MAHWISH PART 2 PAGE 7

62 8 3
                                    

Tsayawa Hajiya Mama ta yi, dauke da kwano a hannu, ta na jiran Sa'eed ya isa wajen nasu, Sumayyah na gefe, ta na tunanin mafita, tare da fatan kar Hajiya Mama ta bashi labarin me ke faruwa.

"Ahh Hajiya Mama?"

"Ai ina hango ka na ce bari na jira ka qaraso, a gaisa,"

Risinawa ya dan yi, sannan ya gaishe ta, Sumayyah ma ta risina ta gaida shi, bin su ya yi da kallo, a hankali ya fahimci me ke faruwa,

'Sumayyah sarkin qoqari, har ta gama dafa mata naman kenan'

Shi ne abinda Sa'eed ke ayyana wa a ran shi, Sumayyah kuwa fatan ta kar wannan matar mai shegen surutu ta furta wani abun da zai b'ata ta a idon Sa'eed.

Ba tare da ya jira komai ba ya ce,

"Bari in dan shiga ciki in watsa ruwa, a gajiye nake yau sosai"

"Ahh ya kamata, ai kana ma qoqari, kai dai Allah ya maka albarka, nima bari na qarasa wajen waccan yar buta uban, in ji dalilin lalata min abinci na da tai,"

Ta na gama fadin haka ta sa kai tai gaba, Sa'eed kuwa kallon Sumayyah ya yi da neman qarin bayani, daga kafada ta yi sannan ta ce,

" Ni ma ban gama sanin me ya faru ba,ta dai zo ta na tambayar ko na gama dafa naman, na ce eh, ta zauna ta fara ci anan, sannan ta dau sauran xa ta wuce, sai na ji ta na cewa Ihsan ta bata mata abinci"

Murmishi kawai ya yi, a iya sanin shi da Hajiya Mama, ba wani abu da ya faru, ta fada ne kawai dan kar a ga kwadayin ta,

"Allah ya kyauta, bari in je in wanka, Allah ya saka maki da alkhairi"

"Ameen,"

Wucewa sashen Mahwish ya yi, ta shiga nata, Mahwish ke da girki, amma Sumayyah ke taimaka mata, saboda laulayi baya barin ta yin ayyuka sosai, watarana ma Sa'eed din kan shi Sumayyah take tura wa shi, ya je can ya kwana, saboda ba za ta iya da fitinar shi ba, bata da kwarin yin hakan.

Ko da Sa'eed ya shiga sashen Mahwish, gani ya yi ta na gyara saman table, ta gama aje komai, ta yi kwalliyar ta daidai misali, da sauri ya nufe ta, nan da nan ta saki wata iriyar fara'a, buda mata hannayen shi ya yi, kafin ta rungume shi, Ludhfi ya tafi da gudu ya rungume shi tare da fadin,

"Abbaaahhh"

Dariya su Mahwish suka saka, kafin daga baya ta maqale hannayen ta a qirjin ta, irin na yara masu shagwaba, tura bakin ta ta yi gaba da alamun ta na so ta yi kuka, da sauri Ludhfi da Sa'eed suka qarasa wajen ta, su na rige rigen son sanin me ya same ta take so ta yi kuka,

"Baby na me ne ne/Mama Abba ne?"

Kallon yaron Sa'eed ya yi, ya daga gira,

"Ka ji min yaro, daga dawowa ta, sai kuma a nemi a doran laifi? Ina laifin ka tambaye ta me akai mata, amma kai tsaye ka ce ni ne? To bani bane ni, ni yanzu ma na shigo gidan"

Dariya sosai Mahwish ta sanya, sannan ta bude hannayen ta ta ce,

"Ni ma sai an min irin na Ludhfiiii"

Qarasa maganar ta tayi cike da shagwaba, Ludhfi da Sa'eed suka hau yi mata dariya, qin rungumar ta ya yi, ya dauki Ludhfi suka shige ciki, suka barta tana bubbuga qafa irin na yara, bayan sun shige ne ta daga murya ta ce,

"shikenan ku je din, na yi fushi, kuma ba zan kula ku ba yau"

A bakin kofar bathroom Sa'eed ya ajiye Ludhfi, ya na ajiye shi yaron ya fita da gudu sai wajen Sumayyah, ya na matuqar son Sumayyah, ita ma ta na son shi tsakani da Allah, tana kyautata masa sosai, haka in laifi ya yi, ko a gaban waye za ta hukunta shi, ba ta boye komai a game da shi, ta na nuna masa yanda take tsananin son shi, shi ya sa yake son ta shima.

MAHWISHTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang