MAHWISH PAGE 28

30 3 0
                                    

"Malama me ya shigo da ke kuma? Ko akwai wani abu naki anan sashen ne?"

Dariya Ihsan ta yi sannan ta ce,

"Ni kuwa nake da abu anan, tunda Yaya na, uwa d'aya, uba d'aya na nan,"

"Ohhhh ashe fa alaqar ku da shi kenan? Lallai kuwa an yi azzalumar 'yar uwa, kuma na taya Sa'eed baqin cikin rashin dacen dangi, ke ba zan iya sa in sa da ke ba, fita ki bar nan, kar ki bari na sake ganin qafar ki anan, kome ki ke so ki jira d'an uwan na ki ya fito sai ku yi da shi, amma nan sashe na ne, inda miji na ya ajiye ni,ok? Dan haka fita"

"Hayaniyar me nake ji ne wai?"

Kuka Ihsan ta fashe da shi, sannan ta ce,

"Ai dole ka ji hayaniya, ka na ji ta na zagi na , da Hajiya Mama, to ki tabbatar wadannan abubuwan da ki ka ce kamar a kunnen ta ki ka fade su"

Da sauri Ihsan ta bar sashen na Mahwish ta yi nasu, baki bud'e Mahwish ke kallon Sa'eed, ta kuma kalli inda Ihsan ta bari, gani ta yi yanayin sa'eed ya sauya, alamar ya yarda da abinda Ihsan ta fada, kallon shi ta yi cikin b'acin rai ta wurgar da mayafin ta, ta wuce ciki.

Ya na nan tsaye tunanin shi ya dawo jikin shi, bai kyauta ba, da sauri ya bi bayan Mahwish wadda ke tsaye ta na cire d'an kunnen ta, sarqa ya cire mata, ya fara kissing wuyan ta, tare da furta mata kalmar,

"I am sorry love, zuciya ta bata jure jin magana mara kyau akan mahaifiya ta, duk da na san halin ta, uwa uwa ce, Mahwish ko ya take ita ta haife Ni, dan Allah ki yi hakuri, kuma ina roqon alfarma a wajen ki, kar ki na bari ku na musayar yawu da su, saboda ko baki fad'a ba ma za a ce kin fad'a, i am sorry kin ji"

"Na ji shawarar ka, kuma in shaa Allah zan kiyaye, amma sai ka karbi punishment akan yarda da ka yi cewar zan iya zagin mahaifiyar ka"

"Ni ? Ni ki ka ji na ce na yarda? Yaushe?"

"A fuskar ka na ga hakan, soooo dole ne ka karbi hukuncin hakan, oya zo nan"

Kwanta wa ta yi ta mimmiqe qafa, ta tada kan ta da pillow ta ce,

"Yi min tausa, kuma ba da qarfi ba, kar ka min tsagewar qashi"

Juya kai ya fara yi, kamar yaron da aka zalunta , ya fara matsa mata qafa, ita kuma ta na sake miqe su, tare da nuna masa jin dad'in tausar da yake mata, daga haka naga Sa'eed ya kashe fitila, cikin duhun na lallab'a na fita.

Washegari da asuba, tare suka shiga wanka, sai hira yake da cikin ta, shi a dole magana yake da babyn shi, tura baki ta yi, cike da shagwaba ta ce,

"Shikenan yanzu da na haihu ka dena kira na da babyn ka, ka yi sabon baby ko? Ni dai gaskiya ba zan yarda ba"

Shure Shure ta hau yi da qafar ta irin na yara masu rikici, ruwan da suke ciki na ta fallatsa waje, kama ta ya yi, ya rungume ya ce,

"Never, ke din baby na ce har abada, i love U Mahwish"

"And I love u more Yah Sa'eed, au Zuma na"

Dariya ya yi, ya ce,

"Yarinyar nan ba kya jin kunya ta ko?"

Kunyar ce ta kama ta, dan ta san ma'anar maganar shi, da sauri ta kulle fuskar ta, su na dariya,

"Kin ga mu yi sauri kar mu makara sallah,"

Da sauri suka qarasa wankan su, suka shirya,shi ya wuce masallaci, ita ta yi sallar ta a gida.

Kafin ya dawo ta tafasa shayi, ta sa a flask,ta koma ta kwanta, dan maida baccin safe.

Ko da ya dawo ya ga abinda ta yi, sai ya shiga kitchen ya fere dankali, ya soya da kwai, ya ajiye sannan shi ma ya kwanta bacci.

Basu tashi ba sai wajejen sha biyu na rana, bayan sun wanke bakin su, ta wuce parlour, ta kwanta a doguwar kujera, shi kuma ya wuce kitchen, dan d'akko musu abinci, ya na zuwa ya had'a duka abinda za su buqata a babban faranti ya dakko ya ajiye a dinning, ta na ganin haka ta miqe cike da murna, ta zauna, a baki ya dinga bata itama ta na bashi, har suka qoshi, ta tattara kwanuka ta kai kitchen ta wanke, ta ajiye kowanne inda ya dace, sannan ta koma ta ce masa.

MAHWISHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora