*MAHWISH PART 2*
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 14:
Mamakin Mahwish da Sa'eed ya qaru ne a daidai lokacin da suka ga Hajiya Mama na qoqarin durqusa wa a gaban MAHWISH, cike da nadama, ta ce,
"Mashawi ba zan ga laifin ki ba idan ki ka ce baki yafe min ba ni da 'ya' ya na, amma duk da haka ba za mu fasa roqon ki gafara ba akan abubuwa munana da muka yi miki a rayuwa, ban taba sanin zafi da quncin da ki ka shiga ba a lokacin da na raba ki da Sa'eed sai da Ihsan ta kamu da son Munkaila, na maki mugayen abubuwa kala kala wanda in na tuna su ina jin zuciya ta na wani irin zafi, kunyar ki da kunyar Allah ta gama mamaye ni, Mashawi ki wa Allah ki yafe mana"
Wani irin kuka ne mai qarfi me maqaqi a wuya ya kwace wa Mahwish nan da nan ta fara tuna wahalhalun da suka sanya ta a ciki, musamman rayuwar ta ta Makka, ita ce shaye shaye, bin mata 'yan uwan ta, zubar jini, makanta, ciwon ciki, ciwon kai me tsanani, ita ce tashin jinnu a jikin ta, sihiri kala kala duk dan a hana ta zaman aure da mijin ta, wulaqanci da masifar kishiya, nan take shaidan ya dinga girmama laifin su Hajiya Mama fiye da yanda ya kamata a zuciyar Mahwish, ta kasa dena kukan baqin cikin da ke ran ta,nan take ta tuna da yanda suka azabtar da Ludhfi kawai dan ya na d'an ta, har qona shi suka yi, me ya musu? Yaro ne fa, jikan ta ne, d'an su ne, bata jin za ta tab'a yafe musu, a guje ta rufe qofar ta ta koma ciki, bata tsaya ko ina ba sai saman gadon ta, kuka ta dinga yi, kamar an aiko mata da rasuwa, Hajiya Mama murmushin baqin ciki ta yi, ta san za a yi haka, ba kowanne mutum bane za a yi wa abubuwan da suka yi wa Mahwish ya hakura ba, ta yi alqawarin za ta yi duk wani abinda zai sanyaya zuciyar Mahwish ta yafe mata laifin da ta mata, ta yi alqawarin za ta sauya rayuwar ta daga wannan daren, ta tabbatar dama duk zaman nan da ake Mahwish na zaune da su ne kawai, amma ba sa gaban ta kamar yanda suka nuna mata zazzafar qiyayya, ta na zaune ne kawai saboda son mijin ta da yaron ta, Hajiya Mama ta tabbatar da cewa Mahwish na hakuri da ganin su ne saboda ita ba mai mugun hali bace kamar su, da wata ce tabbas sai ta dauki fansar abinda suka aikata mata, amma Mahwish sai ta dena shiga sabgar su da yi masu duk wata hidima da take masu a baya, ba kuma ta zaman gaba da su, ba ta nuna masu qiyayya, sai a yanzu Hajiya Mama ta gane Mahwish na zaune da su ne kawai, amma zuciyar ta na cike da qunci da baqin cikin abubuwan da suka aikata mata, ji ta yi ana qoqarin d'aga ta daga bakin qofar, qarasa miqewa ta yi ta na share hawayen ta, tare da sanya wani busasshen murmushi a fuskar ta, Zaituna da Sa'eed ta gani akan ta, kuka ta fashe da shi sannan ta ce,
"Sa'eed ka taimaka ka nema min gafarar wannan yarinyar, idan na mutu a haka ba abinda zai hana walakiri yi min shegen duka, ka dai san duk irin abubuwan da na aikata mata, na san zai dau lokaci kafin zuciyar ta ta yi sanyi, dan Allah ka taimaka min kai ma ka yafe min duk abinda na maka,"
Murmushin da bai kai zuci ba Sa'eed ya yi sannan ya ce,
" Hajiya Mama kenan, ni d'an ki ne, na jima da yafe maki duk abinda ki ka aikata min, saboda ba zan taba yarda na qi yafe maki ba Allah ya azabtar da ke, dan na san tsakanin Allah da bawan shi yana yafe zunubi, amma tsakanin bawan Allah da wani bawan Allah din Allah baya yafe haqqin wani bawan akan wani bawan, ko da tsakanin bawa da ubangiji babu zunubi to in bawan nan na da haqqin mutane akan shi ba zai samu rahamar Allah ba, har sai bayin Allah sun yafe masa abubuwan da ya musu, Hajiya Mama na yafe maku, Mahwish kuwa zan roqe ta ta yafe maku, amma ba zan tursasa ta ba, saboda an cutar da ita, an wahalar da ita, wahalarwar da ba kowacce mace bace za ta iya daukan irin azabobin da kuka gana mata ba da sunan zaman aure, mata da dama za su hakura da wannan auren tun a karon farko ba sai abu ya yi nisa ba ma, dan haka ku je ku kwanta, inshaa Allahu zuwa gobe zan mata magana"
Tun da Sa'eed ya fara magana kunyar shi ta kama su, tabbas shi din yaro ne mai biyayya a gare su, ya na gudun bacin ran su, Zaituna kuwa kamar ita ta haife shi ba Hajiya Maman ba ma, yanda take bashi Umarni da juya shi,ya yi musu biyayya iya biyayya, albarka Hajiya Mama ta dinga sanya mashi har ya raka su sashen su ya koma, tsaya wa ya yi ya na kallon dakin Mahwish da ta kunna fitila, ya na hango ta ta cikin labule ta na tsaye sanye da hijabi, da alama sallah take, fatan shi Allah ya sa ba qarar su Hajiya Mama take kai wa Allah ba, dan kuwa Allah baya bata lokaci wajen amsa addu'ar wanda aka zalunta, ji ya yi kwalla ta taru a idanun shi, shikenan yanzu su Hajiya Mama za su fara ganin bala'i da masifa, dan ya tabbata in bata yafe masu ba sun dinga ganin tashin hankali kenan, ko zuwa ze yi yanzu ya bata hakuri? To amma ai sallah take, kar ya katse ta, ya zai yi ne? Ya na nan tsaye, ya ga Sumayya ta bude qofa ta na kallon shi, yanayin da ta kalle shi da shi ne ya sanyaya jikin shi, kallo ne irin na mace mai son danne kishin ta, dan kuwa ta ga inda yake kallo, ita ma ta ga Mahwish din, da sauri ya bi bayan ta, tare da tsaida ita amma bata tsaya ba, ta shiga ciki, a gaban ta ya tsaya ya kama hannayen ta dika biyun, idanun ta a rufe suke saboda bata so ta bude su ya gano tsantsar kishin da ke ran ta,
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........