Assalamu alaikum my beautiful readers, Alhamdulillahi ina godiya ga Allah da ya bani iko zan ci gaba da rubuta maku ci gaban labarin MAHWISH, duk da dai wasun ku sun san ina da babban uziri da ya sa wannan novel ya jima ban kammala shi ba, amma ga wadanda basu sani ba ku yi hakurin jira da jinkiri da tsaiko da ake ta samu a wannan rubutu nawa, in dai kun saba karanta labarai na, kun san ba hali na bane tsawaita novel ko jimawa ban gama shi ba. Amma inshaa Allahu zan qoqarin ganin na ci gaba, a duk sanda na samu damar yin hakan, da fatan za ku ci gaba da min uziri da hakuri,na gode. Allah ya bani ikon gamawa lafiya, Allah kuma ya bani ikon rubuta alkhairi ya kiyaye ni daga rubuta sharri ameen.
Mutane na yawan tambaya ta wai labarin nan na gaske ne? Kwarai na gaske ne, tun daga page 1 a part 1 in baku manta ba, na sanar da ku cewar labarin gaskiya ne, so a yau zan sake tunatar da ku labarin Mahwish na gaskiya ne, sannan kar ku manta gaba daya labarai na da na rubuta kusan guda ashirin, da dama jigon su labarin gaskiya ne, sai dai kun san dole za a rufe wani abu, a sanya wani abun saboda wasu abubuwa suna buqatar sirri a rayuwa, ko a qara wani abun dan labari ya qara fadakarwa ko ilmantarwa, ko nishadantarwa. Ku biyo Haermeen Haermmaerh dan jin ci gaban labarin MAHWISH..
PAGE 1
Kallon da mutanen da ke tsakar gidan ke bin ta da shi ne ya sanya baiwar Allah'n qarasa shiga ciki, cike da rashin kunya, ta ke takawa, har ta isa gaban Mahwish, wadda ta saki baki da hanci ta na kallon matar, mutanen wajen kuwa sai rarraba idanu suke tsakanin Mahwish da baiwar Allah'n nan, ba dan komai ba sai dan tsananin kamanni da suke da Mahwish, duhun fata kawai Mahwish za ta nuna mata, duba da cewa ita bata shafe shafen mai ko amfani da wani sabulu da zai sanya ta fari, ta fi ganewa amfani da natural abubuwan mu na gida, dan gyara skin din ta.
Miqewa Mahwish ta yi, da sauran mutanen da ke wajen, aka hau yi wa matar maraba, cikin fara'a Mahwish ta miqa hannu dan rungumar ta, cike da rashin mutunci matar ta daga wa Mahwish hannu,
"Dakata macijiya, wadda bata ramin kan ta, ban zo bikin nan dan ina so ba, na zo ne dan an tursasa ni, sannan in miki gargadi, ki rabu da kurwar miji na da ki ka lashe, na gaji, na gaji ba zan iya ba, ba zan iya zama da Yah Saleem ba, matsawar ki na raye, ki na numfashi ba zai taba son wata mace a duniya ba bayan ke, Mahwish me ki ka yi masa ne? Me na rasa a matsayi na na mace? Me ki ke da shi da ban da shi? Akan in faranta wa Yah Saleem miji na, har bleaching nake yi, in qara gashi, in saka farce duk wani abu da zai qara min kyau, in ga na fiki a idon shi, na yi, da wanda ya halatta, da wanda Allah ya hana, amma har yanzu, bashi da magana sai taki, bashi da tunani sai naki, a yanzu ma shi ya aiko ni, in zo biki, in tabbatar mun yi hoto ni da ke, ba zai iya jira ba sai dinner ya gan ki, can u imagine my own husband sending me to take a picture with another woman? "
Ta jima da fara kuka, amma ba zata iya ci gaba da magana ba saboda ya ci qarfin ta da yawa, da alama Badi'a na cikin tashin hankali, wace ce ba zata shiga tashin hankali ba in mijin ta na hali irin na Saleem?
Da sauri Mahwish ta qarasa rungume ta, Badi'a kuwa ture ta ta fara yi, amma Mahwish bata bata dama ba, qarshe dakin su ta ja ta, ta ba wa kowa hakuri a bar su su biyu, hatta da Zulaihah ta so zama, su lallashe ta tare, Mahwish ta ce ta jira a waje.
Mahwish bata hana Badi'a koka baqin cikin ta ba, sai da ta yi kuka ta qoshi sannan ta ce,
"Yah Mahwish dan Allah ki gafarce ni, na rasa yanda zan yi in jawo hankalin Yah Saleem, na yi hakuri iya tsahon shekarun nan, na yi duk wani abu da kk san mace za ta yi dan burge mijin ta, kowa a dangi zato yake Yah Saleem ya manta ki,ya ci gaba da rayuwar shi normal, sam ba haka abun yake ba, ni ke rufa masa asiri, kar Abban mu ya yi masa fada, Goggo tai fushi da shi, duk wani zane naki da ya yi ya na nan ya tara su a d'aki d'aya, zai iya shiga ya kulle ya rufe kan sa, anan zai sallah, anan zai ci abinci da komai, ya dauka a wayar shi, in bacci zai sai ya gama kallon hotunan sannan ya yi bacci, in kwanciyar aure muke watarana sai ki ji ya na shi miki albarka, ki na tunanin hankali na zai taba kwanciya a haka? Komai da ki ka sani ina qoqarin yi, amma sam bana burge shi, da fari ni shaida ce ya yi qoqarin manta ki, amma abun ya fi qarfin shi shima, lokuta da dama ya kan zauna ya yi kuka, ya yi kuka, ya ce shi ya cuci kan shi, yanzu da tuni kema ki na nan ki na son shi, wataqila da bai ji zafin rabuwa da ke da ya yi ba, wataqila da ki na nan ki na qoqarin koma wa gare shi, da sauran surutai marasa kan gado, ya zama kamar wani tababbe, a ido za ki gan shi fess amma da kun yi zurfi a hira zai fara sakin layi, na yi qoqarin mu zo gida in sanar, sai na ji nauyin hakan, sai in zo in ce me? Na kasa jan hankalin miji na ya so ni? Ko in ce miji na ya haukace saboda son yayata?

YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........