MAHWISH PAGE 15

40 4 0
                                    


Washegari da safe Mahwish bata tashi ba sai da Sa'eed ya tada ta kafin ya wuce masallaci, amma bata tashi a lokacin ba sai da ta sake komawa, ta ji dad'in baccin nan sosai, asali dama ita mai son jiki ce, jiyan ta samu yanda take so, kusan gaba d'ayan ta a jikin shi ta kwana, a zato na zan gan shi a gajiye, ya na mitar ta daddane shi, sai na ga annuri da nishad'i tare da wata iriyar fara'ar da ban tab'a gani ba a fuskar Sa'eed, burin shi ya cika, ga shi, ga Mahwish, ba qiyayya, ba fad'a, ba zagi, sai aminci da yarda da juna, fatan shi soyayya ta wanzu a tsakanin mai qarfi kuma mai tsafta  watarana.

Ta idar da Sallah cikin sauri da hanzari, hakan kuwa ya yi matuqar daukan hankalin Sa'eed, har ya kasa hakuri sai da ya mata magana,

"Babe me na ga kin yi yanzu? Ba dai har kin idar da Sallah ba?"

Cikin dan had'e gira da mamakin tambayar shi ta na ninke carpet din sallah ta ce,

"Uhumm why? Baka ga sanda na yi sallah bane?"

"Nooo na gani, kawai gani na yi kin yi ta a gaggauce, kamar ba ki qarasa karatun sallah ba"

Kama qugu ta yi ta ce,

"Ka ga kar ka sa wa sallah ta ido za mu b'ata, ko a gida ma haka nake abata,su Hajiya ma wai haka suke cewa kamar ina daukan wuta, nan da nan na idar to me zan tsaya yi?"

Kad'a kai ya yi, ya ce,

"Zo ki ji me ake tsaya wa yi, ina dai abinda ake tsaya wa yi ne baki sani ba?"

Daga kai ta yi, ta na ture turen baki, Sa'eed danne zuciyar shi kawai ya yi bai sumbaci bakin ba, ita gani take ko ta na rashin kunya ne in ta yi hakan oho? Amma bata san irin kyawun da hakan ke mata ba, zama ta yi a gefen shi, shi kuma ya ja ta jikin shi sosai ya kwantar da ita, ta yanda zai zama ta na a tsakanin qafar shi, a kunne yake mata magana kamar me rad'a,

"Mahwish sallah babban ginshiqi ne a cikin addinin Islama, sallah d'aya ce daga cikin abubuwan da aka wajabta wa dukkan Musulmi, wanda ya yi ta da kyautatawa ya tsira, wanda ya ke wulaqanta sallah azabar Allah zata tabbata akan shi,Mahwish ki sani, in mutum na yin Sallah, ya na hira ne tsakanin shi da mahaliccin shi, kin kuwa san hira da Allah tafi hira da Salim, ko Sa'eed, ko Abba, ko Hajiya ko Xulaihah,ko sarki ko gwamna, hira da Allah lada ne da ita da sanya nutsuwa da kwanciyar hankali, me ya sa za ki ga muminai da suka yarda Allah shi ne Ubangijin su, kuma sun maida Allah shi ne babban abin dogaron su, in damuwa ta dame su sai su yi sallah? Ai in dai za ki nutsu ki na sallah ki na tadabburin ayoyin da ki ke karantawa to saboda dad'in sallahr ba za ki so ki dena ba,Sallah fa ita ce farkon abinda za a fara tambayar mutum a lahira, in sallah ta yi kyau, mutum ya taimaki kan shi da tonon asirin lahira,amma in bata yi kyau ba, mutum na yin ta kamar mai daukan wuta, ko caccaken kurciya to fa tabbas zai ja wa kan shi binnciken manya da qananan laifukan shi, dan haka dan Allah Sweetheart ki gyara kin ji? Na ji labarin kin sauke qur'ani ke da Xulaihah, to me zai sa ki dinga yin Sallah kamar ba ki san me Allah ya ce game da ita ba? Kuma ki sani, shi jinkirta sallah har lokacin ta ya fita, ko ya gota, shi ma babban laifi ne mai zaman kan shi, wanda a cikin qur'ani Allah ya bayyana mana wuta duk wani mai wulaqanta lokacin sallah zai tafi, subhanallah, Allah ya kiyaye mu, kin ga na tashe ki, ki je sallah, har na je na dawo baki ba, kuma ki na fara wa kamar ki na sauri zaki wani abu da ya fi sallar mahimmanci, har kin idar, to me ne ne a duniya da ya fi hira da mahalicci dad'i? Ai ko mene ne ya jira ya kuma tsaya a bayan sallah ko?"

Lafewa ta yi sosai a jikin shi, kalaman shi sun shige ta sosai, cikin zuci da labb'an ta take furta istighfar, tabbas ashe ta na tafka babban kuskure, iyayen ta sun jima su na mata fad'a akan wulakanta sallah, amma ba wanda ya tab'a mata bayani irin wannan, ta gamsu matuqa, ta kuma fuskanci dole ne ta gyara, godiya ta masa da alaqawarin za ta gyara.

Sa'eed na so ya karb'i haqqin shi ba ya so ya takura mata,ya fi so har ta dawo da kan ta ta ji ta na son abun ita ma, amma ya zai yi da matsananciyar buqatar ta da yake? Cikin dabara ya daga ta daga jikin shi, zai bar wajen, ta kama hannun shi, kan ta a qasa ta ce,

MAHWISHDove le storie prendono vita. Scoprilo ora