*MAHWISH PART 2*
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 12:
Da sassafe sai ga Ihsan na buga wa Sumayya qofa, Sa'eed ne ya bude, dawowar shi kenan daga masallaci su na karatun qur'ani shi da Sumayya, Ludhfi na wasa a gefen su, dan a nan ya kwana, Sumayya qin ba da shi ta yi, a cewar ta kar ya dami Mahwish tunda har yanzu ba a so ta na aiki mai nauyi, shi kuma akwai rikici wani lokacin, sai ya ce sai ta dauke shi, ko ta goye shi, in ba haka ba, ya yi ta ihu, ya na tada hankalin kowa a gidan, ko da Hajiya Mama ce ta zo goyon shi ba zai yarda ba sai dai Mahwish d'in.
Gaishe da Sa'eed Ihsan ta yi, can ciki, ita ba haka ta so ba, ta so a ce Sumayya ce ta je ta bude, ta mata gargadin ta hanzarta kammala bada labarin ta, dan kuwa ba ta da lokaci, labarin rayuwar ta ya riga ya wuce, ita kuwa yanzu take son nata ya fara, uban yaran ta ya qi maida ta, ko yana son maida ta ba hali, ta sha wahala da kyar ta samo Munkailan ana so a raba ta da shi, hanya Sa'eed ya bata ta wuce ciki ganin ya tsare ta da ido, ya na so ya ji me ya kawo ta da sassafe, sai ta wayance ta ce,
"Ina kwana Aunty Sumayya? Dama zuwa na yi in ji ci gaban labarin ki, gaskiya jiya da kyar muka yi bacci, saboda tausayin ki, gashi ina so ki yi ki gama bamu labarin, ko zan fahimci darasin da ke ciki, kuma a gaggauta zuwa ba wa su Munkaila hakuri,"
Murmushi Sumayya ta yi, sannan ta ce,
" Kar ki damu, yau gaba dayan mu a nan za mu karya, kar ku yi girki, Abban Ludhfi kan shi ya ce ba zai je ko ina ba sai sanda ya ji qarshen labarin nan, dan haka kar ki damu, ki je inna gama zan kira ki"
A zabure Ihsan ta ce,
"Ahh ahh.. Zan taya ki aikin, dan a yi saurin gama wa,"
Kallon ta suka yi dika, ta hau yaqe, cikin zuciyar ta kuwa kamar ta fasa ihu, ita har yanzu bata ga me ya hada labarin Sumayyah da soyayyar ta da Munkaila ba, gashi jiya ko kiran ta night call be ba, wace iriyar mummunar qaddara ce ke son fada wa soyayyar su ne?
Ta na nan zaune su Sumayyah suka idar da karatun su, suka yi addu'a suka shafa, Sa'eed ya shige daki, Sumayyah ta kalli Ihsan ta ce,
"To bismillah, mu fara da fere dankali ko?"
Ran Ihsan a bace, ta wuce gaba, dan ba abinda ya kawo ta ba kenan, uban dankalin da ta ga Sumayyah na lodo wa shi ya fi bata haushi, wato ga jaka ko? Kwafa ta yi, ta hau fira, Sumayyah kuma ta dora farfesun naman ragon da ya sha kayan qamshi da albasa, ta dora ruwan shayi mai cike da kayan qamshi, sannan ta yi readyn mai da duk wani abu da za ta buqata wajen suyar dankali, sai ta zauna su ka ci gaba da fere dankalin tare, Ihsan sai tsaki take, Sumayyah kuwa sai murmushi take.
A haka suka kammala aikin su tsaf, zuwa tara da minti sha biyu na safe, 9:12am, kowa ya hallara, abinci kawai ake ci, ana santi, kallon Mahwish Sumayyah ta yi, ta ce,
"Ga wadda ta koya min nan, ni in banda abincin gargajiya ban iya irin wadannan ba sosai,"
"Habaa ai yanzu kin fi ni iya wasu abubuwan ma"
"Kin dai fada dan ki ji dad'in bakin ki ne hajiya ta"
Murmushi suka yi, Sa'eed kuwa sai ya ji farin ciki ya lullibe shi, yana jin dad'i in ya ga suna wasa da dariya irin haka.
Ihsan ce ta fara tattare kwanunan, sannan ta ce,
"To Sumayyah ke muke sauraro"
"Ohhh Ihsan, yau in ban kammala labarin nan ba, ina jin sai kin yi tsalle kin fada zuciya ta kin ga qarshen shi"
Dariya aka sanya a wajen banda Zaituna, ta matsu ta ji ci gaban labarin, amma wani girman kai ke damun ta, bata so ta yi magana, Sumayyah ce ta gyara zama sannan ta ce,
![](https://img.wattpad.com/cover/292798077-288-k314670.jpg)
ESTÁS LEYENDO
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........