Tun da asuba da Sa'eed ya tashi ya yi wanka ya fita sallah bai sake koma wa gidan ba, ya na masallaci, ya na ibada, har gari ya yi haske, daren jiya ke ta masa gizo, abubuwa da dama na masa yawo a jiki da zuciyar shi, ga kuma wani irin tsoro da ya ke ji, kar ya sake jiki da Sumayyah ta zama kamar Tasneem,ko ma ta fita mugun hali, kai inaa ba zai taba wannan gangancin ba, mace ce dai Allah ya bashi, ta nuna wa sa'a cikin ruwan sanyi, amma ba zai yi gangancin sanya soyayyar ta a rai ba, har sai ya san wace ce ita, Mahwish din shi ta ishe shi a yanzu.
A iya sanin Sa'eed ya san ba yanda za a yi Hajiya Mama ta zaba masa mace kamar Sumayyah ba tare da wata manufa a bayan hakan ba, domin tunda Allah ya azurta shi ya san bata tab'a masa abu, sai in ta na da wata manufa akai.
Hannayen shi ya daga sama tare da rintse idanun shi, ya na jin wani irin baqon lamari a tattare da shi wanda shi kan shi ba zai iya cewa ga abinda yake ji ba.
"Ya Allah ka sauya dikkan wani mummunan abu a rayuwar mu ni da iyali na, ya zama alkhairi, ya Allah ka ninninka alkhairi a rayuwar mu, ka yi wa rayuwar mu albarka, Allah dik abinda zai dame mu ka kawar da shi, Allah ka sanya mu kasance alkhairi a rayuwar duk wanda muke tare da shi, ya Allah ka cire min tsoron da ke zuciya ta, ka mayen gurbin shi da aminci"
Ya yi wasu addu'o'in masu yawa kafin ya tashi ya tafi gida.
Sashen Mahwish ya fara zuwa ya tarar da ita da qannen ta su na karya wa, ana hira, gaba daya ta maida hankalin ta wajen hira, lallai zuwan su ba qaramin kewa ya debe mata ba, zuwan su ya taimake shi ya kuma taimake ta, cikin fara'a ya qarasa shiga, ta na ganin shi ta ji wani abu mai zafi ya daki zuciyar ta, da ganin annurin da ke fuskar shi jiya bai kwanan baqin ciki ba, be kwanan kewar ta ba, da sauri ta fara kiran sunan Allah, sannan ta shimfida murmushi a fuskar ta, tare da miqewa zuwa gaban shi,
"Barka da safiya ango, da fatan kun tashi lafiya kai da amarya? Allah ya dawwamar da farin cikin nan da na gani a fuskar ka ameen"
Murmushi kawai ya yi, dan kuwa kunyar ta ba zata bari ya yi magana ba, ya kasa hada ido da ita, sai kewaye wa hada ido da ita yake, Ludhfi ne ya tafi da gudu wajen shi, ai kuwa ya daga shi sama ya na masa wasa, yaron na ta bashi labari, yana amsa masa,
"Baby bari mu je mu gaishe da su Hajiya Mama,"
"Ok sai kun dawo, da kun dawo dan Allah ka kawo shi nan, ku je ku karya, kar ka kai shi ya dami amarya ta na buqatar hutu"
Kasa amsa mata ya yi, shi kwata kwata baya so yayi zancen amaryar da Mahwish, sai ya dinga jin nauyin ta.
Abincin da Mahwish bata iya qarasa ci ba kenan, tabbas mijin ta ya kwana da wata jiya, dama haka kishi yake? Dama zafi ne da shi kamar zafin wuta? Anya zafin shi bai wuce wuta ba ma? Tuna wa ta yi da addu'a nan da nan ta hau addu'a ta na tasbihi ga Allah, a hankali ta fara jin sauqi a zuciyar ta, kwanciyar hankali na xuwar mata.
Ludhfi kuwa su na fitowa daga sashen Hajiya Mama da baban na shi, ya ce zai koma wajen Maman shi, Sa'eed kuma ya so ya kai shi wajen Sumayyah ta ga d'an shi, yaron nan kamar ya san Mahwish ta hana a kai shi a ranar fir yaqi, sai ma ya fara kuka shi xa shi Maman shi, haka Sa'eed ya maida shi, ya gode wa Allah da bai tarar da Mahwish a parlour ba, ya ajiye shi ya tafi wajen Sumayya amarya.
Ta sha gayun ta da riga da skirt sun amshi jikin ta sosai, ta yafa mayafi kalar kayan ta, ta jera abincin da Mahwish ta aika mata, ga qamshin turaren wuta da ta kunna, ga qamshin abincin da ta jera.
Sa'eed na shiga, ta miqe tsaye, ta masa sannu da zuwa kan ta a qasa, saboda kunyar shi take ji, shi din ma kau da kai ya yi, dan kuwa shi ma kunyar ta yake ji, haka kawai daga kai masa mace, ko taba ganin ta be ba, ya hau kwana da ita, lallai maganar Mahwish gaskiya ne, namiji baya wuce tayin mace.
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........