MAHWISH PART 2 PAGE 19

40 2 1
                                    

*MAHWISH PART 2*

PAGE 19

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

"Grema a hankali ya tattare ba shi da wajen hira sai gidan mu, da ya dawo daga kasuwa sai ya wuce gidan mu ya sha hira sai dare zai dawo gida na, ko ya koma gidan d'ayar matar ta shi,tun abun baya ba kowa mamaki har ya dawo ya na ba mutanen gidan mu mamaki, da ya kula ana so a gano shi sai ya dauke qafar shi kamar ruwa, sai ya zamana ya koma damun khadeejah ta waya, ko ya ce yaushe za ta kai min ziyara ne, ita kuma takan ce masa ai kullum ma tana zuwa, kawai dai basa haduwa ne, se ya fita take zuwa, tun da ya ji haka sai Grema ya fara lattin fita kasuwa, watarana har sai Khadeejah ta zo ya gan ta sannan zai fita"

"Ana haka Grema ya gaji da bin gini sai ya yanke shawarar ya afka cikin gida kawai, ta waya ya tura wa Khadeejah saqo, ya sanar da ita shi fa son ta yake, ya za a yi? Cike da tashin hankali Khadeejah ta kira shi a waya, ta na tambayar shi shin abinda ta gani gaskiya ne? Ta yaya zai ce ya na son ta bayan ya san ya na auren yayar ta, ai ba hauka ake ba ko? Budar bakin Grema sai cewa ya yi, "

'Kar ki wani damu, irin soyayyar nan ai ba se ta sani ba, daga ni sai ke ba wanda zai ji,'

'Amma dai Yah Grema baka tsoron Allah, ka manta matsayi na ne a wajen sumayyah? Ni fa qanwar ta ce uwa d'aya uba d'aya , shekarun da ke tsakanin mu na da yawa fa, kai a ma bar batun shekaru ka dai san haramun ne ma ka furta irin wannan maganar a gare ni alhalin kana auren yaya ta ko? '

"Nan dai sukai ta fafata wa da Khadeejah, da ta kula ba zai fahimce ta ba, sha'awar da ke ran shi ta danne tsoron Allahn shi, sai ta kashe waya ta bar shi ta na ta mamakin shi, qarshe sai gani na yi ta dena zuwa gida na, duk abinda zai faru ba zata je ba, ko ni na je baya baya take da ni, Grema kuwa be dena mata naci ta waya ba, wata rana ta ce da shi, idan bai dena damun ta ba za ta fada min, hakuri ya dinga bata, ya na sanar da ita, in har na sani sai an yi bala'i da masifa, tunda ni dai yanzu na raina shi a cewar shi, alqawari ta masa akan ba zata fadan ba, in dai ya dena kula ta, in ko be dena ba, za ta sanar da ni, jin haka ne ya sa shi dan dakatawa na dan lokaci, ana haka sai na dan yi rashin lafiya ta kan zo ta kula da ni ta koma gida, bata kwana, har na ji sauqi, hakan sai ya qara tado wa Grema son kasancewa da Khadeejah, dan haka ya ci gaba da damun ta, ta same ni ina zaune, a tsakar gida ina shan iska, ta zayyana min komai da ke faruwa, ta nuna min irin messages din da yake tura mata, na gani, hankali na ya tashi, na yi kuka sosai, na gode Allah akan jarabawar da ya yi min ta auren miji kamar Grema, sannan muka hada baki da ita, na ce mata gobe ta ce masa zata zo zata bashi amsa ko tana son shi ko bata son shi, "

" Haka kuwa akai, ni kuma a daren na ce masa zani unguwa washe gari, nan da nan ya lalubi waya ya fada wa Khadeejah,tare da sanar da ita da na fita zai mata waya sai ta je, ita kuma ta tura min me ya ce mata, nai kamar ban san me ke faruwa ba, da safe kuwa haka akai, na gyara gida, nai girki na yi wanka na fita,na labe ita kuma a wannan lokacin ya sanar da ita na tafi ta hanzarta ta zo kafin na dawo,da yake gidan iyaye na da gidan Grema ba nisa sosai, dan haka da safen ta shirya ta tafi gida na, ta na shiga ta tadda Grema ya yi d'ai d'ai ya na jiran ta, kafin wani abu ya faru na afka gidan, nan muka hadu muka masa tofin Allah tsine, muka zage shi tatass muka kunyata shi, na ce masa"

'Ashe kai ina maka kallon jahili ashe ka ci uwar jahili, to daga yau aure ni da kai babu shi, tunda kai ka fi bunsuru iskanci, qanwata da muke ciki daya zaka nemi ka ciwa zarafi'

"ya tsugunna ya dinga bamu hakuri, tare da roqon mu rufa masa asiri kar wani ya ji maganar nan, ai kuwa muka ce sai mun sanar wa iyayen mu, ba bata lokaci muka tafi gida, muka sanar, mahaifan mu sun ji baqin ciki da takaicin faruwar hakan, da ace ita Khadeejah wata yar iska ce da ta biye masa an yi latata a gida na,da kyar iyayen shi suka bada hakuri na yarda na ci gaba da zama da shi, amma na raba shimfid'a da Grema kowa harkar gaban shi yake a gidan, dan kuwa duk yanda ya so na kula shi, duk nacin shi bana masa magana, da asuba in na masa sallama, kama baki na nake na tsuke kamar takashi,"

MAHWISHDove le storie prendono vita. Scoprilo ora