Har ya isa office bai dai na tunanin abinda ya faru ba, shin me Hajiya Mama ta ce ma? Wanne umarni ta bashi? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wannan umarnin daidai yake da mutumin da ke tsananin buqatar iska ko haske a rayuwar shi, amma a datse musu ita, wannan umarnin daidai yake da wanda ke cikin sahara, ya na jin tsananin qishi a kawo masa ruwa mai sanyi, amma a tsiyyar da shi a qasa, kuma a gaban idanun shi, me ya yi wa Hajiya Mama haka da zafi da take so ta datse masa farin cikin shi? Ta sanya shi rayuwa kamar tsayayyen matacce? Shiru ya yi, a lokacin da ya zauna a kujera a office din shi da ke cikin babban super market din na shi, hannayen shi biyu ya dora akan shi da ke tsananin sara masa,shin ya zai yi? Kafin wani tunanin ya zo masa wayar shi ta yi qara, alamar saqo ya shiga, ya na duba wa ya ga sunan Mahwish kamar haka,"Baby Na"
A hankali wasu siraran hawaye ke bin kuncin shi a lokacin da ya gama karanta saqon ta, saqo ne mai cike da kalaman so, da tsantsar qauna, da kuma kulawa, saqo ne da kullum suka saba yi wa junan su, har sai ya koma gida, kowa zai ta bayyana abinda yake ji game da d'an uwan shi,kuma kowa zai ta yabon d'an uwan shi, kalamai na tsantsar kusancin da ke tsakanin su ne za su yi ta yi, har sai in zai wani aiki, ko in ya na komawa gida sai su bari, to yau me zai tura mata?
Wayar shi ce ta yi qara, cikin zumud'i ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga, zai amsa, a zaton shi Mahwish ce, ta ga jinkirin shi bai mata reply ba.
"Aunty Zaituna"
Shi ne sunan da ya bayyana a jikin wayar, ya na d'agawa ya ji Muryar Hajiya Mama, na masa tuni, akan sakin Mahwish da ta saka shi,
"Hajiya Mama ko zan iya sanin laifin da ta yi da ku ke so na rabu da mace mai biyayya kamar Mahwish, matar da na....."
'Sa'eed na fahimce ka yanzu, sakin ta ne ba za ka yi ba, to bari na tsine maka in yaso kun had'u a yawon duniya, a lokacin da ka bi duniyar da yawon tsince tsince, Sa'eed Allah ya...."
Cike da tashin hankali ya miqe tsaye, ya na gunjin kuka a cikin office d'in shi, inda mutuncin shi da dukiyar shi take, ya ce,
"Hajiya Mama na sake ta, dan Allah kar ki qarasa, kar ki tsine min rayuwa ta ta shiga musiba, Hajiya Mama, dan Allah ina roqon ki in wani laifi na maki, ko Mahwish ta maki ki ka tsane mu haka ki yafe mana, dan girman Allah"
Sa'eed na ta magana bayan ya gama furta wa Hajiya Mama ya saki Mahwish, ta kashe wayar ta, ba tare da ta tsaya ma jin me yake fada ba, su ka hau murna ita da yaran ta.
Message ya gani daga wayar Aunty Zaituna, an ce ya kira Mahwish ya sanar da ita sakin, yanzu yanzun nan.
Kukan shi ne ya qaru, zama ya yi, a kujera, ga AC amma ji yake kamar ana hura masa wuta dan zafi.
Mahwish na can na hira da Xulaihah, su na ta audio chats, su na hira abun su, su na ta dariya, cike da nishad'i, gefe d'aya ta na girki, mai dad'i da qamshi, duk gidan ya dauka da qamshin girkin ta, dan kuwa ya ce da wuri zai dawo.
Ludhfi ne ke ta mata gwaranci da wayar Xulaihah ta na dariya,bayan ta gama girkin, sai ta juye pepper soup da ta yi a qarshe a mazubi mai kyau, ta jera abinci a dinning, sannan ta gyara kitchen din ta tsaf, ta fita dan zuwa wanka.
Ta na kammala wanka, ta yi shiri cikin qananan kaya masu d'aukan hankali, sannan ta saka tauraruka masu sanyin qamshi, bakin nan sai zuba qamshi yake, wayar ta ta d'auka ta kwanta a kujera dan ci gaba da Chatting da Xulaihah, sai ta ga saqon Sa'eed ya shiga, murmushi ta yi, sannan ta tura baki, kamar ya na ganin ta ta ce,
"Na yi fushi, yau sai yanzu ake amsa min saqo ba koma, za ka dawo ne zan ra...."
Maganar ta ta tsaya cak, a daidai lokacin da ta karanta, saqo kamar haka,
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........