Hankalin su gaba daya ya tashi banda Tasneem da ke fatan Allah ya sa kar ya tashi, ya wuce daga suman da ya yi, tunda ya sake ta, sakin da zai wahala ta sake koma wa rayuwa da shi, to da wata ta more shi, gwanda kowa ya rasa.
Hankalin Hajiya mama ya yi mugun tashi, dan kuwa duk tashin hankalin da suke saka Sa'eed ciki be taba haka ba, Zaituna da Ihsan kuwa kuka kawai suke, Abubakar ne tsaye akan komai, sai shige da fice yake, ran shi a matuqar bace, dan kuwa ya tabbata koma me ya sami abokin shi, laifin dangin shi ne, kwata kwata baya qaunar bude ido ya ga Hajiya mama da tawagar ta a wajen, dan haka ya na koma wa dakin da aka kwantar da Sa'eed ya aika wata Nurse ta ce kowa ya bar wajen, su na damun marasa lafiya da hayaniya.
Saqo na isa kunnen su Hajiya mama Zaituna da Ihsan da Tasneem suka bar wajen, Hajiya mama kuwa ashar ta buga, ta ce,
"Na ga dan abu ta kazar uban da ze matsar da ni daga nan ba hayaniya ba, kasuwa ake ci a nan din, dalla malama matsa min daga nan ki na tafe kamar an tsoma kaza a ruwan zafi,"
Ran Nurse din nan a matuqar bace ta kama hanya za ta bar wajen, Hajiya Mama ta tare ta, ta na wani washe baki,
"Baiwar Allah na ce ba, uhmmm ya me jikin? In ce dai ya farfado?"
"Ta ya kazar da aka tsoma a ruwan zafi zata yi hankalin sanin abinda ke faruwa a duniya? Mtsww" Nurse din ta Fada wa Hajiya Mama cike da rashin kunya.
Tafiyar ta ta yi ta bar Hajiya Mama na rashin mutunci da zagin ta, ta na shiga za ta yi wa Abubakar bayani, ya daga mata hannu kawai, ya san taurin kai irin na Hajiya Mama, baya buqatar sake jin wani bacin ran, ga abokin shi nan kwance, stress ne ya masa yawa, gaf yake da kamuwa da hawan jini, saboda jinin shi ya wuce qa'idar da ya kamata a same shi.
Sun samu ya farfado, amma har a wannan lokacin ya kasa bude idanun shi, maganganun Hajiya Mama ke masa yawo a zuciya, wannan wace irin uwa ce mara son farin cikin d'an ta?
'Sa'eed kamar yanda ka sakar min Tasneem, to fa dole ka saki waccan me kama da yaran aljanun wato Mashawi, na baka daga yau zuwa gobe, ka sake ta, ko in tsine maka, ka ji na rantse ba zan sauya magana ta ba, ka kuma san hali na in na ce zan yi abu, se na yi, ba uban da ya isa ya sauya min magana ta, ka sake ta ka auri wata, tunda ka qi auren wadda na zaba ma da fari, akwai wata na samo maka, 'yammata gasu nan da yawa a gari, in hudu ka ke so a rana daya zan iya sama maka su, ka ji na fada maka kuma....'
Tunda ya saurari wadannan munanan kalami nata hankalin shi ya bar jikin shi, bai san me take ci gaba da fadi ba, taya ma za ta ce za ta tsine masa in be saki macen da ke bashi farin ciki ba? Macen da ta sadaukar da duk wani farin cikin ta dan ta zauna da shi, macen da ta sha matuqar wahalar rayuwa duk ta dalilin su, mace mai matuqar son shi kamar MAHWISH uwar dan shi, a bar so da qaunar shi, macen da ya tabbata har abada ba zai samu kamar ta ba, a gaskiya in dai Hajiya Mama ta dage akan sai ya saki MAHWISH tabbas ya san qarshen numfashin shi ne ya zo a duniya, yanzu meye abun yi? Wasu siraran hawaye ne suka zuba masa masu mugun zafi, wannan wace iriyar rayuwa yake ciki?
'Ya Allah ka kawo min agaji, Allah kar ka raba ni da MAHWISH sai dai in ka san Hakan shi ne zai fiye min alkhairi a rayuwa ta, Allah ka bani nutsuwa da kwanciyar hankali'
Addu'ar da yake ta yi kenan cikin ran shi, Abubakar ya shiga, a hankali ya bude idanun shi, ya kalle shi, ji yayi zuciyar shi ta gama yin rauni, ya na buqatar koka wa sosai, cikin wani irin mawuyacin hali yake bayyana wa Abubakar abinda ya faru, Abubakar kan shi ya ji tashin hankali bayan gama sauraron abokin na shi, wannan wace iriyar uwa ce da bata qaunar farin cikin dan ta?
"ina zuwa"
Cikin sauri ya fita, ya rufe qofar, Hajiya Mama na ganin shi ta sha gaban shi har da tara hannayen ta dika biyun.
![](https://img.wattpad.com/cover/292798077-288-k314670.jpg)
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........