Haka suka kwana rai ba dad'i, Mahwish na ganin ba ta da laifi a maganar ta, shi kuma ya na ganin bata kyauta masa ba, bai kamata ta fad'i magana mai zafi game da mahaifiyar shi ba irin wannan.Da safe kowa ya kama harkar gaban shi, ba tare da ya kula ta ba, ya wuce wajen Hajiya Mama ya gaishe ta, ta qi amsa wa, ya jima a zaune a gaban ta, bai ce komai ba, ita ma bata ce komai ba, sai da ta ga ba shi da niyyar tashi a gaban ta ne ta ce,
"Kaiii in dai ba so ka ke ka hango yatsun ungozoma ta ba a goshi na , tashi ka bar nan, ban kira ka ba, ko na kira ka? Shanyayye?"
"Dan Allah Hajiya Mama ki yi hakuri, ki yafe min, in akwai laifin da na maki, a rayuwa ta, ko nake maki, a iya sani na, ni mai biyayya ne a gare ki, ban taba tsallake duk wata doka taki ba, amma sau d'aya a rayuwa ta na zabi matar da nake so na rayu da ita, ki ke nuna ba ki qaunar ta, abun ma bai tsaya akai na ba, har ita ya shafa, Hajiya Mama dan...."
"Sannu alqali, ka zo ka tisa ni a gaba da maganganun banza, to bari kaji, har abada ba zan so matar ka ba, tunda ku ke nuna min ku yaran zamani ne, zan nuna Maki ni uwar zamani ce, shege ka fasa a tsakanin mu, ka ban waje ko ran ka ya fi na kwarton da aka kama b'aci Sa'eed"
Hakuri dai ya sake bata ya bar sashen ta, bai koma sashen Mahwish ba ya bar gidan a motar shi, ya na hanya Tasneem ta kira shi, ta na roqon shi kud'i wai za a sai wa yarinyar da suka je bikin ta kayan gado, iyayen ba su da qarfi,shi ne ta tausaya musu, tausayin sai ya shige shi, nan da nan ya tsaya a gefen hanya, ya tura mata dubu d'ari biyar, tare da saqon gaisuwa zuwa ga Goggon ta, ya musu fatan alkhairi, ya so tambayar ta yaushe za su dawo, amma can qasan ran shi ya ji dadin tafiyar da suka yi, a qallah mai d'aga masa hankali da bani bani tare da masa rashin kunya bata nan, damuwar shi yanzu ta zama d'aya, wato damuwar Mahwish.
A qofar gidan su ya tsaida motar shi ya kai kimanin minti biyar a zaune, ya na tattara nutsuwar shi a cikin jikin shi kafin ya yi sallama, ya shiga,firar dankalin Hausa ya tarar da su Xulaihah da Hajiya na yi, su na hira, da sauri Xulaihah ta miqa masa kujera sannan ta gaishe shi, amsa wa ya yi, cikin sakin fuska, da tsokanar ta,
"Xulaihah ni fa ban gane me ya sa Abubakar ke yawan cewa na gaishe ki ba, ko dai akwai wata a qasa ne da mu bamu sani ba? Me ku ke qulla wa ne?"
Da sauri ta rufe fuskar ta, dan sai ta ji kamar yanzu ne abinda ya faru daren jiya tsakanin ta da Abubakar ke faruwa, a daren jiyan ya bayyana mata soyayyar shi, cikin wani irin salo mai tsaya wa a rai, a duk sanda ta tuna kalaman shi sai tsigar jikin ta ta tashi, ta ji wani irin son shi da bata dan sanda ya shige ta ba ya motsa a ran ta.
Daki ta shige da gudu, ta na dariya, shi ma Sa'eed cikin dariya ya ce,
"In ta yi wari ma ji ko Hajiyar mu? Shi ma in na tambaye shi sai ya qi cewa komai, ya ce in komai ya tabbata zan ji, koma dai mene ne, ina fatan abinda nake zargi ya tabbata, lallai da kun samu abokan rayuwa nagari, ke da shi kun dace, a iya sani na ku din mutanen kirki ne, Allah ya tabbatar da alkhairi"
"Ameen ya Allah, ai in fada maka yarinyar nan kunya kamar ita aka haifa a riga ba ni ba, na mata tambaya akan shi ya fi sau shida a satin nan, amma ta qi sanar da ni komai"
Cikin dariya Sa'eed ya ce,
"Ai mu bar su kawai, dole dai a sanar da mu, a matsayi na na babban yaya in ku ka bata lokaci na ce ba za ai auren ba ba shi kenan ba"
Dariya Hajiya ta yi, cikin ran ta kuwa so kawai take ta ji kyakkyawan labari akan Mahwish daga gare shi, Sa'eed ne ya gyara zama, ya sanya hannu ya dauki dankalin da ya fadi qasa ya mayar robar da suke tarawa ya ce,
"Ammmm....Hajiya Abba na gida kuwa? Ina so na gan shi dan Allah in ya na nan"
"Eh ya na nan, ya dan koma bacci ne, ko kuma aiki yake, kasan yanayin aikin su ba zama"
DU LIEST GERADE
MAHWISH
RomantikQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........