Tasneem bata kwanta ba sai da ta aiwatar da abinda bokan ta ya umarce ta da kyar dan kuwa b'angaren Mahwish a kulle ya ke, da kirsa da kisisina ta sa ya bud'e mata da sunan za ta ga bangaren qanwar ta ta,sun yi kutun kutun an fasa kai ta gidan ta ita kadai, anan za a had'a su yanzu, ta lallab'a sa'eed tare da nuna masa cewar in an kawo amarya ba lallai ta kalla ba,bayan ya bude mata ya wuce daki ya kwanta dan huce gajiyar biki da ke jikin shi,Allah Allah Ya ke gobe ta yi, ya yi shiri tsafff dan tarbar amaryar shi, farin ciki ya hana shi rintsawa, dan haka tashi ya yi, ya shiga bayi dan yin alwala, a daidai wannan lokacin Tasneem ta koma d'akin ta kwanta ta na murmushin mugunta, cikin zuciyar ta kuwa banda sharri ba abinda take saqawa da kwance wa, bata jin za ta iya hakuri ta jira Hajiyar Sa'eed d'in, tunda ba su za a yi wa kishiya ba, hankalin su kwance su na fad'in ta bari a yi auren, ba wadda ta fi bata takaici da nuna mata halin ko in kula akan kishiyar da za a mata face Aunty Zaituna, amma in ba mai taimaka mata za ta taimaki kan ta, ai ta san hanyar duk inda ake zuwa neman taimakon.
A kan idon ta Sa'eed ya tada sallah, ya na sallah ta na kallon shi, takaicin rashin son da yake mata na taso mata ya na tokare mata duk wata kafa dake sada numfashi a huhun ta, me ta rasa? Me ye laifin soyayyar da take masa? Ba ya ganin kowa a idon shi sai yarinyar da bata san darajar shi ba, yarinyar da bata d'auke shi ma a namiji ba ballantana ta so shi, ba komai, mu je zuwa.
Juya bayan ta ta yi, ta gyara kwanciyar ta, tare da rintse idanun ta ta na hango dramar da za a sha tsakanin ango da amarya gobe, dan ta yi imani da maganin bokan ta, ta tabbata za a samu b'araka a tsakanin ango da amarya gobe, murmushi ta zabga mai sauti.
Shi kuwa bawan Allah Sa'eed ya na raka'a ta farko sai zuba karatun Kur'ani ya ke, kusan a haka ya kwana daren ranar, in ya yi sallah ya sallame ya yi addu'a,sai ya ji ba ya jin bacci, dole ya sake tashi ya qaro wasu raka'o'in, a haka asuba ta yi, ya yi shirin tafiya masallaci.
************************
An daura auren ango Sa'eed da amarya Mahwish akan sadaki dubu d'ari da hamsin, wanda dubban mutane suka shaida hakan, a ranar ta juma'a, Sa'eed cike yake da farin ciki wanda ba zai tab'a misaltuwa ba, ji yake kamar babu sauran mai farin cikin da ya zarta shi a duniya, fara'ar shi sai ta qarawa shigar shi ta farin kaya kyau, gaisawa kawai yake da mutane ya na musu godiya.
Salim na gefe ya na masa murmushin mugunta, domin ya sani aure dai an d'aura da Sa'eed ne, amma a zuciyar Mahwish shi ne mijin ta, to ai shi ne babban mai riba (a ganin shi).
************************
Sanda labarin d'aura auren Mahwish ya riske ta, mutanen gidan nan sun ga tashin hankali da bala'i a wajen Mahwish, ta yi kuka, ta yi surutai wanda sam basu dace ba, ta yi fashe fashe da iface iface, amma inaaa aikin gama ya gama, ta zama mata a wajen Sa'eed, wayar ta ta dauka ta kira Salim, kuka take har Muryar ta bata fita, hawayen ma sun qafe, ta rasa inda za ta saka ran ta ta ji dad'i Xulaihah ma kan ta kukan take, domin tsananin tausayin yayar ta ta, a ganin Xulaihah wannan abun ba abun damuwa bane, da zata kwantar da hankalin ta, da ta gode wa iyayen su akan zab'in da suka mata, Sa'eed miji ne da kowacce mace zata yi fatan samu, miji mai addini da kula da ibada ga kyau, ga kud'i, ga ilimin addini da na zamani, to me take nema?
Kamar an daki kan ta haka ta juya dan jin me Mahwish ke fadi cikin dasasshiyar murya.
".....baka so na Yah Salim tabbas, da kana so na da baka bari an d'auran wannan auren ba, dan Allah ka zo mu gudu, mu bar gidan nan, mu bar musu garin ma baki d'aya, ba zan iya rayuwa da kowa ba in ba kai ba, Yah Salim zan kashe kai na in baka zo ka ɗauke Ni daga wajen nan ba, kai kad'ai nake so, kai ne zab'i na, kai ne miji na ba wani banzan Sa'eed ba"
Daga can bangaren Salim kuwa, tunda suke yau ne ya tab'a jin wani abu na gaskiya game da ita, a baya ya sani jikin ta ya fi so, amma yau kalaman ta sun daki zuciyar shi, ya tabbata zai wahala a samu yarinyar da za ta so shi sama da Mahwish, hawayen da suka gangaro masa ya yi sauri ya share, dan kuwa har yanzu su na wajen d'aura auren, hannu ya sa ya kare bakin shi, sannan ya fara magana.
![](https://img.wattpad.com/cover/292798077-288-k314670.jpg)
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........