Mahwish na ganin Sa'eed ya shigo hannun ta na rawa, ta na kuka ta sanya wayar a handsfree , sannan ta ce,
"Hajiya Mama me zan fara, ban fahimce ki ba,"
Sa'eed ma ya ce,
"Me za ta fara?"
Jin Muryar Sa'eed a kusa ne ya sanya Hajiya Mama sauya maganar ta, ta ce,
"Cewa na yi ta fara shirin had'a kayan ta, ta dawo Nigeria, zaman a nan ya ishe ta haka, Tasneem nake so ta dawo nan ta zauna, ni ma ina da burin tawa 'yar ta zauna a qasa mai tsarki, ba ita kad'ai za ta zauna anan ba, shafaffiya da mai"
"Hajiya Mama kar ki damu, za ta fara shirin dawowa, inshaa Allahu, ki yi hakuri"
"Ya kamata, dan in ba haka ba....."
Wani.irin sauti ta fitar na rashin mutunci, sannan ta kashe wayar, Mahwish kuwa durqusawa ta yi a wajen ta na kuka, karuwanci? Me zai hada ta da shi? A gaskiya lamarin su Hajiya Mama ya fara bata tsoro, anya ba za ta hakura da wannan auren ba? Tunawa ta yi da kalaman Sa'eed, a yanzu kullum nuna mata yake, za su iya rayuwar su, ba tare da kowa ba, su rabu da kowa su riqe junan su, ya mata alqawari ba zai sake zuwa gida Nigeria ba, har sai ta warke daga ciwon da ya same ta na shaye shaye ,indai shi zai iya hakura da iyayen shi, me zai hana itama ta rage kiran mutanen gidan su? Sannan ta boye sirrin su?ita amma me ya kamata ta yi yanzu? Shin ta sanar da 'yan uwan ta halin da take ciki? Kar kuma hakan ya bata ran Sa'eed ko ya b'ata shi a idon mahaifan ta rasa madafar da za ta dafa na matuqar sanya ta a matsanancin tashin hankali da damuwa, ta yanda har sai abun ya kai su da kwanta wa a asibiti.
Kukan da take ya yi tsanani, damuwar ta kullum qaruwa take, hankalin ta ba a kwance yake ba, hawan jinin ta kullum sake tashi yake, asibiti kuwa ya zame musu kamar shiga d'aki da fitowa, dan kuwa kusan kullum sai sun je.
Watarana Mahwish na zaune, sai ta fara jin ta na so ta karanta qur'ani ko da da ka ne, tunda ta sauke, kuma ta na da haddar ta, lalube ta fara yi cikin kwakwalwar ta, amma ta kasa kama ko da aya d'aya ne ta karanta, balle a kai ga sura d'aya, abun ya bata mamaki matuqa, cikin tsananin damuwa da tashin hankali ta dakko qur'anin ta bude ta fara karantawa, jin ta take kamar wata 'yar koyo a fagen karatun qur'anin, nan da nan hawaye ya fara zuba, kukan ta ya yi tsananin da har sai da ta jiqe page din da ta bud'e dan karantawa, Sa'eed ne ya shiga ya karbi qur'anin, ya d'aga ta, ya rungume ta, ya na lallashin ta, cikin kuka ta ce,
"Yah Sa'eed rayuwa ta ta zama bata da amfani yanzu, Yah Sa'eed qarfi na ya qare, ba zan iya ba, na gaji, addu'a muke amma kamar ba ma yi, anya Allah ya na amsa addu'ar mu kuwa? Anya ba mu aikata babban laifin da Allah ya daina duban mu ba"
"Subhanallah, Mahwish kar ki yi sab'o da kalaman ki,Allah mai ji ne, kuma mai gani ne, sannan ya na amsa addu'ar bayin shi, ki sa a ran ki duk yanda mu ka so mu sama wa kan mu mafita akan wannan lamarin, ba zai samu ba, har sai sanda Allah ya so, hanyoyin amsa addu'a na da yawa, bamu sani ba, wataqila akwai musibar da ta fi wadda muke ciki Allah ya kare mana ita, ko ya jinkirta mana ne ya ga hakurin mu, a lahira ya saka mana da alkhairi, ko ya na nan ya na ji, akwai lokacin da ya d'ebar mana ya yaye mana dukkan quncin da muke ciki, ya zama kamar ba a yi ba, baby ki qara hakuri, lokaci na nan zuwa da komai zai zama tarihi, baby ba na so mu gaza hakuri mu zobe ladan mu ya zama mun sha wahala a banza, ki qara hakuri kin ji?"
Daga masa kai kawai ta yi, dan kuwa ba ta da sauran abun cewa, amma dai za ta so ta sanar da ko da Xulaihah ne, ko Hajiya abinda ke faruwa da ita.
Sa'eed kuwa koma wa ya yi parlour ya ci gaba da kallon shi.
Yunqura wa ta yi ta sauka daga gadon dan daukar wayar ta ta kira Hajiya ta sanar da ita halin da suke ciki, waya ta ce daukar ni a inda ki ka aje.
Tun bata fara damuwa ba, har dai ta shiga tsananin damuwa, kiran Sa'eed ta dinga yi, da qarfi, da sauri ya shiga d'akin ya ce mata

YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........