MAHWISH PART 2 PAGE 2

45 10 1
                                    

A daren wannan rana Saleem ya sha gayu kamar wani sabon ango, mata ana ta hidimar tafiya kai amarya, wayar shi ya dauka ya kira Badi'a, Badi'a kuwa ta na ganin kiran shi ta qi d'aga wa, dan kuwa ta d'auki shawarar Mahwish da gaske ba da wasa ba, ta na matuqar son mijin ta, za ta iya komai dan ganin sun daidaita, ya fara son ta, duk da cewa ta na jin zafin tazarar da ta bashi, amma ta yi imanin hakan shi ne daidai.

Ta yi ringing ta fi sau hud'u ba ta d'auka ba, qarshe message ya tura mata, akan in bata d'auki wayar shi ba, ta manta da koma wa Lagos da shi, hankalin ta ya yi matuqar tashi, hannun ta na rawa ta nufi motar da Mahwish za ta shiga, dan wasu motocin ma tuni sun yi gaba, kafin ta isa har motar ta tashi, wata iriyar zufa ce ke karyo mata, ga kiran Saleem na sake shiga cikin wayar ta, shin ya za ta yi ne?

'Ya Allah ka kawo min dabarar da zan yi, kai na ya kulle'

Kiran Saleem ne ya katse, ba tare da ta dauka ba, hannu na rawa ta sa ta latse makashin wayar gaba dayan ta, ta mutu, qannen ta na ta kiran ta, ta je su tafi kai amarya, amma inaa ko sauraren su bata yi, cikin gidan su Mahwish ta koma, ta na sharar hawayen baqin ciki.

Mahwish kuwa na mota ita da sauran 'yan uwa, ana ta mata nasiha akan ta dena kukan da take tana sake sa Zulaihah kuka, ita ya kamata ta lallashe ta, ba ta sake sanya ta kuka ba.

Ludhfi na manne da Zulaihah shi ma ya na kuka, bai san meke faruwa ba, amma ya ga favorite aunt din shi na kuka, Goggo Zulai ta fara quluwa, cikin fada fada ta ce,

"ke Zulai ban son iskanci ya za ki rungumi yaro ki ta kuka kamar uban ki ya mutu, in auren ne baki so, ni sai in sa a warware shi yanda aka qulla, ji yanda jikin ki ya dau zafi saboda shegen kwalaficin gida, laifin uwar ku ne da ko d'an kwana bata bari ku je yi wani wajen, shi yasa duk ki ka ishi mutane da shegen kuka"

Matar Baffa Sageer ce ta ce,

"Haba Goggon su, wannan fa rana dole ta koka, ba amaryar da ake kaiwa gidan miji bakin ta da dariya komai son da take wa miji,"

"Yo yaran zamanin nan ba sai su baki mamaki ba, Allah Allah suke a kai su gidan miji,"

"Tarbiyyar yaran Hajiya ai kin san daban ta ke Goggon su"

"Eh to ba laifi kam, Allah dai ya basu zaman lafiya, amma in mutum ya ishe ni da kuka gida za a maida shi, ba shikenan ba"

Dariya sauran mutanen da ke motar kawai suka yi, dan sun san ba da wata manufa ta fadi duk abubuwan da ta fadi ba.

Bangaren Saleem kuwa ganin Badi'a ta qi daga wayar shi, kawai sai ya hau motar Baban shi, ya nufi gidan su Mahwish, a mashigar layin su ya aje motar ya kunna kida ya na tunanin ta ina zai fara, ya na cikin tunani ya ga wasu mata sun fita daga gidan su Mahwish din suna ta fadin

"Allah ya sa gidan zaman ta ne, Allah ya basu zuri'a dayyiba,"

Hajiya na ta amsa wa, ta na musu godiya, Hajiya na koma wa sai ya kula ai matan unguwar ne, suka je Allah ya sanya alkhairi.

Da sauri ya bude mota ya kulle ya nufi gidan, kamar a mafarki haka Hajiya ta ga zuwan shi, cikin mamaki suka gaisa, sannan ta shigar da shi parlour su na nan zaune, su na taba hira sama sama, ya ce,

"Hajiya ni kuwa kin gane min Badi'a? Tun da muka zo bikin nan ta watsar da ni Hajiya, yau na kira ta ya fi sau nawa bata amsa ba,"

"Allah sarki, ka san dake ana ta hidima, wataqila bata ga kiran ka bane, kuma ma dai yanzu bana jin tana gidan nan, an tattafi kai amarya, ba kowa gidan, sai baqin dake shigowa a gaisa su tafi, sauran 'yan uwa kuma duk sun koma gidan yaya, tunda can din ya fi girma, "

"Ohhh.. Allah sarki, to bari in jira ta dawo, akwai wata mahimmiyar magana da za mu yi da ita"

"To shikenan, bari in kawo maka abinci"

MAHWISHOù les histoires vivent. Découvrez maintenant