MAHWISH PAGE 17,

61 4 0
                                    

Sun isa Jakarta babban birnin Indonesiya lafiya, Mahwish ta kashe kwarkwatar idanun ta kafin su isa babban katafaren hotel din da ya kama musu mai suna, four seasons hotel, waje ne mai matuqar kyau, Mahwish da ko Kano bata jin ta tab'a bari, sai ga ta a wata qasar ta na ta washe baki,Sa'eed kuwa sai dariya yake mata, ko a jikin ta.

Su na isa d'akin da za su zauna, ta kama baki ta na dariya, daga baya ta yi wurgi da qaramar Jakar ta ta d'iba da gudu, ta haye gadon ta na tsallen murna,Sa'eed kama qugu kawai ya yi ya na  kallon ta, ba zai iya jure yarintar ta ba, dan haka zuwa ya yi, ya dauke ta a ka ya yi bathroom da ita.

Gudun kar a ce na cika sa ayis da yawa ne ya sa na tsaya a waje ina jiran fitowar su, dariya da qarar Mahwish kad'ai ta isa ta sanar da ni irin soyayyar da ake sha a ciki.

Sun jima sosai kafin su fito kowannen su d'aure da bathrobe, Mahwish ta daure kan ta da qaramin towel ,sai tura baki take, ta na tafiyar shagwababbu, shi kuma ya na mata dariya,

"Allah Yah Sa'eed Sam baka da hakuri, kuma wayon ka yawa ne da shi,Indai haka ne ake gane so to bana son ka"

Duk da ya san da wasa ta fad'a,amma sai kalmar bata masa dad'i ba, ita kuwa ko a jikin ta, ta tabbata ba har ran ta ta fada ba, a gaskiya ba zata iya cewa kai tsaye ta na son shi ba, amma kuma babu tsana ko qin shi sam a ran ta.

Kwankwasa qofa akai, room service, abinci ne na halal masu rai da lafiya aka kawo musu, Mahwish ba kunya, haka ta zage ta ci ta qoshi ta yi nak, bayan sun kammala suka je suka wanke baki, suka dawo,Sa'eed ne ya fara shirin fita, cikin sauri, dan fara gabatar da abinda ya kawo shi, gani ta yi dare ya fara shiga, me zai hana ya  huta gobe ya fita? Hakuri ya bata ya lallaba ta, ya sanar da ita cewa, duk abinda ya zo yi a tsare yake, ya na da kyau ya je ya kammala komai, sauran kwana biyar d'in sai su shaqata kafin su koma, kwana biyu zai yana siye da aika kayan shi Nigeria,sauran kwanakin kuma ya mata wani babban tanadin da sai ta yi farin ciki sosai.

Wayar ta ya had'a mata yanda za ta yi chatting ta kira mutanen gida a gaisa, ya na gamawa ya sumbaci bakin ta, da ta ki maida wa, saboda shagwaba, ya fita ya na cewa,

"I love u Mahwish"

Daga masa kai kawai ta yi, ta masa murmushi, cikin d'an sarewar guiwa ya fita, ya na tafiya ya shaqi iska ya furzar cikin ran shi ya ce,

'Sannu ba ta hana zuwa Sa'eed, sai dai a jima ba a je ba, watarana za ta mayar maka da martanin soyayyar ka'

Taxi ya hau ya wuce inda za shi, cikin sauri.

Mahwish kuwa tana hawa WhatsApp ta hau bawa Xulaihah labari, tun daga tasowar su, da zaman ta a jirgi, da isar su qasar, da duk wani abu da ta gani a hanya, har dakin da suka sauka sai da ta bata labarin shi, qarshe ma sai ta tashi ta dinga daukar hotuna da videos tana tura mata, bata bari ba sai da ta ji ta gaji liqis sannan ta ajiye.

Duba time ta yi, ta ga lokacin isha'i ya yi, nan da nan ta ji wata kasala ta kama ta, kamar yanda take ji a baya, a duk sanda lokacin sallah ya yi, tuna wa ta yi da nasihar da Sa'eed ke yi mata kullum akan sallah, juyawa ta yi hannun ta na dama da hagu ta yi a'uziyya ta tofa,tare da miqe wa ta samu kaya ta sanya a jikin ta, ta yi alwala ta tada Sallah.

Ta na idarwa ta rage hasken fitilar dakin ta rage AC, ta haye gado, sai bacci.

Cikin baccin ta take mafarkin ta je Saudiya, ta na d'awafi, dan ita a duniya ba qasar da take son zuwa sama da Makka,  sai Dubai, itama dan ta ji ana zancen kyawun qasar ne.

Har ya dawo ya yi shirin bacci duk bata san ya dawo ba, shigewa ya yi bargon shima tare da yin addu'ar bacci ya kwanta, ya na kwanciya ta mirgina jikin shi ta lafe kamar ta samu katifa, shi kuwa cikin murmushi ya sumbaci goshin ta, ya rungume ta.

MAHWISHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora