*MAHWISH PART 2*
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 11:
"A bakin qofa muka hadu da shi, ya na bi na da wani irin mugun kallo, ba tare da na kula shi ba na sauke kayan abinci na, na shige gidan, ya d'an jima kafin ya biyo ni ciki, ya na shigo wa na bude baki dan yi masa sannu da zuwa, ya d'aga hannu ya dakatar da ni, sannan cikin fushi ya ce, "
'Daga ina ki ke?'
" Cike da jin tsoron me zai je ya zo na ce"
'Daga gidan Yaya Babba nake, ta ce ma ta na gaishe...'
'Ohh wato ba ki jin magana ko? Da na hana ki fitar sai da ki ka fita ko? Kin je ki na tona asirin gida na, ban ce kar ki fita ko qwar gida ba?'
"Zuciya ta ta fara hasala, akan me zai ce ba zan fita ko qofar gida ba? Bayan be bar ni da komai na ci ba, mutuwa yake so na yi?"
' Kar ka manta baka bar min komai ba na ci, to ta ya zan rayu tunda ni ba dutse bace? '
' Au ni ki ke mayar wa da magana? Da kyau'
" Cikin fushi ya fita ya bar min gidan, ni kuwa nan take na hada murhu na dora girkin sahur, a haka muka rayu na tsahon sati guda baya min magana, ba ya kula ni, baya kowacce mu'amala da ni, shi a dole fushi yake da ni, ga abinci ya sake qare wa, dan ma bana almubazzaranci ina tattalawa tunda na san banda shi, bawan Allahn nan haka zai dawo a qoshe, ina zaune ba ci ba sha, balle sutura, ko sauke haqqin aure, na gaji matuqa, yunwa ba abokiyar wasan kowa bace, washegari da na tashi gidan mu na nufa direct, na tarar da Umman mu kwance a tabarma ta na shan iska, qanwa ta na fere dankalin shan ruwan azumi, qani na na wanke bayi, gaba dayan su ba wanda ya gane ni a cikin su, sai Umma na, a ranar na tabbatar da cewa Uwa ta daban ce, qanne na haka suka dinga xubar da hawaye, Umman mu mace ce mai dauriya, amma sai da kwalla ta taru idanun ta, ta kama ni muka zauna, ta ce,"
'Sumayyah? Me ya same ki? Shin jinya ki ka yi ne?'
" Kuka na fashe da shi, sai da na yi ya ishe ni, sannan na ce, "
'Umma tun farkon auren nan da na ce maki miji na mai kulle ne, ku ka dauke qafafun ku a gidan, ni ma ba bari na zuwa yake ba, wanan shi ne dalilin da ya sa baku san irin azabar da' yar ku take sha ba, yau ma na ji zan rasu ne in ban zo na nemi taimako ba, shi ne dalilin zuwa na'
"Nan na kwashe komai na fada wa Umma na, hawaye ne ya ke zuba a idon ta kamar an bude famfo, ta kalle ni cikin tausayawa da so da qauna irin na iyaye, ta ce,"
'Wannan shi ne labarin da yayar ku ke ta kokonton fada min? Sai ta ce ta na da magana da ni sai ta fasa, Tabbas biri ya yi kama da mutum sak, abubuwan na daure min kai, ace unguwannin mu ba nisa ko ciwo muke aka fada maki baya bari ki zo gaishe mu, ni kuma ina hana su zuwa ne saboda kar mu ja maki matsala ke da mijin ki, dan wasu haka suke kulle gare su, a rai na watarana nakan ce mijin Sumayyah na son ta da yawa shi ya sa yake kishin ta, ashe azaba yake ta gana maki, ba komai ki bar wa Allah, za ki tafi da abinci, da ya qare xa a aiko maki da wani, ni dai fata na ku zauna lafiya, wataqila bashi da shi ne'
'Humm Umma kenan, ai maganar babu a wajen Bukar bata taso ba, saboda mutumin nan xuwa na ya fara kiwo daga rago da tunkiya yanzu har garken shanu yake da su, ko da madara da nono zan rayu, Allah ya sa wa dukiyar shi albarka ta yanda a kullum fadi yake ya na cewa ni ce abokiyar arziqin shi, gashi daga xuwa na arziqin shi ya habaka, dama an fada masa, ni abokiyar arziqin shi ce, in na tambaye shi wa ya fada masa sai ya yi shiru, kin ga kuwa ba talauci sai mugunta tsabar ta'
'Haka ne, kar ki damu, komai xai zo qarshe ne watarana da yardar Allah'
"A ranar na ga gata daidai irin na iyaye masu qarfi madaidaci irin nawa, an min sha tara na arziqi babana da kan shi ya maida ni gida, a hanya ya dinga min nasiha, ya na ban shawarwari masu matuqar amfani, godiya na masa bayan ya aje ni ya wuce, shiga na dinga yi da kayan, wanda ba zan iya ba na sa aka shigar min, da bawan Allahn nan ya dawo ya ga abinci, sai ya sake daukan fushi da ni, in ya sa kai ya fita sai ya kai qarfe daya, biyu, watarana har uku na dare, a ya dawo da wuri ne ma zai kai sha biyu, na dare,da sallah daga gidan mu aka min kayan sallah, hatta da takalmin da zan saka da jaka, hakan sai ya sake hasala shi, sai ya zamana ni dai gani nan ne kamar hoto, dan kuwa ba haqqin aure na da yake sauke wa, abun har yana ban mamaki, a yanda yake da tsananin buqata, ace yau sai yayi watanni be kusance ni ba, watarana in ya dawo daga yawon shi, sai in ga ya shiga bayi, ya wanko gaban shi da sabulu ko detol, ya zo ya nemi waje ya baje kamar jakin da yayi aiki ya gaji, sai kuma safiya"
ŞİMDİ OKUDUĞUN
MAHWISH
RomantizmQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........