*Assalamu alaikum ma fiful, ina mai sake baku hakuri, saboda ji na shiru da ku ke yi kwana biyun nan, abubuwan ne sai a hankali, ba lokaci kamar da, a kullum dai hakuri ne zan ci gaba da baku har Allah ya sa mu gama, ina fatan ba za ku gaji ba, labarin MAHWISH ba zai fita a ran ku ba saboda jimawar da nake, ana uhibbukum katheeran ma fiful Allah ya qara mana son juna domin shi❤️*
Mahwish bata ga kowa ba, amma ta ji alamar kamar an shiga, tsoro ne ya shige ga, tsigar jikin ta ta miqe, addu'a ta fara yi, wadda ita kan ta bata san ta mene ne ba, tashi ta yi daga wajen gaba d'aya ta koma d'aki ta kwanta, ta rufu, a zuciyar ta ta na addu'ar Allah ya sa ba wani tashin hankalin bane Kuma zai biyo baya, dan kuwa har ta fara murmure wa qibar ta mai ban sha'awa ta fara dawowa.
Ji ta yi komai ya lafa, duk wani tsoro da take ji ya kau, tashi ta yi, dan ta fita zuwa parlour, amma me? Gani ta yi wajen ya koma mata duhu dulum, ba ta ganin komai, a tunanin ta ko wuta aka d'auke, dan haka ta koma ta kwanta, dan bata san ina za ta fara neman abinda za ta haska waje da shi ba, tunda ba waya a hannun ta, kuma tunda ta zo ba a tab'a d'auke musu wuta ba, balle ta ce ko su na da wani abun haske.
Ta na nan kwance har bacci ya dauke ta, abu kamar wasa cikin bacci ta ji Muryar Sa'eed ya na tashin ta, ta yi sallah, dan da alama ta jima ta na baccin, ba ya jin ma ko azahar ta yi.
Ta na sake bud'e idon ta sai ta ga duhu, cikin Muryar bacci da shagwab'a ta ce,
"Baby ka kunna mana fitilar wayar ka mana, duhu, tun d'azu aka d'auke wuta, shi ya sa ma.na kwanta, har bacci ya d'auke ni,"
Cikin tsananin mamaki Sa'eed ya ce,
"Duhu kuma babe? Wane irin duhu, gida duk haske, ga wuta nan, tin da Allah ya azurta ni ko a gida Nigeria, ko a qasashen waje ban taba qin biyan kud'in wuta ba, balle a yanke min,"
A razane Mahwish ta sauka daga gadon, ji ka ke quum ta bige goshi qara ta sanya mai had'e da kuka, Sa'eed ma ya kid'ime, me ya ke gani ne?
"Yah Sa'eed na shiga uku, ba na gani, me ke faruwa ne? Ba na ganin ka, ba na ganin komai, ba na ganin haske, ido na duhu,"
A rud'e ta ke maganar, Sa'eed ma ya rikice amma sai ya ke qoqarin kwantar mata da hankali.
"Yah Sa'eed ka bari kawai, na san so ka ke na kwantar da hankali na, amma hankali na ba zai tab'a kwanciya ba har sai na ga fuskar ka, Yah Sa'eed, zan iya jure komai, ba zan iya jure rashin ganin ka ba, ina zan saka kai na ni Mahwish, yanzu kuma ta nan aka biyo? Makanta? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allah ka isar min, Allah ka shiga lamari na kar ka bar Ni da kai na, ba zan iya ba, Allah ka sani na gaji, ya zan yi in makantar nan ta tabbata a kai na?"
A tare suka sanya kuka ita da Sa'eed, su ka rungume junan su, kuka suke ba mai lallashi, Sa'eed fada yake ya na sake wa,
"Mahwish ki yafe min, ki yafe min, ban san me ya kawo maki wannan rashin ganin ba, domin zato ba shi da kyau, amma na san duk a sanadiyyar aure na ne ki ka samu makanta, Mahwish i am so sorry, you have to go through all this because of me, I am sorry, I am so sorry baby, ni kai na qarfi na ya qare, basira ta da duk wata hikima ta ta qare ina neman shawara a wajen ki, ya zan yi? Ya zan yi ki samu lafiya?"
Cikin kuka ta lalubi fuskar shi ta riqe a hannun ta, sannan ta ce,
"Yah Sa'eed mu hakura da junan mu kawai, in muka yi haka shi ne zaman lafiyan mu"
Da qarfi ya yarfe hannayen ta, sannan ya ce,
"Nooo ba zai yu maqiyan mu su yi nasara akan raba mu ba, in su na taqama da sihiri, mu na taqama da Allah wanda ya basu nasara qalilan dan ya jaraba imanin su, na tabbata ba a banza yake jarabtar mu ba, hakurin mu kawai shi ne zai tabbatar da mu mu ci gaba da zama tare da Allah, rashin hakuri na nesanta bawa da Allah, mu nemi wata mafitar, amma ba wannan ba"
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........