MAHWISH PAGE 51

47 8 1
                                    

Hajiya ba ta dawo gidan ba, sai da hantsi, a lokacin MAHWISH da Sa'eed, sun yi wanka, sun shirya, su na yin abincin karya wa a tare, sai hira suke, kamar ba su taba shan wata wahala ba a rayuwar su.

Cike da jin nauyin junan su, suka gaisa, Hajiya ta wuce d'akin da yake a mazaunin na ta, wanka ta yi, ta na fito wa ta tarar da abinci sai tashin qamashi yake, da tea na fitar da tururi da alama ba a jima da gama wa ba, sai da ta shirya cikin shirin bacci, sannan ta zauna ta ci, ta qoshi, ta yi hamdala, sannan  ta nemi waje ta yi kwanciyar ta, dan rama baccin da bata samu yi ba a daren jiya.

Su MAHWISH kuwa ana can ana qara'in soyayya a wajen cin abinci,ba tare da zato ko tsammani ba Sa'eed ya ji muryar MAHWISH na fadin.

"zuma na a gaskiya in Hajiya za ta tafi tare za mu koma, ni na gaji da zama anan, ina so in je qasa ta, ga bikin Zulaihah ya gabato ka dai san ba za ai ba ni ba ko?"

Shiru Sa'eed ya yi, domin ya san duk abinda ta fada gaskiya ne, to amma ya zai yi? Bata san a halin da ake ciki guduwa ya yi ba, ta ina zai fara mata bayani?

Bai amsa ta ba, sai da ya ji gaba daya ta kwanta a jikin shi, ta na shagwaba, sannan ya sake gyara mata kwanciya a jikin shi, cikin magana mai sanyi ya ce,

"Baby Na na ji me ki ka ce, amma ina so ki dan jira har a gyara gidan can kafin ki koma, saboda baki san abubuwan da na samu ba sanda na koma,ban sanar da ke bane gudun kar hankalin ki ya tashi,so ina ga ki bar Hajiya ta yi gaba, kafin bikin qanwa ta na maki alkawari za mu koma gida, ai kin ga ma ni ne babban yaya, to ta ya ya zai kasance a yi auren qanwa ta bana nan? "

Da sauri ta rungume shi, ta na farin cikin amince war shi, nan da nan ta fara tsara yanda komai,, zai kasance, in ta koma gida, Ludhfi kawai take hango wa a idanun ta, farin cikin da take ji dan tuna Hakan ba shi da misali a zuciyar ta.

******************************

"ke bana son iskanci, wace iriyar magana ki ke, baki gan shi ba kamar wani kwabo? Sa'eed din layar zana gare shi, da za a nema a rasa a cikin gidan nan?"

"To ai se ki je ki duba da kan ki, tunda baki yarda ba, (rashin tarbiyya)"

Ai kuwa a hasale ta fita sashen MAHWISH, ta duba ko ina bata gan shi ba, kwafa ta yi sannan ta koma sashen ta, Ihsan da Zaituna na tattauna possibility din ko dai ya gudu ne.

"ke ban waya ta,.... Za ki tashi ki miqon ko sai na dura miki ashar?"

Tura baki Ihsan ta yi, sannan ta miqe ta miqa wa Hajiya Mama wayar ta, bata b'ata lokaci ba wajen danna kiran Sa'eed, Number din shi ta Nigeria dai ba ta tafiya, Hakan ya bata tabbacin baya qasar ma gaba daya kenan, Layin shi na Saudiyya ta kira, cikin sa'a kuwa ya shiga, ta yi ringing har ta tsinke ba a dauka ba, wani irin ashar su Zaituna suka ji ta saki, sannan ta zauna dab'ar a kujera.

"Ni Adama, ni ce zan haifi yaro a ciki na, sannan ya guje ni saboda wata macen? Lallai Mashawi ko da boka ki ke yawo sai na nuna miki ni Adama bokanyar kai na ce, Zaituna shirya mu fita"

Ba bata lokaci Zaituna ta shirya, suka bar gidan da Hajiya Mama, aka bar Ihsan da Ludhfi, wanda ke baccin shi hankali kwance, dan kuwa dika dika qarfe 7:45am ne.

Itan ma dakin ta ta shige ta yi kwanciyar ta, ta na murnar za a kawo qarshen MAHWISH.

Sun jima a gaban boka su na kora bayani, boka ya zayyana musu qudirin su Sa'eed din, ta hanyar duba da ya yi.

"Boka ni abinda nake so, na fi son ta dawo inda muke, ta nan ne zan sa musu ido sosai, in dinga ganin shige da ficen su,ta haka ne zan raba ta da yaro na, tunda duk wata wahala mun ba wa yarinyar nan, amma ta kafe ta nace,"

"Duk abinda ki ke so za a yi, amma aikin na da tsada,"

"kar ka ji komai, a shirye na zo"

A gaban su, ya yi duk wani surkulle da zai yi, sannan ya ce su je, za su ga abinda zai faru.

MAHWISHOnde histórias criam vida. Descubra agora