Washegari Mahwish ta tashi da tsananin bacin rai, domin plan din su ya rushe, banda zagin Sa'eed ba abinda take yi cikin zuciyar ta, ta zage shi ya fi cikin carbi, da tasbihi ta ke tabbas da ta samu lada mai tarin yawa.Ganin halin da take ciki ne ya sanya Xulaihah tsuke d'an k'aramin bakin ta, ta hau aikace aikacen ta, kar ta ja wa kan ta rashin mutuncin Mahwish, sanin hali ya fi sanin kama.
Zaune take a tsakiyar parlour ta na shan tea, ta na danna wayar ta, Abban su ya d'aga labulen parlour'n ya ce,
"Mahwish dear, ki fa fara shirin tarbar baqi, dan kuwa yau 'yan uwa na na qauye za su zo, dan Allah ba na son wannan halin naki sabo da ki ke yi yanzu, ki kyautata halayyar ki, ke d'in mutuniyar kirki ce, amma yanzu kin sauya gaba d'aya kin koma wata daban, dan Allah ki dawo da kyakkyawan halin ki da kowa ke sha'awa kin ji?"
Da fari ta yi matuqar jin haushin zuwan 'yan uwan mahaifin nata na kauye saboda auren ta da maqiyin ta Sa'eed, to amma yabon da Abban ta ya mata ya sanyaya mata zuciya, kowa na manta cewa ita ta mutane ce, mai fara'a, mai wasa da dariya, mai barkwanci,kowa na manta itan ta kowa ce, kuma kowa nata ne, wannan qaddararren auren dolen ne ya sauya mata halaye daga mai kunya zuwa mara kunya, auren dole kuwa ba wanda yake son shi, to ita dan me za a qaqaba mata wani Sa'eed ta na zaune lafiya? Ga Salim d'in ta d'an dangi, kowa ya san shi, an san halayyar iyayen shi da shi kan shi, wane ne kuma Sa'eed a mutane?
"Baki ce komai ba Mahwish, pls ki min alqawarin za ki zama at your best behavior, ba za ki yi abinda za a tafi da ke a baki ba ana baki da tarbiyya,"
Dan tura baki ta yi kafin ta kurbi tea d'in ta da ya riga ya yi sanyi, sannan ta ce,
"Na maka alqawari kuma zan cika maka inshaa Allahu, za a yi komai lafiya ba tare da tashin hankali ba, ni zan zama mai cika alqawari ko da zuciya ta bata so, amma Abba ka ban mamaki da ba za ka iya cika min alqawarin da ka dauka ba na aura min wanda nake so,komai wuya komai rintsi, sai gashi ba tare da wani yunqurin mai nisa ba ka amince da aurar da ni ga wanda zuciya ta da ruhi na ba su son shi kuma.ba sa qaunar shi, Abba..."
Kafin ta kai qarshen kalaman ta hawaye sun wanke mata fuskar ta, ya na ganin haka ya san magana ta ke so ta ja,aiko se ta hau masa magiyar ya aura mata Salim shi kuwa ba shi da iko akan hakan, ba ya so akan ta ya b'ata zumuncin shi da 'yan uwan shi, tunda Salim d'in nan nasu ne suma, amma suka zab'i bare akan shi, dan ganin baren shi ne ya fi cancanta 'yar shi ta aura, to akan me zai watsa musu qasa a ido, bayan qauna ce da soyayya ta sanya su yin hakan ba qiyayya ba?
Wucewar shi ya yi, ya bar ta ta na sana'ar da ta fara mara riba, wato kuka.
Salim ta Kira ta ce ya je ya raka ta gidan da ake mata gyaran jiki,a hausawa can bawo road, gidan wata 'yar Sudan da ta kware a gyara amare, ba musu kuwa ya amince, ajiye wayar ta tayi, ta fara shirya wa, ta na kammalawa ya mata waya ya na qofar gida, cikin sauri ta wa kowa sallama ta fice.
Machine din shi roba roba ta d'ale, shi kuwa ya qara boqarewa yanda zai dinga tab'a ta da kyau, ta na jin yanda yake gogar qirjin ta, amma ita bata kawo wa ran ta ya na sane yake hakan ba, a zaton ta yanayi ne na zaman machine din ya kawo hakan.
Tun da suka tafi suke zuba hirar su ta soyayya kamar sun manta da abinda ke tunkarar rayuwar su a gaba har suka isa gidan gyaran jikin.
Duk tsahon awannin da Mahwish ta dauka a gidan Salim na waje na jiran ta, ya gaji matuqa amma ya na so ya ga kyakkyawar qanwar tashi wadda yake ganin duk duniya ba ya ita a kyau.
Ta na fitowa kuwa ya sauke wata ajiyar zuciya mai qarfi, tare da lashe leben bakin shi, fuskar ta sai walqiya take saboda yanda ta ji gyara, jikin ta na ta tashin qamshi kamar an mata barin turaren larabawa, ta na isa ta zube a gefen shi cike da shagwaba ta hau bude hannayen ta, ta na fad'in,
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........