"bayan kimanin watanni bakwai da mutuwar aure na, manema suka ce salamu alaikum, samari da basu tab'a aure ba sun fito a yi da su, dattijan da sun isa su haifi kamata suma su na layi, da wadanda ba za su wuce arba'in ba a shekaru, a wannan lokacin gaskiya na ga masoya kala², har abun ya dinga ba ni mamaki, se kace wadda suke jira na fito daga gidan miji su kawo caffa""Ana haka mahaifa na suka kira ni, suka ba ni shawara akan na fidda miji a cikin tarin maneman da nake da su,mutane na ta qananan magana akan yawan zuwan manema aure na, nan take na sanar da su ni yanzu aure baya gaba na, domin na yi shi ban ji da dad'i ba, ba ribar da na samu sai tashin hankali da baqin ciki, Umman mu ta so ta matsa Baba ya ce a bar ni komai lokaci ne, in lokaci ya yi ko bana so, ko ina so sai an yi, a haka aka bar maganar, iyaye na na min addu'a ni ma ina yi kai na"
" Wata rana ina zaune a zauren mu na kusa da tsakar gida ina shan iska, Umma na na daki ta na qailula, sai yaro ya shigo tare da sallama, ya ce min ana sallama da ni, na ce in ji wa? Ya ce shi ma be sani ba, nan take na miqe na sanya hijabi na na fita dan ganin ko wane ne, ina fita na ga wani tsohon aboki na, tare mukai wasa da shi, tun dawowar mu garin, maqota muke da su, sun san iyaye na iyaye na sun san nashi, akwai sanayya sosai a tsakanin mu, dan haka ina fita na sakar masa murmushi irin na sanayya, shi ma murmushin ya mayar min, muka yi musayar gaisuwa cikin yaren su na Kanuri"
"Gyara tsayuwar shi ya yi, tare da sanya hannu ya gyara zaman hular shi Zanna bukar ya kalle ni cikin wani yanayi da salon sace zuciya sannan ya ce,"
'Sumayya, na san za ki mamakin gani na anan,amma ba abun mamaki bane, na zo ne dan qarfafa qawancen mu na yarinta ya koma soyayya irin ta auratayya, ina so ki amince da ni ki bani dama na turo magabata na a daura mana aure, ke ni ko da yau ne ma ina so saboda na jima ina dakon soyayyar ki ban samu damar bayyana wa ba sai yanzu, ina fatan za ki bani damar zama miji a gare ki? '
"Kallon shi na yi daga sama har qasa, na jima ina kallon kowanne saqo da lungu a jikin shi, dogo ne sosai irin mazan nan da ake kira da giant, kafin in sauke ido na a saman idanun shi, sannan na ce,'"
'Yanzu kai Grema kai ne ka zo da kan ka ba aiko ka akai ba, har ka iya furta ka na so na? Amma dai wannan yaron ka bala'in raina min hankali, a zato na fa aiko ka akai, ni yanzu ban fi qarfin tunanin ka ba? Shekara nawa ka bani? Shekara d'aya fa ko ka manta ne in tuna maka? Wani yaro da kai zaka zo ka ce ni ka ke so, to bari ka ji, ni Sumayyah na fi qarfin yara, sai dai yayun yara, saboda yaro ya yi kadan ya iya riqo na a matsayin mata, to wa zai na wani fada ni da kai? Ko kuma in ce ta yaya zaka iya da dawainiya ta kai kan ka neman taimakon a kula da yarintar ka ka ke, ka ga dan Allah mu bar ma wannan maganar, da aiko ka aka yi ne sai in yarda in auri wanda ya aiko ka ya ci darajar ka,amma yanzu dan Allah a ci gaba da zumunci kawai, banda maganar aure, aureee inaaa ba wannan maganar haba Grema, dika dika nawa ka ke? Ta yaya zan auri wanda yake sa'a na? '
"Ashe cikin rashin sani kalamai na sun yi matuqar qona zuciyar Grema, dan haka ba tare da ya sake jaddada soyayyar shi ba ya min sallama ya wuce, bayan tafiyar shi ina zaune sai na ke jin dariya, ina ganin dika dika nawa yake da zai wani nace ya ce ya na so na? Abun ba a girman jiki yake ba, mace kamata da na taba aure ina buqatar babba mai hankali, ba yaro ba da za mu yi ta yarinta, tunda ni dai ya min kadan a miji gaba daya na raina shi, ya zama miji na, to ko a yayana ya zo zan iya juya wa na koma yayar shi, dan haka ban ga dalilin da zai sa in auri yaro ba"
"Matar Grema ta dauki tsanar duniya ta dora ta akai na, rashin mutunci da tashin hankali ba kalar wanda ban gani ba saboda haka za ta zo gidan mu tai ta zage zage ta na rashin mutunci da cin alwashin kar in sake in auri mijin ta, in na auri mijin ta zan ga tashin hankalin da ban taba ganin irin shi ba, ni kuma na tabbata kishiya ba ta isa hana ni zaman gidan miji ba, sai dai in ni ce na ji bana son miji, masifa da bala'i wanne ne ban iya ba dan haka ba wanda ya kula ta, dangin shi kan su ba qaunar irin rashin mutuncin da take min suke ba, mahaifiyar shi 'yar kano to Jiddah ce, ta na masifar so na, haka mahaifin shi, dan haka bana jin kishiya za ta hana ni aure a kaf rayuwa ta"
BINABASA MO ANG
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........