Watanni bakwai kenan da zuwan Sumayyah gidan, ba abinda bata gama gane wa ba na daga halayyar mutanen gidan, ba kuma abinda bata sani ba, da dalilin da ya sa aka auro ta a gidan, shi kan shi mijin nasu ta gama gane shi, ya ba wa Mahwish babban kaso mai tsoka a cikin zuciyar shi,Dan haka ba kishi take da hakan ba,duk da cewa ta fara jin son shi a ran ta, ta san in ma ta yi kishin wahala za ta sha, mutuncin ta da Sa'eed da Mahwish suke gani xai zube,kuma ta riga ta san dama dole haka za ta kasance, ta shirya wa hakan.
A cikin watanin nan Mahwish ta samu ciki, mai laulayi sosai fiye da sauran cikin da take samu, wata daya da sati biyu kenan da gane ta na dauke da cikin, Sumayyah na iya qoqarin ta dan ganin ta sauqaqa wa Mahwish ayyuka a bayan idon Hajiya mama, bayan Hajiya Mama bata damu da duk wanda zai gan ta tana taimaka wa Mahwish ba, Hajiya Mama ta yarda da ita sosai ta yanda ko Zaituna ce ta ce mata Sumayyah ta yi abu, ba yarda take ba, Mahwish kuwa na jin dad'in yanda Sumayyah ke kula da ita, amma ta na mamakin yanda take nuna mata halin ko in kula a gaban Hajiya Mama, tsananin kishi take nuna mata a gaban Hajiya Mama, ta na so ta tambayi dalili, amma ta kasa, hakan kuwa na da nasaba da yanda Sumayyah ke tafi da ita ta Mahwish din, yau ma kamar sauran kwanakin da suka gabata.
Sumayyah ce zaune ta na tsinke zogale a sashen Mahwish, dambu Mahwish ta ce ta na sha'awa, wanda ya ji gyada, Sumayya kuwa ta kware a irin girke girken nan na gargajiya,dambu na can saman gas ya na dahuwa su kuma su na parlour su na hira, cikin jin dad'in hirar Mahwish ta ce,
"Nikam dan Allah in tambaye ki, me ya sa jiya Hajiya Mama ta aiko a bata farfesun naman da mukai ki ka ce ya qare, bayan akwai, dan na je daukan attaruhu zan dafa indomie na ga kin juye ragowar a mazubi kin aje,"
"Mahwish kenan, na ga alama ke har yanzu baki san kalar mutanen da ki ke tare da su ba shekara da shekaru ko? Ko dake na tabbata kin sani, kawai dai halin mu ne ya banbanta, ni bana daukar rainin hankali, kuma na tsani shegen roqo da kwadayin tsiya, da muka dafa ba an kai musu ba? Mene ne na sake aiko wa? "
Shiru Mahwish ta yi, a zuciyar ta tana saqa abubuwa da dama, a zahiri kuwa bin Sumayyah kawai take da idanu.
Sumayyah ce ta shiga kitchen dan wanke ganyen, ta na shiga Ihsan na shiga,
" Ke Mahwish wai kin manta Hajiya Mama ta ce yau da safe tana so ki daka mata sakwara?"
Daga kitchen Ihsan ta jiyo muryar Sumayyah ta na bata amsa..
"Ko ni da nake lafiya qlou ba zan yi dakan sakwara da safe ba, balle ita da take laulayi, so ku ke cikin ya samu matsala ko me? Ku jira in za ku iya, in na gama dambu na sammaku, tunda ku kun zama taron tsintsiya ba shara, uwar taku ma ba za ku bauta mata ba, ta huce takaicin haihuwa, tirrr da halin ku"
Ba qaramin sandarewa Mahwish da Ihsan suka yi ba, kalaman Sumayyah sun daki kunnuwan su da kyau, ta yanda suka sanya Mahwish tashi xaune ta kalli hanyar kitchen, tsaye ta ga sumayya ta na bin Ihsan da wani mugun kallo.
Ihsan gaba daya bakin rashin kunyar ta ya mutu, ta kasa cewa kanzil, sai baki da ta tura ta na maganganu qasa qasa, fita ta yi cikin sauri kamar wadda ake tura wa.
"Sumayyah kin san me ki ka yi kuwa? Kin san me ki ke fada kuwa?"
Iska ta shaqa, ta lumshe ido sannan ta kalli kitchen ta ce,
"Dambu na ya yi, kin jiyo qamshi ko? Bari na zubo maki maman biyu, ina zuwa"
Baki Mahwish ta saake sake wa a karo na ba adadi, ya tana mata maganar hatsarin abinda ta aikata, amma ita ta na maganar dambu ya yi? Nan da nan wahalar da ta sha a hannun su Hajiya mama ta dinga gilma mata a idanun ta, jikin ta ne ya hau rawa, idanun ta suka kada suka yi jawur, a cikin wannan yanayin Sumayyah ta same ta,
"Subhanallah me ya same ki? Mahwish mene ne?
Fashewa Mahwish ta yi da kuka sannan ta ce,
"Baki da masaniyar kalaman ki me zai janyo mana, ko kuma na ce me zai janyo min, domin duk wannan abubuwan da suke faruwa hatta da auren ki an yi shi ne dan jawo min matsala, kin kuwa san irin uqubar da na sha a gidan nan? Kin kuwa san rayuwar da nake fuskanta kafin zuwan ki? Dan Allah na roqe ki ki xauna lafiya da kowa, bana so laifi na ya shafe ki, kin ga dai Hajiya Mama na son ki, kar ki bari ki xama maqiyyiyar ta, baki san abinda za su iya aikata maki ba, a da na yi taurin kai, na yi rashin ji amma zama na da mutanen nan sai da na koyi nutsuwar dole, sun cutar da ni, sun cutar da mu baki daya, ni, miji na da d'a na, dan Allah sumayyah... "
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........