Karo suka yi da Goggo Zulai za ta fita ,a gigice ta hau masa bayani, shi kuma ya zaro waya ya sanar da Abubakar, Abukar ya ce su gaggauta kai ta asibiti, kashe wayar ya yi, ya hau neman key d'in mota, dan Goggo Zulai bata san inda yake ba, ita kuma ta suma.
Da kyar ya gan shi, ya dauke ta, ya fita da ita, Hajiya Mama na hango su ta nufe su, da gudu, zata tsaya masa surutu ya ja mota, ya ce,
"Hajiya Mama ki shiga mu je, ko ki jira ni na kai ta asibiti na dawo,yanzu ba lokacin tambayar na dawo lafiya bane,"
Tasneem ce ta taho kawai ta fada motar ba tare da ta wa kowa magana ba, bashi da lokacin magana da kowa yanzu, ta matar shi yake.
Su na zuwa kuwa suka tarar da Abubakar da midwifes biyu a bakin qofar asibiti, da gado, akai aka dora ta, aka shige da ita, Sa'eed ya na ta kai kawo, wani abu yake ji, ya tokare masa qirjin shi da maqoshin shi, garin yaya aka bar Mahwish a wannan halin ? Da bai zo ba fa?
Dr. Abubakar da midwifes din nan su na can su na iya bakin qoqarin su, sun samu ta farfaɗo, sun mata duk wani abu da ya dace, sun daidaita babyn ta yanda za ta haife shi/ta ba tare da matsala ba, sannan suka ci gaba da taimaka mata, dan ganin ta haihu lafiya.
Ta kusan awa biyu ta na naquda, kafin daga baya Allah ya bata iko, ta haifi yaron ta qatoto namiji,yaro kyakkyawa mai kama da iyayen shi, Dr. Abubakar da ya kalle shi, sai ya ji qaunar yaron ta shiga zuciyar shi, cikin farin ciki ya bar dakin ya fita, Sa'eed na ganin shi ya nufe shi, murmushin da ya gani a fuskar Abubakar kawai ya wadatar da shi sanin an samu nasarar haihuwa, amma ya na so ya ji, ya Mahwish da jaririn suke?
"Dr. Ya suke? Su na lafiya kuwa? Dan da gani babu tambaya ta sauka ko?"
"Kwarai da gaske aboki na, Allah ya sauke ta lafiya, mun samu namiji, da babyn da maman suna cikin qoshin lafiya."
Tasneem ji ta yi hawaye na zubar mata, Sa'eed kuwa hamdala ya dinga yi, ya nemi izinin shiga,
"No, please ka d'an jira a gyara su, na so ace ka shiga ka ga ya ake haihuwar ai, Dan maza a yanzu su na buqatar su na ganin ya matan su ke haihuwa , ko za su rage wasu abubuwan, kamar rashin mutunci, da ikon da suke wa matan akan yaran da su suka haifa da cikin su, amma kar ka damu, next time da kai za a shiga"
"Thanks man, ban san da me zan saka maka akan dukkan kulawar da ka ke bani da iyali na ba,Allah ya saka maka da alkhairi"
"Akwai abinda za ka bani, amma ba yanzu ba, in lokaci ya yi zan sanar da kai"
"Koh ? To Allah ya kai mu,i will be very much Happy to help you in any way aboki na"
"Na gode, yanzu za ka iya shiga, na ga ana mana magana, Uwar gida Bismillah, taso mu shiga ki ga d'an naku"
Cike da takaici, ta share hawayen ta a b'oye suka shiga,
"Masha Allah, Alhamdu lilLAAH"
Shi ne kawai abinda Sa'eed ke maimaita wa, ya na leqa fuskar jaririn bai san sanda ya durqusa qasa ya kafa goshin shi a qasa ba, ya hau sujjadar gode wa Allah, da wannan kyakkyawar kyauta da ya masa.
Allah ya bashi kud'i, ya bashi matar da yake so,ga kuma kyautar yaro, ba abinda zai ce wa Allah sai godiya.
Hannu Mahwish ta miqa masa bayan ya d'ago, da sauri ya isa ya kama hannun nata, ya sumbata, sau ba adadi, tare da yi mata sannu,
"Baby love, na gode, na gode, baki na ba san yanda zai jera kalaman godiya a gare ki ba, Allah ya albarkace ki, da abinda ki ka haifar mana, Allah ya sa ya zama mana sanyin idaniyar mu, Allah ya sa ya amfani Musulunci da Musulmai, ina son ki Mahwish, Tasneem zo, zo nan ki d'auki d'an ki kema, he is our son, babu bambanci a tsakanin mu, Allah ya masa albarka mu amfana da shi"
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........