MAHWISH PAGE 21

56 3 0
                                    

*KI NA BUQATAR TSAHON, GASHI?LAUSHIN GASHI? KI NA DA AMOSALI AKAN KI DA YAKE HANA GASHIN KI TSAWO? KI NA FAMA DA KARYEWAR GASHI? HANZARTA KI SAI HAMIBRAH HAIR CREAM AND OIL*

*HAMIBRAH HAIR CREAM ₦1800 NE KACAL, HAMIBRAH HAIR OIL QARAMIN ROBA ₦1200, BABBAR ROBA ₦1800*

*ANA SAMU A GARIN KANO DA DUK INDA AKE BUQATA INSHAA ALLAH* *HANZARTA KI NEMI NAKI AUNTY GUIDEES (GUIDA YARA)* 💃🏻💃🏻❤️💖

*Dan neman qarin bayani kira ko ku aika saqo a wannan lambar*

*09031416423*

Tun kafin ya isa gida ya kira ya sanar da Mahwish abinda Aunty Zaituna ta basu, murna ta dinga yi, ta na masa fatan koma wa lafiya, su na gama wayar ta kira Hajiyan ta, ta sanar da ita, Hajiya shiru ta yi, sannan ta ce,

"A gaskiya hankali na be kwanta da wannan naman ba, tunda tunda ku ka yi aure bata taɓa zuwa ko da sau d'aya ba a gaisa, balle wata kyauta ta gilma a tsakanin ku, mene ne na bashi nama kuma? A gaskiya duk hanyar da za ki bi, ki bi, kar ki ci naman nan"

"Ni ma abinda ya sa na neme ki kenan, ji nake gaba na na fad'uwa ,tsoro na shiga ta Hajiya"

Hawaye ne suka fara zuba daga idanun Mahwish,

"Kar ki ji komai, na fad'a maki ki yawai ta fad'in Hasbiyallahu la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem, in ki na yawan faɗin haka, ba dai mutum da aljan ba sai dai Allah d'in kawai, duk abinda ki ka ga ya same ki duk da ki na karanta wannan,to fa Allah ya yi nufin ya jarabci imanin bawan shi ne, in ki ka shiga hali na jarabawar sai ka roqi Allah ya baka ikon cin jarabawar"

"To Hajiyan mu na gode, Allah ya qara girma"

Ta na kashe waya, Mahwish ta tashi ta sake gyara wa, ta shafe jikin ta da humrar HUMKAM da Kolaccar HUMKAM, ga gidan ta sai qamshin turaren wutan HUMKAM yake, qamshin da ya rikita su Hajiya Mama,dan kuwa ya kai musu ziyara, ba abinda suke da ya wuce zagin Mahwish, sun san ta ko ina daidai misali, bata bar qofar da ta gaza ba wajen kula da Sa'eed.

Hajiya Mama cikin fushi, ba tare da ta duba time ba, ta dauki waya ta miqa wa Ihsan ta ce,

"Kira min waccan aranni mu je bikin miji na baya fad'a, ta kama hanya ta tafi biki sai ka ce in bata nan waliyyan amarya da ango ba za su hallara ba,"

Kiran Tasneem sukai ta yi, ta na ringing ba a daga ba, nan kuwa ta na can, sun je dinner mota ta lalace musu a hanya wajen komawa gida, gashi dare yayi, masu gyaran mota ba ko d'aya, gashi da nisa tsakanin gidan su amarya da inda abun ya faru, sun yi dabarar tsaida abun hawa,adaidaita sahu guda d'aya aka samu, a guje 'yammatan suka cika shi, ya rage Tasneem da wasu 'yan mata biyu ne kawai, sai driver da abokin ango, Tasneem na ganin kiran ta qi d'aga wa ta hau masifar basu san a halin da take ciki ba za su dame ta da kira.

Ihsan gajiya ta yi ta ce,

"'yar mulkin bata ga damar d'agawa ba, ko ta yi bacci,sha d'aya da rabi fa yanzu"

"Allah ya kai mu gobe an kira ta"

Qarar bude gate da shigar Sa'eed gidan ce, ta sanya su Hajiya Mama leqen shi ta window, ya na fitowa su ka bi hannun shi da kallo, kwano suka gani, nan da nan farin ciki ya baibaye su, suka koma suka zauna, tare da jinjina wa Zaituna, sannan suka koma gode wa Allah da ya bata ikon fita a daidai lokacin da suka fi buqatar ta.

Sa'eed kuwa ya na fita daga mota qamshi ya daki hancin shi, sai ya ji wani irin kwanciyar hankali ta kama shi,zuciyar shi wasai kamar ba shi da wata damuwa a duniya.

Sai da ya rufe qofar su sannan ya shiga, labewa ta yi a labule, ya na yin gaba ta bi shi a baya ta na qunshe dariya, sai da ya ajiye kwanon a saman dinning zai shiga ciki ya kira ta, ya na juya wa suka had'u, ta yi mamaki da bai ji tsoro ba, kawai ta ga ya d'aga ta sama, ya na kissing din duk wata gab'a da ya samu, cikin wata iriyar murya ya ce,

MAHWISHNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ