Kafin mu isa na dinga gwada layin wayar Grema ta na shiga amma ba a dauka ba, sai na hakura na ajiye, mun isa gidan Tukur da misalin shida da rabi na yamma, matar shi Aysha mai mutunci kafin mu isa ta min shimfid'a a tsakar gida, ta ajiye min abinci da ruwa mai sanyi, ta kai min ruwa bayi, ina shiga ko gaisawa ba mu tsaya yi ba Tukur ya fita ni kuma na shige bayi, sai da na sauke nauyin da ke ciki na na watsa ruwa, na yi alwala, na fita na yi sallar magariba da ake ta yi a masallatai, ina idar da sallah na ci gaba da kiran wayar Grema bai dauka ba, na masa message nan ma shiru, abinci na na ja na hau ci muna hira, har Tukur ya dawo daga masallaci muka hau hira gaba dayan mu, mu na tsaka da hira Grema ya kira ni, na dauka cikin fara'a, na hau gaishe shi dakatar da ni ya yi sannan ya ce,'Ina ki ka tafi?'
"Cikin mamakin yanda ya min magana na ce,"
'Baka san da wa ka ke magana ba ne? Me ya sa baka dauki kira na ba? Tundazu nake kira in sanar da kai ina gidan Tukur saboda gudawa ta kama ni, ga matan baban ka ga Maa a dakin kunya nake ji shine na kira Tukur yanzu haka ma gamu tare da matar shi da shi'
'Dalla malama dakata, waye kuma hakan? Ko dai kin tafi yawon ki ba,'
'Dakata Grema kar ma ka soma yi min magana a haka,in baka yarda ina gidan Tukur ba gashi ku gaisa har da matar shi, dakata wai kai gani ka ke abinda ku ke aikatawa a zuri'ar ku shi kowa ke yi? To ka tsaya ka ji ni ba kamar wadannan tsoffin guda uku bane, dan haka ka dena min magana irin haka'
"Cike da fushi na hau qoqarin kashe waya ta, can na ji ya na ce wa"
'Wanne tsoffin ki ke nufi?'
'Ka je gida ka tambayi tsohon ka zai baka labari'
"Kashe waya ta na yi cikin jin haushin abinda ya faru, ai kuwa Grema ya dinga kira na na qi daukar wayar shi nima, har ya gaji ya hakura, da safe kuwa sai ga kiran mahaifin shi, ina dauka muka gaisa sai ya ce,
'Haba Sumayyah, me ya sa zaki fadi maganar da ta jima da faruwa? Me ya sa xa ki haka?'
'Ah Ah fa Baa, na gaji da halin Grema na zargin tsiya, shi ya sa nake tuna masa ni ba mutuniyar banza bace, kuma kaf tarihin zuri'ar mu ba mutanen banza, na san kai ka san wane ne Tukur tunda aure ya hada ku da' yar uwar shi ba ku samu zuri'a tare ba ku ka rabu, to me zai sa ya dinga zargi na ni da d'an uwa na? '
' To ki yi hakuri, inshaa Allahu haka ba zai sake faruwa ba, sannan dan Allah ki dena tona abinda ya riga ya wuce'
(A shekaru masu yawa da suka wuce iyayen Grema maza suka hadu su uku suka wa wata yarinya fyade, ya zamana sun shahara wajen yi wa matan aure, 'yan mata, dattijai da qananan yara fyade, sai dai in mace bata biyo ta hanyar ba, amma sai sun bi sun fyade, al' adar su ce bin matan aure, duk wani kalar zinace zinace sun san ta kan shi, shi ya sa yake zargi na, yake zuwa da dare ya ga ko na kawo wani, yake bin diddigi na ko da unguwa za ni, ko bikin qanwa ta da akai da kyar ya bar ni na je, saboda a tunanin shi zan je na kwana da wasu ko wani, zargin Grema akai na ya samo asali ne daga Mummunar zinar da zuri'ar su ta dauka a matsayin ado, na tabbata qaddara ce ta sa ni auren Grema ba komai ba)
Da safiyar ranar na shirya ko gidan suna ban koma ba na yi garin mu, direct gida na na wuce, nan na tadda Grema ya na zaune shi kad'ai, cike da matsananciyar sha'awa a idanun shi, kamar ya san zan koma a ranar, ya na gani na ya ce,
'Ya ki ka dawo yanzu, sunan fa? Ko dake ba matsala zo nan, hawo ta nan,'
"Wani mugun kallo na bi shi da shi, sannan na warce hannu na daga nashi, na ce"
'Kar ka sake hannun ka ya sake taba jiki na Grema, Sunan qanwar uwa ta ake ko ta uba na? Ba zan tsaya ba, na fasa, nan nan akai bikin qanwa ta da kyar ka bar ni na kwana da kyar da sid'in goshi sai da ka ga zan maka ta mahaukaci sannan, shima kana nan manne kana biye da ni, dan haka ba zan zauna ba tunda ba sunan qanwar uwata ake ba,'
ŞİMDİ OKUDUĞUN
MAHWISH
RomantizmQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........