MAHWISH PAGE 36

25 2 0
                                    


*Alhamdu lilLAAH, yau muke cika shekara sha biyu cif da aure, mu na barar addu'ar ku makaranta, Allah ya qara wa dukkan masu aure zaman lafiya a gidajen su, marasa aure Allah ya kawo mazaje na gari ameen*

Ihu Mahwish ta sanya, saboda wani irin azababben zafi da ta ke jin marar ta da qasan ta na yi mata,  a firgice Sa'eed ya sauka daga saman kujerar ya hau jijjiga ta, ya na tambayar ta ko lafiya? Da ganin yanayin ta, duk wanda ya kalla ya san ta na cikin azaba da rad'adin ciwo, ita kan ta ba za ta ce ga musabbabin jin wannan azabar ba, ta rasa inda za ta sanya kan ta, saboda zafin da take ji, Sa'eed ya gigice, cikin sauri ya sanya wandon shi, ya sanya mata rigar ta, ya dauke ta suka shiga bathroom, wanka ya so ya mata, ya wanke wajen amma ta qi bashi had'in kai, saboda azabar da wajen ke mata.

Tun Sa'eed na jure wa, shi ma sai ga hawaye, domin dukkan mai rai in ya ga halin da take ciki sai ya tausaya mata.

Su na nan tsaye har misalin sha biyu na dare, Mahwish na murqususu a cikin gidan, daga d'aki su koma parlour daga parlour a je bathroom, har d'akin da Ludhfi ke kwana sai da ta shiga, ta rasa ina za ta sanya ran ta dan azaba.

Da misalin d'aya na dare, duk ta gaji, ta galabaita, jikin ta ya sake, a haka ya samu, ya mata wanka, har da na tsarki, shima ya yi, ya kai ta d'aki ya kwantar, ta na jin zafin sama sama, har bacci mai dad'i ya d'auke ta.

Sa'eed na tsaye a kan ta, ta na sauke numfashi, tare da ajiyar zuciya, tunani yake ta yi, a game da dalilin da zai sa marar ta da gaban ta su dinga ciwo bayan ya gama saduwa da ita, ko dai ya na da nasaba da b'arin da ta yi ne?

"Bari da safe xan kai ta wajen Abubakar in ya dawo, wataqila Dr. Da ta duba ta bata iya aikin ta bane, in kuwa haka ne, sai na yi qarar ta kotu, ta na neman kashe min mata"

Kwanta wa ya yi a gefen ta, ya sumbaci goshin ta, ya ja ta jikin shi ya rungume, sake manne wa ta yi a jikin shi,tare da sauke ajiyar zuciya mai qarfi, ta ci gaba da baccin ta.

Can bangaren Tasneem kuwa, murna kamar ta yi yaya, maganin da ta binne ya yi aiki, ta na zaune cikin tsakiyar daren bayan ta gama lab'en jin su Mahwish ta hau kora fresh milk abun ta, ta d'ora qafa d'aya kan d'aya, ta na doka murmushi,

"Mahwish na tabbata wahalar da kika sha yau, ta ishe ki ishara gobe na tabbata ba za ki yi marmarin had'a shimfida da miji na ba, ba ke matar so ba? Zan ga qaryar soyayya daga sanda ki ka fara qin bashi had'in kai, zai juya maki baya, dan kuwa na san Sa'eed, ba ya iya kwana ba tare da ya yi sex ba ko wasannin da za su gamsar da shi, in ana jinya ta ya za a yi wasannin? shawarar Aunty Z ta yi, dole ne gobe na bata wannan dadd'an labarin"

Ta na gama zuqe madarar ta, ta miqe ta shige daki, ta haye gado, ba addu'a ba komai, ta kwanta kamar dabba.

Washegari da safe Sa'eed ya wa Mahwish wanka,sannan ya wa Ludhfi wanka suka shirya cikin shadda kala d'aya, ruwan zuma, ta yi masu matuqar kyau, sai baza qamshi suke mai sanyi, har a wannan lokacin marar Mahwish na ciwo, daure wa kawai take, sashen Hajiya Mama suka je, suka gaishe ta, ta amsa gaisuwar Sa'eed da Ludhfi da ke gwaranci , amma ta qi kula Mahwish, ta kaicin ganin ta cikin shaddar nan take, ji take kamar ta cire mata ta sa musu wuta su qone.

Mahwish ba yau ta fara fuskantar haka a wajen Hajiya Mama ba, dan kuwa kullum sai ta zo gaishe ta, ko da rana, ko da safe, amma in Hajiya Mama bata ga dama ba, ba za ta d'aga kai ta kalle ta ba ma, balle ta amsa ta.

Sa'eed na gama gaida Mahaifiyar shi, ya sa hannu a aljihu zai bata kudi, Mahwish na ganin haka ta kama ludhfi suka fita suka basu waje.

Budar bakin Hajiya Mama sai cewa ta yi,

"Tooo matar ka ta yi fushi za ka ba wa mahaifiyar ka kudi maza bita ka bata hakuri kar tai fushi,"

"Haba Hajiya Mama wanne irin fushi kuma, Mahwish da ki ke gani, ta sha nuna min yanda zan kyautata maku, ita 'yar da ki ke ji da ita sau nawa ina so na kyautata muku ta na hanawa? Hajiya Mama ya kamata ki fuskanci yanda yarinyar nan ke girmama ki, take son ki, jiya na ji gaba d'aya hirar ku, akan goyon bayan da su Tasneem suka samu suka je Lago...."

MAHWISHTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon