba da cikin nan, sannan ta sanya rai akan shi, sai gashi ya zube, bayan zaman shi a jikin ta na wata da watanni.

Ba yanda Sa'eed ya iya, dole ya kira gidan Hajiya Mama ya sanar da b'arin da Mahwish ta yi, ba wanda ya wani nuna damuwar shi akan hakan, illa addu'a da suka yi sama sama, na Allah kiyaye gaba, daga qarshe ma Hajiya Mama ta so ta jefa wa Sa'eed zargin anya ba ita ce ta ke zubar da cikin ba, nan take ya dakatar da ita,ya bata labarin abinda ya faru, bakin ta bai mutu ba, sai da tai ta kalace kalacen maganganu.

Sati d'aya da b'arin Mahwish, ta na zaune ita kad'ai kasancewar yanzu tunda suka koma can ya na jima wa bai koma gidan ba, aiki ya na masa yawa.

Wayar ta ce a hannun ta, su na chatting da 'yan uwa da abokan arziki, sai ta ga message na shiga kala kala, wajen guda uku.

Saqo ne daga wajen Zaituna, a kullum maganar ta ba ya wuce Mahwish ta mallake Sa'eed duk da qanqantar shekarun ta, da kuma yawan shekarun Sa'eed d'in, wannan saqon ma kamar ko yaushe maganar akan Mahwish ta mallake Sa'eed ne ta hana shi zuwa ganin su, kuma ba ya basu kulawa kamar da, waya ma ya dena yi akai akai, bai fi ya kira Hajiya Mama ba, ita Zaituna ba ya ma kiran ta, balle kuma Ihsan.

Alwashi Zaituna ta ci a saqon nata na sai ta raba tsakanin Sa'eed da Mahwish, nan take Mahwish kuwa ta mayar mata da nata martanin masu zafin da ya fi na Zaituna.

Wannan shi ne dalilin sabuwar qiyayya da kuma muguntar da ta sake qulluwa tsakanin Mahwish da Zaituna.

A daren Mahwish ta nuna wa Sa'eed abin da ya faru tsakanin su, sai ya nuna bai ji dad'i ba, ta gaya wa yayar shi magana, bayan gaba take da shi,balle ita qarama,duk da ya san cewar ana cutar Mahwish.

Haka suka kwana rai a b'ace, Sa'eed sai juyi yake, ya kasa bacci, gashi ya b'ata ran gimbiyar tashi, ya jima sosai idon shi biyu, kafin ya samu bacci ya dauke shi.

Da safe kuwa tashi suka yi kamar ba abinda ya faru, su na zaune su na karya wa, Sa'eed ya fara jin ya na tsananin son zuwa gida, ya yi weekend, zuciyar shi da ruhin shi gaba d'aya sun yi gida, ba ya jin zai iya qara awa d'aya a gidan nan, ba gaban Tasneem ba, da Hajiya Mama.

MAHWISHWhere stories live. Discover now